✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na samu sunan ‘karkuzu Na Bodara’- Audu Kano

Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da ‘karkuzu Na Bodara’, ya shafe shekara 33 a harkar wasan kwaikwayo da kuma fim. Ya yi bayanin yadda…

Audu Kano (Karkuzu) a lokacin da aka karrama shi yayin bikin karrama ‘yan fim a Kano makon jiyaAbdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da ‘karkuzu Na Bodara’, ya shafe shekara 33 a harkar wasan kwaikwayo da kuma fim. Ya yi bayanin yadda ya samu lakabin ‘karkuzu’ da kuma bambacin da ke tsakanin harkar a yanzu da kuma a da.
          Tarihinka a takaice
Sunana Abdullahi Shu’aibu. A halin da ake ciki duk garin da ka je nema na da wannan sunan ba za ka same ni ba, musamman a inda ni ke zaune a yanzu a Jos, amma kana cewa karkuzu, duk inda ka tsaya, Insha Allahu za a kawo ka har gidana. Sai dai ga yadda taken sunan yake: “karkuzu na Bodara ikon Allah na Bodara Malam.”
Kafin na shiga harkar fim a da ni dan tireda ne. Ina sayar da kwado da agogo da gilas da sauransu. Ina cikin haka sai muka hada wata kungiya muka fara wasan kwaikwayo. Ina tabbatar maka da cewar muna yi a fili a titi, har Allah Ya sa muka fara a gidan talabijin na NTA da ke Jos a wancan lokacin shekara hudu da bude shi.
Ka share kamar shekara nawa yanzu kana harkar wasan kwaikwayo da fim?
A takaice yanzu shekara ta 33 ina wannan aiki.
Kana iya tuna wasan da ya yi sanadiyyar shahararka a duniya?
Wannan wasa na karkuzu lokacin muna yi da garmaho, ina yin waini. Shi garmahon ba shi da batir ko soket a wannan lokacin. Wata irin hikima ce ta Bature. Wannan wainin shi ne batir da soket. Bayan na waina, sai in kawo kan garmahon in dora a rika waka a wannan lokacin. A wannan lokaci shi ne na shahara da shi a kan wasan karkuzun nan.
Akwai lokacin da ka tafi dogon hutu a harkar ko me ya jawo hakan?
Akwai dalilan da suka sanya hakan. Idan ba ka manta ba na gaya maka cewar shekara 4 da kafa NTA Jos muka yi ta gabatar da wasannin kwaikwayon karkuzu. A lokacin Marigayi Solomon Dushep Lar shi ne Gwamnan Jihar Filato. Marigayin ya ga cewar abubuwan da muke gabatarwa na matukar wayar da kan jama’a. A matsayinsa na gwamna sai ya ba mu mota a kungiyance. Da ya bayar da wannan motar shi ke nan sai bakin ciki ya tashi. Shugaban Gidan Talabijin din ya sa aka kira ni, bayan na je sai ya ce mini mun koma siyasa, saboda haka ko dai mu bi wanda ya ba mu wannan motar a rufe wannan fili namu a NTA, ko kuma mu koma NTA mu rabu da wanda ya ba mu wannan motar, a ba mu wannan fili. Ni a wannan zaman sai na ce wa shugaban gidan talabijin ba za mu iya rabuwa da wanda ya yi mana wannan alherin ba. Domin akwai Hadisin da ya ce, babu mai mayar da hannun alheri baya sai Shaidan.
To ni ba zan mayar ba. Wanda ya yi mana alherin nan ba siyasa ya ce mu zo mu yi ba. Mu kuma wayar wa mutane kai da muke yi aiki ne muke taya shi yi a jiharsa. Saboda haka, wanda ya ba mu wannan motar duk wurin da ya dauke kafa nan za mu ajiye tamu. Don haka wannan fili na NTA sai dai ku rufe. Fadin haka ke da wuya sai na fice daga zauren taron, nan da nan mutanena suka biyo ni. Ka ji dalilin ke nan. Muka zauna muka yi tunanin yadda za mu bullo wa lamarin cikin sabon salo, kawai sai muka fito a cikin fina-finai.
Ka share shekara 33 kana wannan harkar, wadanne ci gaba kake ganin an samu?
Na farko dai da can wasan kwaikwayo ake yi, yanzu kuma fina-finai ake yi, sannan a da samun ‘yan wasa ba karamin aiki ba ne, domin a lokacin ana yi mana kallon ‘yan iska. Duk da haka muka toshe kunnuwanmu, muka ci gaba. Idan kana yin mai kyau ka gani a akwatin talabijin, sai ka kara himma, in kuma marar kyau ne kake yi ka gani, sai ka daina. A da muna amfani na’urorin daukar wasanni irinsu BETAMAd da bHS, yanzu kuwa ka ga ana amfani da na’urorin nadewa a DbD. Sai dai wadancan na da sun fi karko. Dalili kuwa su wadannan kasa-kasan sai su dauki shekaru masu yawa ba su yi komai ba, amma ka ga na DbD da wuya su shekara ana amfani da su, za ka fara karo da matsala.
Mene ne in ka tuna a wannan harkar yake gamsar da kai?
Wallahi a da can din lokacin da muke wasannin kwaikwayo, idan mai kudi ya je ofishin gwamnati yana bukatar ya ga wani babban sakatare ko kuma wani kwamishina za a zazauna ana jira. A wannan lokaci babu yadda za a yi karkuzu ya zo ganinsa ka sha gabansa. Da zarar na mika katina, za ka ga wanda na zo gani ya ce in yi maza in shigo.Wannan ya yi mini amfani matuka.