✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na shekara 50 ina sana’ar dori- Malam Issau

Sana’ar dori tana da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya, kashi 99 cikin 100 na masu yinta ’yan gado ne. Wakilin Aminiya ya tattauna da Sarkin…

Sana’ar dori tana da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya, kashi 99 cikin 100 na masu yinta ’yan gado ne. Wakilin Aminiya ya tattauna da Sarkin dorin garin Jibiya da ke Jihar Katsina Malam Issau, inda ya yi bayani kan irin matsalolin da masu sana’ar dori ke fuskanta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Za mu fara da takaitaccen tarihi?  
Issau: Sunana Issau, an haife ni a garin dan-Indo da ke kudancin Faru a cikin karamar Hukumar Jibiya, Jihar Katsina. Ina da shekara kusa saba’in ko fiye.  
 Aminiya: Tun yaushe ka fara sana’ar dori?    
Issau: Na gaji sana’ar dori a wajen mahaifina, shi ma ya gada a wajen mahaifinsa. Akalla na kai shekara hamsin ina yin dori.   
 Aminiya: Maganar karatu fa?
Issau: Na yi karatun addini, amma ban yi na boko ba. Farkon rayuwa dai ka san akwai sha’anin yarinta. Da mahaifina ya ga dai shiriritata ta fara yin yawa, sai ya kira ni ya ce, in zo in koyi wannan sana’a ta gargajiya.  
Aminiya: Me ake nufi da dori?    
Issau: Abin da ake cewa dori shi ne, mutum ya karye a kashi a zo a hada shi a dasa, sannan a nemi mai duka ya kama.  
Aminiya: To yaya sana’ar take?    
Issau: Kamar yadda take a da, iyayenmu sun yi tane don taimako ba neman kudi ba kamar yadda ake yi a yanzu. Domin mun tashi mun ga sai dai a kawo musu ’yar tsaba ko ’yan kaji. To amma yanzu har ta kai fagen ba ma sai ka ce ga abin da za a ba ka ba, ba ma kamar in ka iya. Yanzu haka ba na rasa mutum 40 da suke kwance.  
Aminiya: Yaya ake yin dorin?  
Issau: Muna yin dori ne ta daidaita kashin da ya karye tare da sanya karare da maganin gargajiya da tsumma mu daure. Kuma duk madorin da ya yi kwana uku bai duba wanda ya dora ba, to ba madori ba ne.  
Aminiya: Ko kuna da doka?  
Issau: kwarai kuwa! Yo duk madorin da ya sake muka gano ba ya kula da wanda ya dora har kwana 3 sai mu sanya a kama shi, don ya nuna bai san abin da yake yi ba.
 Aminiya:   Ko kuna da dangantaka da likitoci?  
Issau: Sosai kuwa, domin sau da yawa idan an yi wani hadarin akan kira ni ko a kawo mani in yi dorin.  
Aminiya: Wace fa’ida ka samu a cikin wannan sana’ar?  
Issau: Alhamdulillahi, sanadiyyar wannan sana’ar a lokacin marigayi tsohon shugaban kasa Umaru ’Yar’aduwa an kai ni Minna a Jihar Neja wajen wani taro na al’adun gargajiya, a nan na nuna irin tamu baiwar, inda na dora wani nan take, na ce, ya tashi tsaye ba tare da ya rike sanda ba, ya mike, sannan ya taka.
Aminiya: Ko ka taba samun wata kyauta?
Issau: Na samu kyaututtuka, wannan sana’ar ta kai ni Bidda da Abuja da Kano da Kaduna da wasu wurare?
 Aminiya: Na ji ana kiran ka Sarkin dori, yaya aka yi ne?
 Issau: Sarkin Arewa Hakimin Jibiya mai ci yanzu Alhaji Rabi’u Rabi’u shi ne ya ce a wajensa babu wanda ya cancanci wannan sarauta sai ni, shi ne ya nada ni, bisa dalilinsa na cewa ba a taba samun wata matsala dangane da dori a wajena ba.    
Aminiya: Akwai matsaloli a cikin sana’ar?  
Issau: Sosai kuwa. Za ka dora mutum, sannan ka tsayar da tafiyar jininsa, idan ka yi kuskure ciwon daji (kansa) ya shiga, kuma ka san kansa ba ta da magani, ko kuma a daure, amma tsokar nama a birkice ko kuma jini na zuba. Duk wadannan matsaloli ne manya ga ita wannan sana’ar. Akwai kuma matsaloli daga wadanda aka yi wa dorin. Wani lokaci sukan ki bin umarnin da aka ba su a lokacin da aka yi musu aiki. Ka ce kada a motsa kafa ko hannun da aka yi wa aiki, amma sai su ki ji, sai in wani abu ya faru sai a ce laifin mai dori ne. Ko a bayar da maganin da za a yi amfani da shi tare da bayaninsa dalla-dalla, amma a  ajiye bayan kwana biyu a fara amfani da shi ko a canza daga yadda muka ce ko kuma a yi amfani da wani daban.    
Aminiya: To yanzu wane kira gare ka?
Issau: Ina kira ga masu wannan sana’a tamu a kiyaye yin mugun dauri, idan an kawo musu aikin da ba za su iyawa ba, to ba abin kunya ba ne su fada. Ina so gwamnati ta duba irin tasirin da sana’ar dori take da shi ta fuskar kiwon lafiya, amma tana daga cikin koma bayan sana’o’i a wurin gwamnati, don haka ta sanya mu a cikin sahun wadanda za ta rika taimakawa. Su kuma jama’a su rika sa ido a kan mu don taimaka mana wajen fitar da bata gari.