Rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji ta kama wasu mutum biyu da ake zargin suna cikin masu daukar nauyin ’yan ta’adda a cikin wani banki a Zariyan jihar Kaduna.
Sojojin sun kuma ce jami’an tsaro sun fara neman wani mai suna Alhaji Abubakar ruwa a jallo saboda yana cikin masu taimaka wa ta’addanci.
Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro ta Kasa, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan, lokacin da yake yi wa manema labarai karin haske kan ayyukan rundunar a Abuja, ranar Alhamis.
Ya ce an kama su ne a cikin bankin Access da ke PZ a Zariya, lokacin da suke kokarin cire tsabar kudi har Naira miliyan 14 da aka zuba a asusun ajiyar wani Alhaji Abubakar.
Manjo Janar Danmadami ya kuma ce rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas ta hallaka wasu manyan kwamandojin ISWAP/Boko Haram a dajin Sambisa.
Ya ce wadanda aka kashe din sun hada da Abu Asiya da Abu Ubaida, kuma sun gamu da ajalin nasu ne a Parisu da Sheruri da ke dajin na Sambisa.
A cewar Kakakin, a tsakanin lokacin, sojoji sun kashe ’yan ta’adda 36, sun ceto fararen hula 130, sannan sun kama wadanda ake zargin ’yan ta’adda ne 46, sai kuma masu samar wa Boko Haram da kayyayki su 12.
Kazalika, ya ce dakarun sun sami nasarar kwato makamai da albarusai da bama-bamai da ma kudade masu yawan gaske daga hannun ’yan ta’addan.