✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda matashi ya kashe bazawararsa ya yi wa gawarta fyade

Matsahin ya ce yana kokarin kare kansa ne a lokacin da abin ya faru.

Wani matashi da ake zargi da kashe bazawararsa ya kuma yi wa gawarta fyade ya shiga hannun ’yan sanda.

An kama matsahin mai shekara 23 bisa zargin sa da hallaka masoyiyar tasa mai shekara 46 wadda mijinta ya rasu ya bar da ta ’ya’ya hudu.

Ana tuhumar sa da kashe ta ne bayan gardama ta kaure a tsakaninsu, inda ya buga mata katako a kai sannan ya yi lalata da gawarta.

Gabanin haka, sai da ya buga wa dan matar mai shekara 13 katako a ka, har ya fita daga hayyacinsa.

Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru mai suna Peter ya ce mijin matar ta ya rasu ya bar ta da ’ya’ya hudu kuma tana zaune ne da karamin danta mai shekara 13.

Ya ce abubuwa ne suka cakude wa matar har ta kasa biyan kudin hayar gidan da take zaune a ciki tare da mijinta kafin rasuwarsa.

“Bayan da mijinta ya rasu al’amura sun dagule mata sai ta roki wani mutum da ke aikin gina gidansa bayan ya rufa kwanon gida, cewa ya ba ta daki daya a kangon ta zauna a ciki kafin ta samu kudin kama haya.

“A kangon take zaune da danta, kuma tana da saurayi birkila (matashin da ake zargi da kashe ta), an san ta tare da shi, yana zuwa wajenta a-kai-a-kai.

“Dan nata ya ba da labarin aika-aikar da saurayin ya yi mata ne bayan farfadowarsa a ranar Juma’a 16 ga watan Yuli, washegarin faruwar lamarin.

“Da farko sai da matashin ya buga wa yaron abu a ka, ya dauka yaron ya mutu.

“Bayan yaron ya farfado ne ya ba da labarin yadda matashin ya kashe  masa mahaifiya bayan ya buga mata katako a ka, ya kuma yi lalata da ita”, inji Peter

‘Ban yi lalata da gawar masoyiyarta ba’

Amma wanda ake zargin musanta zargin da ake masa na yin lalata da gawar bazawarar tasa.

Ya ce gardama ce ta kaure a tsakaninsu a kan siminti da ta nemi ya kawo mata, bayan ya kai mata kuma sai gardama ta kaure a tsakaninsu,  a kan aikin da take so ya yi mata da simintin.

Ya ce hakan ne yasa ya fita daga gidan amma daga bisani ya dawo ya tarar ta kulle gidan, sai ya haura ta katanga ya same ta a daki ita da danta.

A cewarsa dan nata ne ya fara fa rmasa da wuka, shi kuma a garin kare kansa ya ture yaron ya fadi ya buge kansa da bango.

“Da uwar ta ga haka sai ta tunkaro ni, sai na ture ta ita ma ta fadi ta buge kanta jini na ta zuba, sai na dauke yaron na daura shi bisa gado na fita na bar su; amma ban buga musu katako ba, ban kuma yi lalata da ita ba,” inji wanda ake zargin.

Muna bincike —’Yan sanda

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, Kontongs Bello ya tabbatar da aukuwar lamarin a kauyen Ogbekan na Karamar Hukumar Oredo a jihar.

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.