’Yan kasuwar da suke gudanar da harkokin kasuwanci a shagunan da suke filin Idi na Kano suna ci gaba da bayyana irin asarar da suka yi a daidai lokacin da masu kwasar ‘ganima’ suke ci gaba da mamaye gine-ginen da aka rushe da sauran gine-gine a babban birnin jihar.
Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta shiga wuni na uku na rushe gine-ginen da ta bayyana cewa an gina su ne a filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba.
A jijjifin ranar Litinin motar buldoza ta rusa wani rukunin shaguna a kusa da filin Idi, a ci gaba da rusau din da ta faro a ranar Asabar, kuma ta rusa wasu gine-gine na biliyoyin Naira a filin sukuwa da tsohon otel din Daula da kuma Sansanin Alhazai.
Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, wanda ya bayyana rushe-rushen da wani bangare na cika alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zabe na “dawo” da tsarin babban birnin jihar, inda ya ce rusau din ba daukar fansa ba ce a kan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje kuma za a ci gaba da yin rusau din.
Na yi abin da ya dace kan cire tallafin man fetur — Tinubu
Aminiya ta ziyarci filin Idi a ranar Litinin da ta gabata, inda ta iske ’yan kasuwa suna kukan yadda rusau din ya jawo musu mummunar asara.
Yayin da rusau din ya gudana a jijjifin ranar Litinin, an ga daruruwan matasa da wasu da suka manyanta wajen karfe 3:00 na dare suna kwashe kayayyakin da za su iya daga gine-ginen.
Sun rika cire karafuna da kofofi da tagogi da kayayyaki masu daraja daga gine-ginen.
’Yan kasuwa da mamallaka shaguna da dama da suka yi magana da Aminiya sun ce, abu ne mai bakanta rai yadda suna ji suna gani masu wawaso suna kwashe kayayyakinsu da sauran dukiyarsu daga shagunan.
Sun ce, shagunan da aka rushe sun haura 200 makare da dukiya ta miliyoyin Naira da suka yi asarar su.
’Yan kasuwar sun ce, sun fito da tsakiyar dare don su kare shagunansu su kwashe kayayyakinsu, amma barayin suka hana su yin haka.
Aminu Usman Gama, wanda yake sayar da robobi a kasuwar ya ce, ya rasa daukacin jarinsa da ya haura Naira miliyan bakwai da ya yi shekaru yana nema.
“An gaya min ’yan daba sun isa kasuwarmu da misalin karfe 2:00 na dare.
“Lokacin da na isa na iske sun balle kofar shagona sun sace duk kayan da ke ciki.
“Wannan ya hada da kudin da ban ma kirga su ba.
“Ina da sito a saman shagona, shi ma sun sace komai. Sun talauta mu, mun rasa komai. Daruruwan mutane abin ya shafa,” in ji shi.
Wani dan kasuwa, Shamsu Abdussalam, ya ce, rusau din ya jawo masa asarar sama da Naira miliyan 10 kuma ya kawo kayan sama da Naira miliyan biyar a shagon da sitonsa da ke sama ke nan aka zo rusau din.
“Ina da shaguna biyu da wani sito a sama, amma an sace komai a tsakiyar dare.
“Ina da kayan sama da Naira miliyan 10 a ciki. Muna gani ’yan jagaliya suka sace dukiyarmu,” in ji shi.
Umar Abdulmumin ya ce, duk da ya yi asarar kayayyakin da ba su gaza na Naira miliyan daya ba, sai da ya biya wasu ’yan jagaliya suka tsare masa shagon daga wadanda suke fasa shaguna suna sace kayayyaki.
Ya ce, “Sun balle daya daga cikin shagunan, amma na ci sa’a na iso kafin su sace dukkan kayan.
“Lokacin da na zo na dauki hayar wasunsu na biya su, su yi min gadin shagon, kuma na tsaya tare da su.”
Abdulmumin ya ce, ’yan kasuwa da dama sun yi irin wannan dabara don hana sace musu kaya.
’Yan kasuwar sun ce mutane da dama za su rasa abin yi, ganin dubban mutane ne suke samun abin yi a kasuwar kai-tsaye ko a kaikaice.
Sai dai babu daya daga cikin masu kula da shagunan da ke wajen don bayyana wa wakilinmu asarar da suka yi a rusau din, inda wasu daga cikinsu ba su je kasuwar ba lokacin da suka ji ana rusau din.
