A kwanan baya ne Aminiya ta ruwaito cewa wata Bazamfariya ta yi tsintuwar dala dubu 80 a birnin Makkah yayin sauke farali a Aikin Hajjin bana.
Sunan Hajiya Aisha Muhammad Nahuche ya shahara bayan an samun rahoton cewa ta yi tsintuwar kusan Naira miliyan 60 a Saudiyya kuma ta nemi mamallakin kudin ta mayar yayin Aikin Hajjin bana.
Hajiya Aisha ta fito ne daga Unguwar Nahuche da ke Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara.
- Dan kwallon United ya bi sahun Ronaldo zuwa Al-Nassr
- Bazamfariya ta yi tsintuwar kusan Naira miliyan 60 a Saudiyya
Da take zantawa da Aminiya a wannan Lahadin bayan dawowar ta daga kasa mai tsarki, Hajiya Aisha ta bayyana dalilin mayar da kudin da ta tsinta.
Haka kuma, ’ya’yanta maza da suka dauki nauyin biya mata kudin zuwa Hajji domin sauke farali su ma sun bayyana yadda wannan abun yabon da ta yi ya janyo musu martaba.
‘Dalilin da muka dauki nauyin biya wa mahaifiyarmu kudin Aikin Hajji’
’Ya’yanta maza hudu wadanda sun ma fi ta farin ciki, sun ce abin da mahaifiyarsu ta yi ya janyo wa Najeriya martaba kuma ba sa da na sanin daukar nauyin biyan kudin Aikin Hajjin da ta yi.
Daya daga cikinsu, Bashir Muhammad, ya shaida wa Aminiya yadda ta labarta masa tsintuwar kudin da ta yi kuma ya bukaci ta nemi mahukunta mafi kusa ta danka kudin a hannunsu.
“Tun muna yara muke da burin watarana mu biya mata kudin Hajji.
“Ita ta zame mana uba da uwa tun bayan rasuwar mahaifinmu.
“Tun muna kanana mahaifinmu ya rasu, kuma ta ci gaba da dawainiya da mu da kulawa da tarbiyyarmu daidai gwargwado.
“Saboda haka muka yanke shawarar ba wanda zai je Aikin Hajji har sai ta sauke nata faralin.
“Muna yi wa Allah godiya da Ya ba mu ikon biya mata kudin.
“Mahaifiyarmu ta janyo wa danginmu martaba, garinmu da jiharmu da kuma kasa baki daya.
“Muna farin ciki da wannan lamari da zai zama abun koyi ga sauran al’umma.
A nata bangaren, Hajiya Aisha ta ce wannan shi ne Aikin Hajjinta na farko a rayuwa kuma ta tabbatar da cewa ’ya’yanta hudu ne suka biya mata kudin zuwa sauke faralin.
“’Ya’yana — Bashir, Nazir, Muhammad da Ahmad — ne suka biya min kudin zuwa Aikin Hajjin.
“Nauyin dawainiya da su ya rataya a wuya na tun bayan rasuwar mahaifinsu suna kanana.
“Duk cikinsu babu wanda ya taba zuwa Saudiyya domin Aikin Hajji, amma suka yanke shawarar biya min. Ina matukar godiya da wannan lamari.”
Yadda na tsinci kudi ina tsakar dawafi — Hajiya Aisha
Hajiya Aisha ta ce “ina cikin dawafi a Harami sai na yi tuntube da wata ’yar jaka.
“Na yi kokarin na durkusa na dauka sai kuma na ji tsoron kar a tattake ni cikin turmutsutsu saboda yawan jama’a.
“Sai na shuri jakar da kafa ta ta yi gaba kuma aka yi sa’a wani Balarabe ya lura kuma cikin gaggawa ya dauko ya miko min tsammaninsa tawa ce.
“Haka na rike jakar har na kammala dawafi. Bayan na bude sai na ga tsabar kudi a cikinta.
“Wata mata ita ma daga garin Gada ta bude jakar ta ga kudi a ciki.
“Bayan ta lissafa kudin sai ta ce lallai wannan kudi ne masu yawan gaske. Saboda haka sai na nemi daya daga cikin masu kula da Alhazai na Karamar Hukumar Bungudu.
“Sai kuwa wannan jami’i ya kai ni wurin Sheikh Umar Kanoma inda na mika masa kudin,” cewar Hajiya Aisha.
“Daga nan ne kuma aka sanar da mahukuntan Saudiyya kuma bayan wasu kwanaki aka mika musu kudin.
“Da farko bayan na tsinci kudin, sai na kira daya daga cikin ’ya’yan, Bashir na sanar da shi.
“Ai kuwa sai ya tunatar da ni cewa Aikin Hajji ne ya kai ni Saudiyya ba neman kudi ba.
“Shi ya karfafa min gwiwar yin cigiyar kudi, kuma na tabbatar masa da cewa hakan zan yi kar ya ji komai domin haka ya dace kasancewar kudin ba hakki na ba ne.”
Hajiya Aisha ta bayyana cewa ba ta fahimci muhimmancin abin da ta yi sai bayan dawowarta Najeriya.
“Duk wanda na hadu da shi sai ya min tambaya a kan lamarin. Don ba ni da masaniyar labarin tsintuwar kudin ya karade Najeriya sai bayan da na dawo gida.
“Na yi wa ’ya’ya na addu’a sosai da jiharmu da kuma kasa baki daya.
“Ina matukar alfahari da ’ya’yana kuma suna kula da ni yadda ya kamata.
“Suna kasuwancinsu da harkokin noma kuma ba ni da wata matsala da su,” in ji Hajiya Aisha.