✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka fatattaki ’yan bindiga daga dajin Kano — Ganduje

Ganduje ya ce a lokacin da yake mulkin Kano ya nemi taimakon Gwamnatin Tarayya wajen daƙile 'yan bindiga a jihar.

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce dole sojoji su mamaye dazuka domin kawo ƙarshen ’yan bindiga a Najeriya.

Ganduje, ya bayyana haka ne, yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, kan hatsarin tankar mai da ya yi sanadin rasuwar mutane da dama a makon da ya gabata.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaransa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya jaddada buƙatar ɗaukar matakai a kan ’yan bindigar da ke ɓuya a dazuka.

Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya yaba wa Gwamna Bago bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya a jihar duk da girmanta da kuma yawan dazukan da ke cikinta.

“Maganin wannan matsala shi ne mamaye dazuka, domin nan ne ‘yan bindiga suke buya.

“Me ya sa muke kare kanmu kawai maimakon mu kai musu farmaki? Lokacin da nake Gwamnan Kano, na roƙi Gwamnatin Tarayya ta bai wa sojoji damar mamaye dajin Falgore.

“Sojojin sun kafa cibiyar horo a can, kuma hakan ya sa aka fatattaki ’yan bindiga daga dajin. Yanzu haka Kano na zaman lafiya,” in ji Ganduje.

A nasa ɓangaren, Gwamna Bago, ya gode wa Ganduje da shugabancin APC bisa goyon bayansu.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gyara manyan titunan jihar, kamar hanyar Suleja zuwa Minna, domin rage haɗura da ƙara tabbatar da tsaro a jihar.