“Wasu daga cikinsu sun zo, suka tsaya suka ga abin da ke faruwa sannan suka tafi; yayin da sauran ba su ma zo ba. Na san daya daga cikinsu wanda ya cire kofarsa da kwanon rufi,” in ji wani mai wajen wanke motoci.
Ya kara da cewa, wasu wuraren masu rusau din ba su taba su ba, amma ’yan jagaliya sun mamaye su, sun rusa domin su sace kayayyakin ciki.
Aminiya ta samu labarin cewa ’yan jagaliya sun tafka sata a rukunin shagunan ’yan canji da ke harabar tsohon Kamfanin Buga Jaridun Triamph a ranar Lahadi bisa sa ran gwamnatin jihar za ta rushe shi.
’Yan jagaliyar sun farfasa ginin sun sace kayayyakin ciki kafin ’yan sanda su tarwatsa su. Sai dai daga baya sun sake taruwa sun ci karfin ’yan sandan, inda suka ci gaba da sace kayayyakin.
Aminiya ta ruwaito yadda sace-sace ke karuwa a jihar a baya-bayan nan, inda mutane suke korafin cewa ’yan daba suna damun su da sace-sace.
Aminiya ta samu labarin cewa, a titin zuwa filin jirgin sama kusa da Gidauniyar Rochas, an sace karafunan da ake dorawa a rumfunan bikin da jijjifin ranar Lahadi.
“Akwai yiwuwar sun zo ne da misalin karfe 3:00 na dare suka sace karafunan.
“Muna da mai gadi da ke tsaron titin, to amma titin na da tsawo, don haka mabarnatan suna iya kiwon motsin mai gadin.
“Na lura babu karfunan a inda suke da misalin karfe 5:00 na asuba, lokacin da na fito Sallah,” in ji wani dan kasuwa, Abdullahi Sulaiman.
Ya nuna damuwa kan yadda sace-sace suka karu a ’yan kwanakin nan, inda ya ce, “Ko ka hadu da masu kwace waya a hanya, ko miyagu su zo gidanka su sace duk abin da suka gani,” in ji shi.
A ’Yankaba da ke hanyar Hadeja, wani mazaunin yankin ya ce tun ranar Juma’a barayi suke kai musu farmaki a kullum, “Har ma sun sace karfen tsaron da muka kange injin famfonmu da shi,” in ji shi.
A wata sanarwa da Gwamnan ya fitar ta hannun Babban Sakataren Watsa Labaransa, Sunusi Bature, ya bayar da umarni ga ’yan sanda su kawo karshen “Ayyukan ’yan bola da suke yunkurin fasa shagunan mutane da sunan kwashe birbishin kayayyakin da suka lalace daga gine-ginen da gwamnatin jihar ta rushe da aka yi ba bisa ka’ida ba.”
Da aka tuntube shi kan asarar da ’yan kasuwar suka yi kan ko gwamnati za ta biya su diyya ko a’a, Bature ya ki cewa uffan.
Bayanai sun ce tuni ’yan sanda suka kama matasa kusan 50 da ake zargi da kwasar ganima a wuraren da aka rusa da sauran wuraren da suka kai farmaki, suka kwashe kayan mutane.
Abba da Ganduje na musayar yawu kan sayar da asibitin yara
A wani labarin, gwamnan jihar ya ce ya “Kwace Asibitin Yara na Hasiya Bayero da masaukin baki na Gwamna da ke gidajen Kwankwasiyya da aka sayar.”
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a hanzarta gyara asibitin kuma ya fara aiki a matsayin asibitin kwararru na yara.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a madadin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, tsohon Kwamishinan Watsa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Malam Mohammad Garba, ya musanta batun sayar da asibitin.
Ya ce, “An dan dakatar da amfani da asibitin ne sakamakon mayar da shi zuwa Asibitin Yara na Halifa Sheikh Isyaka Rabi’u da aka kammala – daya daga cikin ayyukan da aka yi watsi da su da gwamnatin Ganduje ta gada.
Ya ce, tsohon Asibitin Hasiya Bayero an shirya za a mayar da shi Cibiyar Jinyar Cutar Tamuwa ce, inda ya ce ginin har zuwa lokacin na gwamnatin jihar ne ba a sayar da shi ga kowa ba kamar yadda ake kokarin nunawa.
