✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matsafa suka yi wa wani yaro kisan gilla

Kafin a ankara matsafan suka jefar da gawar yaron bayan sun debe jininsa a garin Jos

Wasu mutane da ke kyautata zaton matsafa ne sun yi wa wani yaro dan shekara bakwai, mai suna Umar Abubakar kisan gilla.

Bayanai sun tabbatar da cewa wadanda suka kashe yaron sun huda wuyansa ne da kwalba suka suka kwashe jininsa suka jefar da gawarsa a lungun wani gida.

“Da yin abun ba a fi minti biyar ba, aka ji sun jefar da shi a wani lungu. Wata mata a kusa da wajen ta ji kamar an zubar da shara ne, nan take ta turo wata yarinya don ta ga waye ya zubar musu da shara.

“Da yarinyar ta je sai ta ga yaro ne a mace shi ne ta je ta fada. Aka je aka kira ’yan banga suka zo aka dauko shi suka kawo gida’’, inji mahaifin mamacin, Malam Abubakar Dan Madiga.

— Yadda suka kashe raron

Lamarin ya faru ne bayan kakar yaron ta aike shi ya sayo mata abincin kaji, a unguwar Tudun Fera da ke garin Jos, Jihar Filato, da safiyar Alhamis din da ta gabata.

Mahaifin mamacin ya tabbatar wa Aminiya cewa an sun caka wa dan nasa kwalba ne a wuya aka kashe shi kamar yadda ake soke rakumi.

Lungun da aka tsinci gawar Umar Abubakar a yashe

Ya ce ba a ciri komai a jikinsa ba, amma da alama sun debi jininsa ne, domin babau jini a wurin da abun ya faru.

Ya ce yaron ko shayi ba a yi masa ba, saboda ba shi da lafiya. A cikin wannan wata ake son ayi masa.

— ‘Yadda muka kadu da wannan lamarin’

Kakar Umar wadda ita ce take rike da shi mai suna Zainab Sa’idu, ta bayyana wa wakilinmu cewa “na aiki wannan yaro ne ya sayo mani abincin kaji, domin na saba aiken sa, sai na ji an zo mini da wannan mummunan labari.

“Ba zan iya bayanin yadda na ji a zuciyata ba lokacin da na ji wannan labari.

“Na rabu da wannan yaro, na ce ya je ya sayo mani abincin kaji, amma sai aka dauko mani gawarsa, ba zan iya misalta abun da na ji a zuciyata ba, kan wannan al’amari’’, inji kakarsa.

Kakar yaron da aka kashe, Hajiya Zainab Sa’idu

Shi ma wan Umar mai suna Khalil Abubakar ya ce ya yi matukar kaduwa da abun da aka yi wa dan uwansa. Ya roki Allah Ya tona asirin wadanda suka yi aika-aikan.

— ‘Mun ga tsananin tashin hankali’

Mai Unguwar Tudun Fera, inda abun ya faru, Alhaji Yahaya Musa ya bayyana cewa sun ga tashin hankali, sakamakon faruwar wannan al’amari. Domin ba a taba ganin irin hakan ba a unguwar.

Ya ce da safe misalin karfe 7.30 yana kwance sai Kwamandan ’yan bangar unguwar ya kira shi a waya, ya ce ya zo ga wani abu ya faru.

“Da na zo sai na samu wannan yaro an kashe shi. Shi ne suka dauko shi, suka kai shi gida.

“Aka kira mahaifinsa ya zo ya gani aka yi masa wanka, aka yi masa sallah aka je aka binne shi”.

Mai unguwar ya roki Allah Ya tona asirin wadanda suka yi wa yaron kisan gilla.

— Shirin hana sake aukuwar hakan

Ya ce sun yi shiri na musamman da dattawa da ’yan banga don daukar matakai na ganin hakan bai kara faruwa ba a unguwar.

Ya yi kira ga iyaye mata su rika lura da kananan yara, a kuma daina barin su suna zama a waje suna wasa su kadai.

— ’Yan sanda su da labari

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ASP Ubah Gabriel, don jin ta bakin Rundunar kan wannan al’amari.

Amma jami’in ya ce masa zuwa lokacin da suke magana rahoton bai isa wajensu ba.

Sai dai  ya ce masa da zarar rundunar ta samu rahoton al’amarin za ta yi magana.