Binciken Aminiya a Jihar Kano ya gano cewa zawara musamman wadanda iyayensu ba su da karfi suna shiga wani hali na kaka-ni-ka-yi sakamakon canjin rayuwa da sukan samu lokacin da suka dawo gidan iyayensu.
Wannan ya hada da rashin samun isasshen abinci da wurin kwana da sauran abubuwan rayuwa, musamman idan aka rasu aka bar su da yara marayu.
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
- An cafke jami’in tsaron ABU da ke hada baki ana garkuwa da mutane
- Abubuwan da ke raba tsakanin masoya
‘Ko wacce muke gaba ba na mata fatan zawarci’
Malama Halima Muhammad, daya ce daga cikin irin wadannan zawarawa wadda ta ce ta kai shekara biyar tana zawarci.
Ta bayyana wa Aminiya cewa a yanzu haka sakamakon halin da ta tsinci kanta a ciki bayan dawowarta gaban iyayenta ta shiga da-nasanin mutuwar aurenta.
“A kullumu ina da-na-sanin mutuwar aurena musamman idan na tuna yadda maigidana yake hidima da ni da ’ya’yana.
“Amma kaddarar mutuwar aure ta shiga tsakaninmu. A yanzu ga shi a gidanmu, ni nake fafutikar abin da zan ci ni da ’ya’yana, domin dan abin da baban yaran ke bayarwa a wata ba isar mu yake ba.
“Babu wanda yake taimaka min, a gidanmu in takaice miki labari daga wanda ake kawo min albarkacin ’ya’yana kannena suke dan samu.
“Abin ba dadi ko kadan, ko wacce muke gaba da ita ba na yi mata fatar zawarci,” inji ta.
‘’Yan uwana sun juya min baya’
Wata bazawara mai suna A’isha Mansur ta ce ta tsinci kanta a halin ni-’ya-su sakamakon juya mata baya da ’yan uwanta suka yi bayan da aurenta ya mutu ta dawo gida.
“Lokacin da na dawo gida ’yan uwana da iyayena ba su goyi bayana ba a kan rigimar da ta shiga tsakanina da mijina har ta kai ga rabuwar aurenmu.
“Saboda haka aka bar ni na zauna a gidan amma ni nake yi wa kaina komai na rayuwa.
“Gaskiya ba zan ce iyayena talakawa ba ne sosai, suna da dan rufin asirinsu amma haka mahaifina ya ki yarda ya dauki nauyina.
“A yanzu haka rayuwata kacokan ta dogara a kan ’yar sana’ar da nake gudanarwa ta awara, a ciki nake yin komai na rayuwata,” inji ta.
Zawarci akwai kawo kaskanci
A cewarta halin zawarcin da ta samu kanta ya janyo mata kaskantar da kanta a wurin maza.
“Kin san kasancewar ina cikin wannan hali sai nake tunanin mafita ita ce in samu in yi aure.
“Da farko-farkon dawowata gida da zarar na samu bazawari ni da kaina nake neman mutum ya turo iyayensa a yi maganar aure, wanda kuma hakan ba abu ne mai sauki a wajen mace Bahaushiya ba, domin a gaskiya hakan wulakantar da kai ne.
“Amma sai ki ga maganar ta shiririce. Daga baya da na sake samun wani ya nuna ra’ayinsa a kaina to haka fa sai na gane mazan ma da ke zuwa ba kowane ne ke zuwa da niyyar aure ba, sun fi zuwa neman mace don su yi shashanci da ita,” inji ta.
Sabuwar makaranta
Wata bazawara da ta shafe tsawon shekara uku tana zawarci mai suna Murja Saleh da ke Unguwar Gwammaja ta bayyana zawarci a matsayin wata makaranta ta daban, idan ta dubi halin da ta tsinci kanta a ciki wanda a cewarta ya sanya take yi wa mata gargadi su rike aurensu komai rashin dadinsa.
“Wallahi sai da aurena ya mutu na dawo gida lokacin na san rayuwa.
“Domin ta kai a yanzu ina dora tukunyata daban da ta iyayena saboda abin da ake ba ni a gidan ba ya isa ta.
“Ga shi dai mahaifiyata ce a gidan amma ni sai nake ganin kamar ta tsani ’ya’yana domin da zarar rashin jituwa ta shiga tsakanin nawa ’ya’yan da kannena sai ta dora wa ’ya’yana laifi koda kuwa a zahiri suke da gaskiya.
“Baya ga wannan dan dakin da ke tsakar gidanmu shi nake amfani da shi a matsayin wurin kwananmu wanda a matse muke,” inji ta.
Sai kin koma gidanuku za ki gane kurenki
Malama Murja ta yi kira ga matan aure su ci gaba da hakuri a gidajen aurensu domin, gudun gara matan ke yi a karshe su kare da zago.