Ya kamata a ba wa jama’a lokaci kafin rusau — Kanawa
Al’ummar jihar da dama suna ganin ya dace kafin gwamnatin ta fara rusau din ta bayar da lokaci ga ’yan kasuwar su kwashe kayansu maimakon auka musu cikin dare.
Amma Malam Adamu Abubakar ya ce abin da gwamnatin ke yi na bisa ka’ida duba da cewa son zuciya ya jawo mutane suka sayi irin wadannan wurare.
Sai dai ya shawarci gwamnatin ta rika sanarwa tare da ba wa masu gine-ginen wa’adi kafin ta rushe.
Shi ma wani mai suna Abdullahi Sulaiman ya soki lamarin, inda ya yi kira ga gwamna jihar ya dakatar da rushe-rushen duba da cewa babu abin da hakan zai haifar sai koma baya ga tattalin arzikin jihar.
“Wannan ba daidai ba ne domin idan aka lura rushe-rushen ba abin da za su kawo sai tangarda ga cigaban jihar, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki,” in ji shi.
Ita ma Hajiya Hadiza Rabi’u ta nuna takaicinta game da abin da ta kira asarar dukiya da rushe-rushen ya haifar, inda ta shawarci gwamnatin ta dauki matakin kwace gine-ginen maimakon rushewa.
APC ta yi Allah-wadai da rusau
Babbar jam’iyyar adawa a Kano, APC ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana da “kai farmaki ne kan dukiyoyin al’umma” da gwamnatin NNPP a ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi a jihar.
A wani taron manema labarai da Jam’iyyar APC ta gudanar a karkarshin jagorancin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Alhaji Shehu Maigari, ta yi Allah-wadai da matakin da Gwamnatin Jihar ta dauka na yin rushe-rushe, inda ta bayyana haka da babbar annoba.
Alhaji Maigari ya ce, dole gwamnatin ta yi duba kan wannan abu da take yi na janyo wa mutane asara, inda kuma wasu suka rasa hanyar neman abincinsu.
Ya shawarci duk wanda rushe-rushen ya shafa su tanadi dukkan hujjjojnsu don neman hakkinsu a gaban kotu.
Har ila yau ya ja hankalin iyaye su hana ’ya’yansu biye wa ’yan Jam’iyyar NNPP suna amfani da su wajen sace kayayyakin al’umma da sunan ganima.
Duk mai bakin ciki da rusau din makiyin Kano ne – Kwankwaso
Jagoran Jam’iyyar NNPP kuma dan takarar Shugaban Kasa, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce duk wanda ke ganin laifin rushe-rushen da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yi a matsayin makiyin jihar.
“Kamar yadda wannan gwamnati ta yi alkawarin kwato filayen gwamnati da aka mallaka wa daidaikun jama’a a jihar nan, to ta cika alkawarinta.
“Domin mun san cewa ana daukar kayan gwamnati a ba wa al’umma su yi makaranta ko asibiti ko makabarta, amma ba a dauka a mallaka wa daidaiku ba,” in ji shi.
A cewar Kwankwaso, “Duk wanda yake bakin ciki da abin da gwamnatin nan ke yi na rushe wadancan wurare to in ma bai fahimci yadda abin yake ba, ko kuma shi cikakken makiyin Jihar Kano ne wanda ba ya son cigabanta.”
A guji yin abu don dadada wa mutum guda – Shekarau
Sai dai tsohon Gwamnan Jihar Malam Ibrahim Shekaru ya ja hankalin Gwamnatin Jihar ta tsaya ta yi duk abin da yake na daidai wanda zai amfani al’umma a maimakon yin abu don dadada wa wani mutum guda.
Mun shirya wa zuwa kotu – NNPP
Barista Bashir Tudun Wazirci shi ne lauyan Jam’iyyar NNPP ya ce rushe-rushen da gwamnatinsu take yi suna bisa ka’ida don haka a shirye suke su amsa duk wata tuhuma a gaban kotu.
A cewarsa Gwamnatin ba ta fara wannan aiki na rushe-rushe ba sai da ta samu yardar kotu a kan haka.
Daga: Clement A. Oloyede da Zahraddeen Y. Shu’aibu, Kano da Salihu Makera