✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda na kwato ’ya’yana daga masu garkuwa da mutane’

Me ya sanya ka tunkari maboyar masu garkuwa da mutane ta Laberiya da ke dajin Kudaru a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna? Babban…

Me ya sanya ka tunkari maboyar masu garkuwa da mutane ta Laberiya da ke dajin Kudaru a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna?

Babban abin da ya karfafa mini gwiwa kan wannan al’amari shi ne, a bara wadannan masu garkuwa da mutane da suke zaune a wannan waje na Laberiya, sun kama mini da, sai da na kai Naira miliyan daya, sannan suka sako shi.

Bayan haka a kwanakin baya da rana-tsaka, sai wadannan barayi suka zo suka dauki matan ’ya’yana guda biyu. A lokacin daya daga cikin ’ya’yan nawa da aka sace matarsa yana aikin dauko shinkafa a gona, yana dawowa sai ya ji labarin cewa an sace matarsa da ta kanensa, nan take ya nufi wajen, yana zuwa sai suka hada da shi suka rike su. 

Bayan haka a wannan rana, akwai wadansu mutanen garin Lahadin Maigamo da ke wannan yanki su uku da suka je aikin gyaran masara a kusa da wurin, sai suka hada da su.  

 Da na ji labarin wannan abu da barayin suka yi, sai na yi kundumbala na shiga daji na je wannan wuri mai suna Laberiya na samu barayin ni da wadansu yarana uku. 

Na shiga dutsen da suke ciki na fada cikinsu da suka gan ni sai suka bude mini wuta, ni ma na bude masu wuta. Yarana suna waje da suka ji karar harbe-harbe, sai suka shigo cikin dutsen, su ma suka bude wuta. Nan take barayin suka firgita suka fara gudu, na samu na karbo ’ya’yan nawa uku da mutum uku da suka je aikin masarar. 

Bayan tarwatsa masu garkuwa da mutanen mun samu kayayyakin da suka tara muka kone su duka, yanzu babu komai a wannan maboyar tasu ta Laberiya. Wannan maboyar barayi da masu garkuwa da mutane ta Laberiya, wuri ne da yake da manyan duwatsu a dajin Kudaru da ke nan karamar Hukumar Lere. A da barayin ba sa barin ko Fulani su shiga wurin don kiwo, kuma sun kori dukan mutanen da suke kusa da wurin.  

To an ce kun kafa kungiyar sa-kai ta yaki da barayi da masu garkuwa da mutane a wannan yanki, me ya karfafa muku gwiwar kafa kungiyar?

Mun kafa wannan kungiya ce sakamakon matsanancin halin da muka shiga a wannan yanki na garkuwa da mutane da fashi da makami da sace-sace. Da kuma yadda wadannan barayi masu garkuwa da mutane suka zo suka kwashe iyalina a ruga a garin Lahadin Maigamo kamar yadda na yi maka bayani. Wannan abu ne ya ba ni karfin gwiwar kiran jama’a kan mu zo mu hada kai mu kafa wannan kungiya, don ganin mu yaki wadannan barayi da suka addabe mu. Kuma kungiyar ta shafi kananan hukumomin Lere da Kauru da Kudan da ke Jihar Kaduna da kuma karamar Hukumar Doguwa da ke Jihar Kano.

Saboda barayi masu garkuwa da mutane suna haurowa daga Jihar Kano su zo su cutar da mutane a wannan yanki, don haka muka hada gwiwa da mutanen yankunan, domin ganin an durkusar da wadannan barayi. 

An ce kuna ta tubar da barayi, ta wace hanya kuke tubar da su kuma zuwa yanzu kun tubar da barayi nawa?

Muna tunanin duk abin da muke yi muna yi ne domin neman tsira a wajen Ubangiji. Don haka muka yi tunanin cewa yana da kyau ya zamo idan mutum ya zo ya same mu da kansa, don tuba yakan yi rantsuwa da Alkur’ani ya ce ya bar abin da yake yi, ba zai sake ba, shi ke nan. Za mu amince da rantsuwarsa, saboda mun yi imani da Alkur’ani Mai girma. Kuma za mu karbi makamansa idan yana da su. Shi kuma wanda ba ya da makami rantsuwa biyu zai yi, zai yi rantsuwa kan ya daina sata kuma zai yi rantsuwa A kan ba ya da makami. Kuma zuwa yanzu mun rantsar da barayi 1,300 a yankunan Lere da Kubau da Kauru da Doguwa. 

 Kuma muna ci gaba da farautar barayin da ba su zo sun tuba ba, a ’yan kwanakin nan ma muna nan muna ta artabu da masu garkuwa da mutane a dajin Falgore da ke karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano.

Wadansu suna ganin kamar kuna wuce gona-da-iri wajen gudanar da ayyukanku, me za ka ce kan masu irin wannan zargi?

 Bam a wuce gona-da-iri wajen gudanar da ayyukanmu, saboda babu wani mutum da muka taba aiwatar masa da wani abu da ba mu tabbatar da laifinsa ba. Kuma wadansu masu laifin ba sa ba mu hadin kai, don haka ake samun wadansu suna samun raunuka. A cikin wannan aiki da muke yi, zuwa yanzu mun rasa mutum 6 sanadiyar artabu da wadancan miyagun mutane. 

Mun samu labarin cewa kwanakin baya kun je kun yi zama da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, mene ne makasudin zaman da kuka yi da shi?

Babu shakka mun je mun yi zama da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna kuma mun samu kyakkyawar fahimta da shi, ya yi mana tambayoyi kan ayyukan wannan kungiya, kuma mun yi masa cikakken bayanai kan ayyukan kungiyar.

Daga lokacin da kuka fara gudanar da ayyukanku zuwa yanzu wadanne nasarori kuka samu wajen yaki da barayi a yankunan?

Babbar nasarar da muka samu ita ce a da kowa ya san irin yadda ’yan fashi da masu garkuwa da mutane suka addabi jama’a dare da rana a kan hanyar Kaduna zuwa Saminaka zuwa Jos, musamman a dajin Kudaru. Wadannan miyagun mutane sun kashe mutane da dama tare da garkuwa da mutane a wannan hanya. Amma yanzu komai dare za ka iya wucewa ta wannan hanya ba tare da wata fargaba ba. 

Yanzu masu garkuwa da mutane da kananan barayi kamar barayin babura da shanu da awaki da tumaki duk sun kaura daga wadannan yankuna ko sun tuba. 

A karshe wane kira kake da shi zuwa ga jama’a? 

To, kirana ga jama’ar wadannan yankuna da wannan kungiya ke gudanar da ayyukanta, shi ne su taimaka mana da addu’a domin cimma manufarmu ta magance miyagun mutane a wadannan yankuna.