John Gebriel, jami’in sojan nan da ake zargi da kisan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami, ya amsa cewa tabbas shi ne ya kashe shi.
Yayin tattaunawarsa da manema labarai a hedkwatar ’Yan Sandan Farin Kaya da ke Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe, John ya ce tabbas shi ya kashe malamin addinin musuluncin.
- Karancin wutar lantarki ya jawo rage lokacin zuwa aiki da na makaranta a Bangladesh
- Farfesa Maqari ya yi wa ASUU tatas kan yajin aiki
Wanda ake zargin ya amince cewa Sheikh Goni ya taimaka ya dauko shi a motarsa daga garin Nguru, bayan da ya ga kamar ya gaza samun mota saboda dare ya yi a kan hanya ba tare da sanin yana da wani mugun nufi ba.
Daga nan sai ya ce a lokacin da suka je gab da garin Jaji-Maji, sai ya shaida wa malamin cewa akwai karar da ke fitowa daga motar, sai ya bukaci malamin da ya sauka don ya duba.
Malam bai yi gardama ba daga jin haka sai yarda ya tsaya don bincikawa, ashe sojan wata dabara ya yi wajen saukar da malamin daga motar.
Ya ce malamin ya duba, bai ga laifin motar ba sai dai a yayin da Sheikh Aisami ke ci gaba da duba ko akwai wata matsala a motar, tuni ya ciro bindigarsa kirar AK-47 ya nuna wa malamin ko zai tsorata ya gudu, amma bai yi ko gezau ba.
Ya kara da cewa, ya yi harbin gargadi, amma Sheikh Goni Aisami bai gudu ba.
Hakan ya sanya shi ya yi harbi kai tsaye kan malamin, inda ya fadi nan take kuma rai yayi halin sa, a cewar John.