Wani lebura mai suna Abubakar Sani da ke aikin dakon siminti a Unguwar Jabi Masallaci a Abuja, ya ce, ya na son barin sana’ar dakon siminti idan ya samu jari, kafin karfinsa ya kare. Ga yadda hirrar ta kasance:Wani lebura mai suna Abubakar Sani da ke aikin dakon siminti a Unguwar Jabi Masallaci a Abuja, ya ce, ya na son barin sana’ar dakon siminti idan ya samu jari, kafin karfinsa ya kare. Ga yadda hirrar ta kasance:
Aminiya: Za mu so mu ji tahirinka?
Sunana Abubakar Sani, ni ina aikin leburanci ne wato aikin dakon siminti a Unguwar Jabi Masallaci da ke Abuja. Idan an kawo tirela mai daukan tan 30, ko kuma buhu 600, mu hudu za su mu iya sauke wa a minti 30 zuwa sa’a guda. Amma idan mu shida ne za mu iya saukewa a cikin minti 20 zuwa 25.
Aminiya: Nawa ku ke karba idan kun sauke tirelan simintin?
A nan kasuwan simintin ta Jabi muna sauke tirela a kan naira dubu shida wato Naira 10 a kan ko wane buhu ke nan. Amma idan za a je wani wuri ne, inda ake gini ko wani aiki, ko wani shagon siminti, muna karbar Naira dubu 10 ko 20 har ma 30 idan wurin da nisa, wani yana kai mu ya dawo da mu, wani kuwa idan ya kai mu muka sauke to ba ruwan shi da mu, ya danganci mutuncin mai aikin. Ko a fadar shugaban kasa idan an neme mu, muna aiki.
Aminiya: Bayan ka ki wannan aikin, idan gari ya waye, yaya kake jin jikinka?
Sumul kalau, ba matsala ko kadan.
Aminiya: Ba ka jin kasala ko dan alaman zazzabi?
Wannan kuma daga Allah ne, domin mai aikin leburanci na motsa jiki, da noma, da sauran aikin karfi ai bai cika ciwo ba, domin yana motsa jiki ne sosai ba mai cin dadi yana kwance ofis ko motar alfarma ana jansa ba, ga kuma fama da shan ruwan sanyi.
Aminiya: Idan kuna aiki sai ruwan sama ya barke, ya kuke yi?
Ai shi siminta dan gata ne, kuma kamar akuya yake, da ta ga ruwa sai ta fake, to shi ma idan ruwa ya sauko, sai a tsayar da aiki a rufe shi ruf don kar ruwa ya taba shi, don idan ruwa ya taba shi zai daskare ya lalace ke nan. Mu kuma sai mu fake har sai ruwa ya dauke sannan mu ci gaba da aiki.
Aminiya: Idan kuna aiki wani ya ji ciwo ko wani dalili, ya za a yi gun raba kudi?
Zai shaida wa abokan aikinsa, sai ya koma gefe ya zauna, idan an gama aikin, sai a raba kudi daidai wa daidada da shi.
Aminiya: Ya kake ji in ka bar Abuja, ka tafi ganin gida a garinku, har na tsawon wata gudu ba ka yi dakon siminta bo ko wani aikin karfi ba?
A gaskiya bana jin dadin jikina, domin zan ji duk gabobi na na min ciwo.
Aminiya: Wane irin abinci kuke ci?
Ina shan shayi da kwai da safe. San nan in ci shinkafa da wake, da yamma kuma in ci taliyar Indomie da kwai. Sannan ina hadawa da gwanda, kabeji, Apple da kayan lambu.
Aminiya: Ko kana da shirin barin wannan aiki don sauya sana’a?
Idan na kai shekara 30 zan bar aikin. Idan na samu kudi zan bar wannan aiki. Don na shekara kusan shida ina wannan aikin. Sannan in matashi bai kai shekaru 17 ba, ba mu barin ya shiga wannan aikin sai da wanda ya horu a kyauye ko da dan shekara 15 ne.
Aminiya: Ya kuke kuna shirya siminti?
Gwani ko kuma masta, shi yake shirya shi ka ga ya miki tsaye cir, su kuma masu karfi suna daukowa, sannan sai dan bana bakwai wato sabon shiga shi kuma ya shiga cikin mota yana mikowa. Sabo yana dauko wa daga mota. Idan buhu ya fashe, wani yana cewa a biya shi, wani kuma kau da kai kawai yake, ya ce shi ke nan.
Aminiya: Wannan aiki yana da hadari don garin siminita da ake shaka, mene ne rigakafi?
Lallai wannan aiki yana haddasa tari, kuma, shi ya sa wasu ke daure hanci.