Mahukunta a jihar Jigawa sun ce mutum 50 ne suka mutu a karamar hukumar Hadejia, sabanin mutum 100 da wasu kafofin yada labarai da na sada zumunta ke ta zuzutawa.
Da yake bayyana hakan ga wakilin Aminiya, shugaban karamar hukumar ta Hadejia, Malam Abdullahi Maikanti Hadejia, ya ce yawan mace-macen bai kai yadda ake ta yadawa ba.
“Wancan labari da ake yayatawa karya ce tsagwaronta; an yi ne kawai don a bata wa gwamnati, domin duk wadanda suka buga labarin babu wanda ya zo Hadejia ya gani…”
Wasu kafofin yada labarai a Najeriya dai sun ba da rahoton cewa an samu mace-mace har 100 a karamar hukumar ta Hadejia a kwana 10.
Alkaluman karamar hukuma
Shugaban karamar hukumar dai ya ce su suna da alkaluman mutanen da suka mutu a daukacin mazabu 11 da ke kwaryar Hadejia.
A cewarsa, a mazabar Rumfa mutane hudu ne suka mutu daga ranar Lahadi zuwa Talata, Atafi mutum biyu biyu, Sabon Garu mutum uku, Matsaro mutum takwas, Gagulmari mutum uku, Kofar Kudu mutum biyar.
Ya ci gaba da cewa a unguwar Kasuwar Kofa kuwa mutane uku ne suka mutu, sai ’Yankoli mutum biyar, sai Yayari mutum uku, Dubantu mutam shida.
Amma inda lamarin ya fi yawa, inji Malam Maikanti, shi ne unguwar Manema, inda aka ce mutane 15 sun mutu.
Wadanda suka mutu a asibiti
Sai dai kuma shugaban Babban Asibitin Hadejia, Dokta Abdullahi Namadi, ya ce su a nasu bayanan, mutane 13 ne suka mutu daga ranar 1 ga zuwa 5 ga watan Mayu, kuma dukkansu babu wanda cutar coronavirus ta kashe.
Ya kara da cewa wasu daga cikin mutanen 13 sun mutu ne sanadiyyar gyambon ciki, wasu ciwon zuciya, wasu hawan jinni, wasu kuma ciwon suga.
Daga cikinsu kuma, inji shi, mutum biyar ba ’yan asalin Hadejia ba ne, jinya ce ta kawo su.
Tuni dai gwamnatin jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti don ya binciki musabbabin mace-macen.
An fara bincike
Shugaban kwamitin, Dokta Muhammad Abdulwahab, wanda darakta ne a ma’aikatar lafiya ta jihar, ya ce za su yi aiki har sai sun gano dalilin mace-macen.
Ya kara da cewa da zarar kwamitin ya kammala bincikensa, wanda yake fatan gudanarwa a kwana uku, zai sanar da gwamnatin jihar dalilan mace-macen domin ta dauki matakin da ya dace.
Wakilin Aminiya wanda ya samu zuwa Hadejia, ya ziyarci babbar makabartar garin, inda ya ga sabbin kaburbura kusan 100.
Ya kuma tattauna da wasu wadanda suka rasa danginsu.
Wadanda suka yi rashi
Daya daga cikin mutanen da suka yi rashi, Malam Adamu Danwawu ya ce dan uwan mahaifinsa ne ya rasu a unguwar Gagulmari.
A cewarsa, ganin idonsa a unguwar mutane hudu ne suka mutu, kuma a kusa da Kofar Fada an yi jana’izar mutum uku.
“Daga unguwar Matsaro zuwa Kasuwar Kofa zuwa Gagulmari na halarci jana’izar mutum 10; a takaice na ga rasuwa ta mutane daban-daban ta kai 15 daga Lahadi zuwa Talata”, inji shi.
Ya kuma ce wasu daga cikin wadanda suka rasun da ma sun jima suna jinya, wasu kuma suna da shekaru, lokacin mutuwarsu ne ya yi.
Shi ma Sabo Sani, mazaunin Sabon Garu, cewa ya yi an zuba sosai a Hadejia, amma galibin wadanda suka rasu manyan mutane ne dattawa da mata tsofaffi.
Ya ce daga Lahadi zuwa Talata gawar mutum 15 ya gani kuma ya halarci jana’izar mutum 10 daga ciki.
Ya ce ya yi amanna mace-macen ba su da nasaba da cutar coronavirus da ake cewa wai ita ce take kashe mutane a garin na Hadejia.
“Wannan wani iftila’i ne na wata annobar ya sauka ake mutuwar duk da cewar ana mutuwar a irin wannan yanayi. Amma magana ta gaskiya na jima ban ga yadda ake binne mutane ba kamar ana shuka Togo a Hadejia kamar wannan lokaci”.
Ya kuma ce da kansa ya ziyarci babbar makabartar Hadejia ya ga sabbin kaburbura da aka binne mutane manya da kananan yara sun fi 50.
Dukkan mutanen da Aminiya ta tattauna da su dai, kama daga shugaban karamar hukumar zuwa ga shugaban Babban Asibitin Hadejia, sun ce babu wata alaka tsakanin mace-macen da cutar coronavirus.
Sai dai wasu masana sun yi kira da a yi bicike kafin a yanke hukunci.