✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda na tako daga Legas zuwa Abuja’

Sulaiman Hashim matashi mai shekara 33 da ya taso daga birnin Legas zuwa Abuja domin taya Janar Buhari murnar nasarar da ya samu a zaben…

Sulaiman Hashim matashi mai shekara 33 da ya taso daga birnin Legas zuwa Abuja domin taya Janar Buhari murnar nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar, ya yi wa Aminiya bayanin irin halin day a samu kansa a lokacin day a tako daga Legas har zuwa Abuja. Inda ya nuna cewa an karrama shi sosai a garurruwa da dama day a shige, kuma da ya isa Abuja ya samu kyakkwan tarbo, hasali ma dai a katafaren otel din nan na Transcorp ne aka ce ya samu masauki, kuma ganinsa sai ya zama da wahala saboda ana so a ba shi dama ya samu hutu sosai.  Ga dai yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ko za ka gabatar mana da kanka?

Sulaiman Hashim: Sunana Sulaiman Hashim, ni dan asalin garin Funtuwa ne da ke jihar Katsina, iyayena duka biyu a can aka haife su, sai dai mahaifiyata ta haife ni ne a jihar Osun kuma har yanzu tana can da zama, shi kuwa maihaifina yana gida Funtuwa. Na yi makarant na a tsakanin nan Arewa da kuma Kudu, Ina kuma aiki ne da wani kamfanin gine-ginen hanya a birnin Ibadan ta jihar Oyo.
Aminiya: Me ya ba ka kwarin gwiwar takowa daga Legas zuwa nan Abuja.
Sulaiman Hashim: Soyayya ce ga Janaral Muhammadu Buhari da Allah ya do ra mana a cikin zukatunmu ta ba ni kwarin gwiwar yin wannann tafiya. Na yi alkawari shekaru biyu da suka wuce cewa idan Janaral Muhammadu Buhari ya fito takara a shekarar 2015 sannan ya ci zabe, in dai ina da rai da lafiya zan yi tattaki da kafa daga duk inda nake zuwa Abuja domin taya shi murnar nasara, kuma in gane wa idanuna yadda za a rantsar da shi. Hakan kuma ya kasance da ikon Allah, ranar Laraba ina Ibadan sai ga sanarwar ya ci zabe. Nan na ce to tafiya ta kama ni tunda dai na sha alwashi kuma ina cikin halin koshin lafiya zan cika alkawarin da na yi.
Aminiya: Kana Ibadan aka sanar da zaben amma sai ka faro tafiyar daga Legas?
Sulaiman Hashim: Dalilin da ya sa na zabi faro tafiyar daga Legas shi ne kasancewar Legas ita ce birni mafi girma a kasar nan, kuma a Legas din ma sai na faro daga Bega Janshan, kasancewar shi ne mafi suna, na kuma faro wannan tafiya ne a ranar Alhamis 2 ga wannan wata ta Afirilu.
Aminiya: Kamar ta wadanne garuruwa ne ka bi ka kuma yada zango a yayin wannan tafiya taka?
Sulaiman Hashim: Duk da cewa ba lallai ne na Ambato su gaba daya ba, amma dai akwai garuruwa da kauyuka kamar Ogerece da ke bayan garin Lagos, daga nan sai Ibadan, sai garin Oyo, sai Odo-Baba, sai Ogbomosho, washe gari sai na wuce Ilorin, sai Oloru, sai Bode-Sa’adu, sai Mokwa, sai Kudu, sai Kutigi, sai Bidda, sai Lapai, sai Lambata, sai Suleja, sai kuma nan Abuja inda na faro da garin Zuba Sarki ya karbe ni kamar yadda wadansu takwarorinsa suka yi mini a baya.
Aminiya: Ya tafiyar taka ta kasance?
Sulaiman Hashim: na kan fara tafiyar ne da karfe 6 na safe sannan in dakata da karfe 6 na maraice, in banda wani gari bayan na wuce wani kauye mai suna Kudu inda na yi sallar Juma’a, na ci gaba da tafiya har karfe 9 na dare kasancewar hankalina bai kwanta da inda karfe 6 na maraice ya same ni ba. Haka dai na yi ta yin wannan tafiya har na kai ga wani gari na gaba na kwana.
Aminiya: Mutane na mamakin takowa da ka yi daga Legas har zuwa nan Abuja, mene ne sirrinka ne?
Sulaiman Hashim: Ba na kwallon kafa, sai dai abu guda da na doge da yinsa shi ne duk safiya ta Allah bayan na yi sallar asuba na kan yi gudu don daidaita jiki, kasancewar ni mutum ne mai saurin yin kiba, kuma na tabbata hakan ya taimaka mini wajen jure wannan tafiya da na yi.
Aminiya: A dan tafiya da na yi da kai daga wani kauye da ke wajen garin Suleja zuwa fadar Sarki ban da ruwan sha da kake sha a dan tsakani ban ga ka ci wani abu ba, ya batun cin abinci?
Sulaiman Hashim: Tun bayan tasowata yau kamar kwana 18 ke nan ban taba cin wani abinci ba kafin karfe biyar na maraice, in banda ruwa ko lemon Maltina da na ke sha a dan tsakani, kasancwar cin abinci zai janyo kasala ya kuma rage mini kuzari.
