✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na kubuta daga hannun Boko Haram – ’Yar shekara 13

Haka muka hakura suka tasa keyarmu har wani wuri wanda a da gari ne.

Wata budurwa ’yar shekara 13, Yakura Muhammad da a ranar Asabar da ta gabata ta kubuta daga hannun ’yan Boko Haram ta shaida wa Aminiya yadda ta kasance bayan shafe shekara daya cur a hannunsu.

Budurwar ta ce ’yan Boko Haram sun kamata ce a bayan garin Bama, bayan sun je gona, domin dibar abin miya, tun a lokaci tana da shekara 12.

Ta ce suna cikin gona da misalin karfe 10:00 na safe suna dibar yakuwa, sai wadansu matasa su biyar a kan kekuna, “Suka tambaye mu me muke a nan, nan daya daga cikinsu, ya tambaye mu a ina sojoji suke da zama a cikin garin Bama, muka ce musu ba mu sani ba.

“Sai babban cikinsu ya ce to yau za ku zama Musulmi, don za mu tafi da ku wajen yin aikin Allah.”

“Nan take na fara kuka haka sauran biyun, ashe daya daga cikinsu akwai bindiga tare da shi, ya ciro ta ya ce ko mu yi shiru, ko kuma ya kashe mu,” inji ta.

Ta kara da cewa “Haka muka hakura suka tasa keyarmu har wani wuri wanda a da gari ne, amma yanzu ya zama fayau, wanda nisansa daga cikin garin Bama ba zai wuce kilomita 2 ba.”

“A nan suka zaunar da mu, bayan wani lokaci da yake ni ce mafi kankanta a cikinmu, sai aka kai mu gaban Amir, shi ma ba babba ba ne sosai, amma duk fuskarsa ta cika da gashi.”

Yarinyar ta ce kwanansu bakwai a wurin “Sai aka daura min aure da daya daga cikin daliban Amir ina ’yar shekara 12.”

“An rika koya mana karatu, sauran yara maza kuma idan sun yi karatu da safe da yamma kuma ana koya musu harbin bindiga.”

“Na yi sa’a, don a kan idona aka kashe daya daga cikin ’yan uwana da aka taho da mu tare, bisa dalilin ta ki amincewa da mijinta,” inji ta.

Ta kara da cewa: “Gaskiya na sha wahala sosai kafin na saba da shi, amma Allah cikin ikonSa ban samu ciki ba.”

“Na yi kuka sosai, duk da cewa ba wannan ne karo na farko ba da na taba zama a hannun ’yan Boko Haram ba domin lokacin da suka kama garin Bama, mun zauna tare da su duk da dai a wancan lokaci ban wuce ’yar shekara tara ba.”

Yakura ta ce a kullum mazansu sukan fita, su ce za su je aikin Allah.

Ta shaida wa Aminiya cewa ba ta taba ganin Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ba, domin su suna cikin kauyukan Bama ne, amma maigidanta yana zuwa can inda manyansu suke.

Game da yadda ta samu kubuta

Yakura ta ce wata rana mijinta da sauran mazan kauyen sun tafi kai hari a garin Pulka, kwana biyu ba su dawo ba, sai ta fita tamkar mai zuwa debo ruwa, “Don mukan je rijiya dibar ruwa, to daga nan Allah Ya ba ni sa’a da wata babbar mace muka gudu, har muka iso wajen sojoji na shiga cikin garin Bama, inda a nan suka tare mu, suka ta yi mana bincike ko an turo mu ne dauke da bama-bamai.”

“Bayan sun kammala bincikarmu, sai aka tafi da mu gidan yari, aka tsare mu na kwana uku aka yi tayi mana bincike, daga bisani aka kawo mu nan sansanin da na fita daga cikin don zuwa dibar abin miya.

Ta ce ba ta fatar Allah Ya sake jarabtarta da sake fada wa hannun ’yan Boko Haram.