“Kullum ina fadin cewa mata su kara juriya a gidajen aurensu duk wata matsala mai shigewa ce idan aka yi hakuri.
“Idan mace tana ganin tana da gidan uba, to wallahi sai ta zo ta zauna za ta gane cewa ta yi kuskure.
“Domin sai ta gwammace ta zauna a dakinta komai wahalar da take ciki a kan ta dawo gidansu.
“Domin tana dawowa gidan to fa za ta fara samun matsala da iyayenta da ’yan uwanta wanda sai ta yi hakuri.
“To kin ga kuwa in har haka ne, gara mace ta yi hakuri a gidan mijinta shi ya fi alheri,” inji ta.
Bincike kafin aure
Haka a Jihar Adamawa zawarawa na kokawa kan irin mawuyacin halin da suke shiga da zarar aurensu ya mutu.
A’isha Garba, wadda ta rabu da mijinta tsawon shekara 10, ta ce yana da kyau iyaye su yi taka-tsantsan da tsananta bincike wajen aurar da ’ya’yansu mata.
Domin wadansu mazan suna yin saki ne a kan abu kalilan wanda bai taka kara ya karya ba.
Ta ce: “Na bar gidan tsohon mijina ne saboda kuruciyar sabon aure wanda namiji yakan yi a sabon aure na nuna isa.
“An yi min rasuwa sai na nemi izininsa a kan zan je gida domin rasuwar.
“Budar bakinsa wai idan na wuce kofar gidan a bakin aurena, ni ko na wuce a hakan dai aka rabu duk da daga baya ya yi biko amma na ki,” inji ta.
Zawarawa abin tausayi ne
A’isha ta ce a layin da take ta san zawarawa mata 30 ba a maganar ’yan bayan layinsu.
“Za ki gan su abin tausayi kowa yana neman na kansa wadansu na shiga sana’ar kosai da sauransu, ba don komai sai don dogoro da kai,” inji ta.
Ita ko Bilkisu Baffa, wadda shekararta uku da fitowa daga gidan miji da ’ya’ya biyar, ta ce abin babu dadi sosai musamman idan ka fito daga karamin gida.
“Iyayenka na murna sun rabu da kai nauyi ya ragu sai a koro ka da yara wanda iyayenka dole su dauki nauyinka da na yaran,” inji ta.
Ba ta taki miji yake ba
Koda Aminiya ta tambaye ta game da barin yaran wajen iyayensu maza, sai ta ce “Yaushe mijin ya kula ka balle yara biyar alhali shi ma fama yake yi?”
Bilkisu ta kara da cewa idan ka dawo gida zamanka zai zama ba kamar na da ba, domin za ka yi fada da kowa.
“Sai ka yi fada da kowa hatta mahaifiyarka a kan ’ya’yanka domin ba ka jin dadin yadda ake yi, a haka kuma wani lokacin za ka hadiye,” inji ta.
Ta ce sai bayan mace ta gama wahalar rainon ’ya’ya sai kawai mijin ya ce wai a ba shi ’ya’yansa wadanda da bai san wahalarsu ba.
Akwai zalunci a ciki
Hafsat Bello ta ce yana da kyau malaman addini su karfafa yin wa’azi ga maza musamman a kan hakkin ’ya’yansu da suka rabu da iyayensu domin abin akwai zalunci a ciki.
Ita kuwa Binta Bashir cewa ta yi tsabagen wahalar rayuwa da ta tsinci kanta da ’ya’yanta shida, ya sa ta fara sayar da abinci a kan hanya.
“Gara in dage domin kula da yarana domin idan na samu biyar zan ajiye in tara kudin Islamiyyarsu.
“Idan na sake samun wata biyar din sai in ajiye domin sayen kayan karyawa na safe,” inji ta.
Ta ce shi ya sa sai a ga wadansu zawarawan sun lalace har sun fita kamaninsu domin irin wadannan kalubalen da suke samun kansu a ciki.
“Babu macen da za ta baro gidan mijinta sannan ta ji dadi.
“Ya kamata maza su rika tsoron Allah, su rika cewa je ki gidanku a kan abu kalilan sannan ya hado ka da yara.
“Yaran nan kuma za su hada ka fada da mutanen gidanku har idan ka yi wa naka ’ya’yan wani abu sai iyayenka su yi fushi su ce ka fifita naka a kansu.
“Kin ga idan so samu ne ai ba za ka so hakan ba,” inji ta.
Ta ce “Ina kira ga gwamnatoci su yi dokoki a kan mazan da suke kin daukar nauyin ’ya’yansu idan suka rabu da iyayensu mata, domin tilasta musu daukar nauyin da ya rataya a wuyansu.