✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda matata da yarana 3 suka kubuta daga masu satar yara a Kano’

Matar ta tsere bayan da ta fahimci ana shirin sace ta.

Matsalar satar kananan yara na daya daga cikin abubuwan da ke ciwo mutane da dama tuwo a kwarya a Jihar Kano a ’yan kwanakin nan.

Iyalai da dama na cikin kunci da damuwa sakamakon satar wasu danginsu da aka taba yi a Jihar.

Ko cikin makon nan sai da aka sace wata yarinya mai shekara biyar a duniya, mai suna Hanifa Abubakar, a unguwar Kawaji, unguwar da ta yi kaurin suna wajen aikata ire-iren wadannan ayyuka.

Sai dai Hanifa ba ita kadai ce da aka taba sacewa a yankin ba.

Wani dan kasuwa a unguwar ’Yankaba da ke Kano, Muhammad Abubakar Muhammad, ya bayyana yadda matarsa da yaransa uku suka tsere daga hannun wanda suka sace Hanifa.

Ya ce “Lamarin ya faru ne ranar Talata, bakwai ga watan Disamba, lokacin da matata da yarana uku suka je siyayya a babban kantin Ado Bayero da ke titin gidan Zu a Kano, sun tsayar da mai Adaidaita Sahu da zai kai su bakin titi.

“Akalla kudin da za su biya zai kai Naira 300 amma direban adaidaita sahun ya ce ta bayar da Naira 100. Ta yarda suka tafi.

“Ba su jima da fara ra tafiya ba ta ji shi yana amsa waya yana cewa ‘an samu’ su hadu a inda suka saba haduwa, wanda ita ba ta gane me yake nufi ba.

“Da ta ji ba ta yarda da shi ba, ta ce ya sauke su amma sai ya nace akan lallai sai ya kai ta inda ta ce za ta je, hakan ya sa ta ce za ta masa ihu, nan take kuwa ya sauketa.

“Tana sauka ko kudinsa bai tsaya ya karba ba ya tsere a guje.

“Babba daga cikin yarana shekararta biyar, wadda idan ka hada ta da Hanifa za ka ce tagwaye ne. Wanda hakan ya sa mai dakina kaduwa lokacin da ta ga labarin bacewar Hanifa.

“Muna rokon Allah ya bayyana yaran da suka bace.”

Bacewar ko satar kananan yara, wani abu ne da ya jima yana addabar jama’ar Kano, musamman yankin unguwar Kawaji.