Wata mata da ta haihu a cikin jirgin sama ta ce ba ta taba zaton nakuda ce ta zo mata ba har sai da ta ga ta haihu.
Jirgi na cikin tafiya a sararin samaniya ne aka ga matar mai suna Lavinia “Lavi” Mounga, ta fara kurmusun ciwon ciki.
- Kwastam sun kashe mutum 5 a garin kama shinkafa
- ’Yan sanda sun ceto yarinyar da aka kulle a keji wata 8
- ’Yan bindiga sun yi wa matar aure fyaden gandu
- Yadda fasto ‘ya babbake’ miloniya yayin yi masa addu’a
Lavi wadda ke hanyarta ta zuwa hutu daga Utah zuwa Honolulu a Hawaii na kasar Amurka tare da iyalanta ta ce ko a lokacin da cikinta ya fara ciwo, ba ta san tana dauke da juna biyu ba.
“Ban san ina dauke da juna biyu ba, kawai sai ga shi na haihuwa,” inji ta, a bidiyon hirar da kafar Hawaii Pacific Health ta yi da ita.
Bayan Lavi ta fara nakuda a cikin jirgi, an yi sa’a a cikin fasinjojin akwai wani likita, Dokta Dale Glenn da abokan aikinsa, wadanda suka karbi haihuwar cikin mai sati 29.
Ta bayyana cewa Dokta Glenn tare da Lani Bamfield, Amanda Beeding da Mimi Ho – wadanda su kuma malaman jinya ne – duk daga asibitin iyali North Kansas City, fasinjoji ne a jirgin, kuma su ne suka yi duk abin da ya kamata na ganin jaririn bai samu lahani ba.
“Abin ya zo da sauki saboda akwai malaman jinya uku da wani likita a cikin fasinjojin da ke cikin jirgin,” inji ta.
Mahaifin Lavi ya nemi a sa wa jaririn suna Glenn domin karrama likitan da ya karbi haihuwar, amma mai jegon ta ki amincewa.
Maimakon haka, ta nemi Dokta Glenn shawarar wani sunan da za a rada, shi kuma ya ba da, “Kaimana,” wanda sunan dan rikonsa ne.
Yanzu “Kaimana,” nada daga cikin sunayen jaririn wanda za a ajiye shi a kwalba na karin mako 10 ko fiye, kafin a sallame shi.