Wata mata da ta yi wata bakwai a hannun mayakan Boko Haram ta bayyana wa Aminiya yadda rayuwarta ta kasance a tsawon lokacin.
Aminiya ta ziyarci garin Bama na Jihar Borno, inda ta zanta da Hajja Falmata (ba sunan asali ba) game da yadda ita da ’ya’yanta suka tsinci kansu a hannun Boko Haram.
Hajja Falmata ta ce ita da ’ya’yan nata suna cikin tafiya a hanyarsu ta zuwa garin Pulka ne suka ci karo da ’yan Boko Haram din.
Ta ce daga nan mayakan suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji inda suka shafe kusan wuni guda suna tafiya, kafin su tsinci kansu a cikin kasar Kamaru.
- Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram
- ‘Yan Boko Haram 36 sun mika wuya a Borno
- Boko Haram: Akwai ayar tambaya tsakanin gwamnati da sojoji – Dattawan Arewa
‘Rayuwa a hannun ‘yan Boko Haram’
Hajja Falmata ta ce, “Bayan an kai mu dajin a cikin kasar Kamaru mun ga mutane da yawa.
“A dajin akwai wani karamin kauye, sai dai dukkannin wadanda suke wajen ’yan Boko Haram ne, in ban da wadanda aka kamo.
“Wurin na da matukar ban tsoro musamman ganin yadda ake zartar da hukunci a kan duk wanda aka samu ya aikita laifi.
“Don haka kowa na taka-tsantsan domin kada ya saba wa Amir ko ya aikata laifin da shari’a ta haramta kamar sata ko zina da sauransu”, inji ta.
Ta ci gaba da cewa a kan idonta an kashe mata da maza da suka aikata laifuffuka daban-daban.
Aurena da dan Boko Haram
“Bayan mun shafe kusan wata hudu, sai aka tara dukkannin matan da ke wajen wadanda aka sato mu, aka ce a yau kowacce za ta yi aure.
“Na shiga halin damuwa, na yi ta kuka har wata mace ta rika ba ni hakuri, cewa babu yadda za mu yi, illa mu ci gaba da addu’ar Allah Ya kubutar da mu.
“Washegari aka daura min aure da Mataimakin Amir, na yi zaman kusan wata uku muna tare.
“Ganin na saki jiki da ‘mijin’ nawa, sai wata rana na tambaye shi, inda yarana biyu suke, don tun zuwanmu aka raba mu, kuma ban sake ganin su ba saboda ba a barin maza su shiga wajen mata.
“Allah cikin ikonSa sai ‘mijin’ nawa ya sanar da ni cewar zai bincika.
“A ranar da ya sanar da ni cewa ya gano yaran nawa, tun daga wannan lokaci na fara tunanin yadda za a yi in gan su.
‘Kubutar mu daga hannun Boko Haram’
“Kamar yadda na bayyana, ni da waccan mata mako daya tsakaninmu da zuwa, mun shaku sosai. Ta fada min ita ’yar garin Madagali ce.
“Akwai wata rana da maigidanmu ya ce za mu je duba ’yar uwarsa da ke zaune a cikin garin Gwoza, wadda ta haihu, kuma ba ta da lafiya.
“Da yake Allah Maji rokon bawa ne, shi da kansa ya sa aka dauke mu a kan babur har zuwa bakin iyaka ni da ita kawar tawa da yake ya ba ni dama in samu wacce za ta raka ni.
“Tafiyar da muka yi ne dalilin guduwarta daga wajen ’yan Boko Haram.
“Bayan mun shiga garin Gwoza, na je har gidan ’yan uwar tasa, har muka kwana.
“Daga nan fa, na yanke shawarar guduwa kuma a haka na samu na tsira na bar ’ya’yana biyu a can, ban san wane hali suke ciki ba”, inji ta.
‘Haka Allah Ya hukunta’
A zantawar Aminiya da mijin Hajja Falmata, ya bayyana cewa babu abin da zai ce sai godiya ga Allah, domin tun lokacin da aka dauke su, a sansanin ’yan gudun hijira yake zama.
Ya ce ya ci gaba da addu’ar Allah Ya dawo da su, “To amma ga yadda Allah Ya hukunta — ita ta dawo yaran na can, ko suna raye ko sun mutu”, inji shi.