Wani mai aikin hakar gwal a kamfanin wasu ’yan kasar China ya tsallake rijiya da baya a hannun masu garkuwa da mutane.
Mutumin da za mu kira Malam Aliyu, ya ce, shi da abokan aikinsa sun yi arba da ’yan bindigar ne wata rana da suka makara tashi a wajen aikin nasu tare da wata shugabarsu, wadda ita ma ’yar kasar China ce.
- ‘Yadda na dambace da dan bindiga muka tsira daga masu satar mutane’
- Tsarin Sallar Tarawih da Tahajjud a Masallacin Harami —Sudais
- Guguwa ce ta sa na ‘samu juna biyu’ —Mace
- An kubutar da mutum 5 daga masu garkuwa a Kaduna
A lokacin ne can sai ga wadansu mutane za su kai 12 rike da manyan bindigogi kirar AK47 da sauransu.
Mutanen sun umarce su da su kwanta, sannan ya sanya wani karamin karfe a cikin wandonsa.
Da aka ce musu su kwanta, sai ya binne makullin motarsa da katunan bankunansa.
Ya ce a wannan lokaci da ya kwanta sai yake ta addu’a Allah Ya sa barayi ne ba masu garkuwa ba. Can sai daya daga cikin mutanen ya ce da su “Mu masu garkuwa ne.”
Ya ce yana jin haka sai ya fara tunawa da matarsa wadda ta haihu ko ganin dan bai yi ba da sauran abubuwa.
Kasancewarsa mai karamin karfi sai yake tunanin a wannan lokaci zai yi wuya ya dawo da ransa tunda ba kudi ne da shi ba.
“Can aka sanya mana ankwa, sai muka shiga ratsa daji. A wannan lokaci da aka sanya mana ankwa a hannu sai na kokarta na saka hannuna a cikin aljihu na cire wannan karamin karfe da na boye, sai na shiga kokartawa ko zan nasarar cire ankwar hannuna. Haka dai na yi ta kokartawa na tsawon awa uku da muka yi muna ratsa cikin daji,” inji shi.
Ya ce da suka isa wani babban dutse sai masu garkuwar suka ce su huta a wajen, su kwana sai gobe su ci gaba da tafiya.
Masu garkuwar sun kwance hannayensu domin su sake daure kafafunsu kafin gari ya waye.
Koda da aka zo kan Malam Aliyu sai mabudin ya gagara bude ankwar saboda yadda ya dame ankwar da karfen hannunsa.
Masu garkuwar sai suka daure sauran a kafa shi kuma sai suka yi ta buga karfen da wata guduma wadda a cewarsa yana ganin kamar za a guntule masa hannun. Duk da haka ankwar ta ki buduwa.
Sai aka bar shi a haka ya kwanta. Ya ce bayan awa daya sai ya fara jin minsharin masu garkuwar amma su da aka kama babu alamar barci a tare da su. Nan ne ya ci gaba da gwada bude ankwar, har ta bude.
Sai ya fada wa abokin aikinsa a kusa da shi cewa shi fa ankwarsa ta bude, don haka guduwa zai yi.
Abokin aikinsa ya roke shi ya tsaya domin zai sanya rayuwarsa cikin hadari ne idan har ya gudu kuma mutanen nan suka kama shi.
Malam Aliyu ya ce tsohuwarsa da matarsa yake tunani, “wa zai biyan fansar?” Can da ya sake tabbatar da cewa masu garkuwar sun yi barcinsu sannan ya tashi tsaye ya rika tsallake su. Ya ce sai da ya yi tafiya ta akalla mita 100 sai ya ji daya daga cikinsu ya ce “Goddo!” Can kamar ya amsa shi ma ya ce ‘Goddo, sai ya yi shiru ya labe kada ya zama kila ba haka suke amsa gaisuwarsu ba.
Da ya ga mutumin ya koma barci, sai ya ci gaba da wurga kafafunsa har sai da tsakaninsu mita 200 sannan sai ya tsinke da gudu.
Ya hadu da wata dabba
Ya ce maimakon ya yi baya, ta inda aka kawo su, sai ya yi gaba tare da barin masu garkuwar a bayansa.
Bai tsaya ba har sai da ya yi gudu fiye da awa daya. Can sai ya fara jin maganganu daga nesa kuma hanya ta kare masa.
Daga shi sai wani babban dutse. Sai ya shiga hawa dutsen can sai ya gagara, sai ya ga wani kogo kawai ya shige ciki.
Sai ga wani abu kamar gwaggon biri amma inuwarsa yake gani kawai kuma bai tabbatar da halittarsa ba a cikin duhu.
A wannan lokaci su kuma masu garkuwan sun biyo shi, har sun iso inda yake. Suka yi ta haska wajen da fitila.
“A wannan lokaci in ban da addu’a babu abin da nake yi har wannan halitta ta bar inda nake,” inji shi.
Ya ce sai da ya tsaya cikin kogon na tsawon awa uku sannan ya fito. A lokacin alfijir ya fara fitowa. Sai ya yi maza ya bi ta inda wannan halitta ta wuce ya sauka ya yi ta zagaya dutsen har sai da ya iso ta inda aka dauko su.
Ya ce nan take ya ciro makullin motarsa da katin, a inda ya binne su ya yi maza ya shiga cikin motar ya tafi.
Garkuwar ta yi sanadin durkushewar kamfanin
Malam Aliyu ya ce ya tafi kamfaninsu, inda ya tarar da hankalin jama’a a tashe kuma shugabansu na waya da mahaifiyarsa.
Sai ya amshi wayar suka yi magana ya sanar da shugabansu cewa garkuwa aka yi da su. Da kyar aka kwato sauran.
Ya ce yadda aka yi kamfanin ya durkushe ke nan, wanda har yau bai farfado ba.