Aminiya: Ka hadu da mutane daban-daban a wannan tafiya taka, wane abu ne ya fi burge ka?
Sulaiman Hashim: Wadansu mutane ne da suka bullo a gabana a wani jeji bayan na baro garin Mokwa kafin isowata Bidda, mutanen wadanda sun manyanta, mazansu da matansu sun taho kaina a guje sanye da ganye a jikinsu suna waka cikin yarensu tare da ambato Buhari a ciki, har ma suna shafa zufar jikina, kamar kai da hannu suna kaiwa ga jikinsu, kamar dai masu daukar wani tubarraki.
Aminiya: Wace babbar nasara za ka ce ka samu a wannan tafiya?
Sulaiman Hashim: Babban nasarar da na samu ita ce irin karbuwar da na samu da kauna a wajen jama’a, a duk inda na je sai an karbe ni cikin murna da girmamawa, har ma da alheri wanda ba zan manta ba, inda mutane ke nuna farin cikinsu da kauna a gare ni, hakan ya kara karfafa mini gwiwa tare da yin alfahari da kaina da abin da na yi.
Aminiya: kalubale fa?
Sulaiman: Daga cikin kalubalen da na fuskanta shi ne, bayan na taso daga garin Ilorin ban kai ga Olorun ba sai gajiya ta kamani tare da jin rashin kuzarin ci gaba da tafiyar, haka nan dai na jure amma ba cikin jin dadi ba har na kai ga kauyen Olorun na zauna da hausawanmu na wajen, suka yi sauri suka kawo min abin sha da abinci na huta har zuwa washegari. Abu na biyu kuma shi ne, wadansu mutane haka kamar barayi da na hadu da su a hanya, mutanen wadanda bisa ga dukkan alamu fulani ne, sun nemi sanin ko ni wane ne, kafin ma in yi musu bayani sai daya daga cikinsu da ya ganni a gari na baya ya shaida ni, sai suka ba ni hakuri, har ma da yi mini kyautar Naira dubu biyu.
Aminiya: Yanzu da za ka hadu da Janaral Buhari mai za ka so ka sanar da shi?
Sulaiman Hashim: Da zan hadu da Buhari babbar damuwata da kuma shawarata a gare shi wanda ke damuna a zuciya ita ce irin yadda motocin tirela sama da dari biyu da na rika gani a yayin tafiyata suna dauke da matasa majiya karfi daga Arewa zuwa Kudu, wadanda idan sun je can ba su da wata sana’a ta kirki sai kananan sana’o’i da ’yan can ba za su iya ba, sai a ce a kira Malam. Wajen kwana sai ka ga mutane kusan goma a daki guda suna kwanciya a kan tabarma, idan ma sana’ar acabar suke yi ne kullum sai hadari. To kirana a gare shi shi ne, ya hanzarta kirkiro hanyoyin samar da sana’o’in da za su rika yi a yankunanmu cikin mutunci ba sai sun je can ana wulakanta su ba.
Aminiya: Ya batun alheri kuma, akwai rahotanni da ke cewa ka samu manyan kyaututtuka a yayin wannan tafiya, ko za ka ambato mana su?
Sulaiman Hashim: Babban dai abin da na samu shi ne wannan karbuwa da girmamawa da kauna da jama’a suka nuna mini a duk inda na je albarkacin janaral Buhari, wannan shi ya fi burge ni fiye da komai, kuma ba zan taba mantawa da shi ba.
Aminiya: Yau kwananka biyu ke nan da shigowarka Abuja, ya al’amura suka kasance?
Sulaiman Hashim: Bayan na taso daga Suleja a ranar Litinin da safe a daidai lokacin da na saba, a karshe na kammala tafiyata da misalin karfe 9 na dare, inda aka karbe ni a hedkwatar APC na kasa, kuma bayan jawabai an kawo ni masauki a wannan otel din inda ka same ni, yau kwanana biyu ke nan ina nan. A rananr da na shigo an sani a cikin motar asibiti (ambulance) an binciki lafiyata a lokacin da na ketara iyakar jihar Neja na shiga yankin Abuja a garin Zuba, kuma an duba tafukan kafafuna da suka dan yi kumburi tare da ba ni magani. Sannan a jiya Talata na ziyarci asibitin Turkiyya da ke nan Abuja inda aka ajiye gawar wani da ya rasa ransa a lokain shigowata nan Abuja, na kuma duba wadanda suka samu rauni wadanda yawancinsu ’yan achaba ne kamar yadda na samu labari a Asibitin, na kuma gode musu yadda suka dauki dawainiyar kulawa da su, ciki har da wadanda suka suma a yayin shigowata, inda suka rika sanya su a cikin motarsu ta asibiti har suka farfado.
Aminiya: Zuwa yanzu ko ka samu ganin shugaban kasa mai jiran gado Janar Buhari?
Sulaiman Hashim: Ban dai samu ganinsa ba tukuna, kodayake na kusa da shi ne suka karbe ni tare da yi mini kyakkyawar tarba, na san ayyuka ne suka yi masa yawa. Amma dai ina fata a karshe zan samu damar haduwa da shi saboda ina dauke da sakonni da dama da jama’a suka b ani zuwa gare shi a kan hanyata ta zuwa, kuma zan so in mika su gare shi a duk lokaccin da na hadu da shi.