✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matashi dan shekara 19 ke kera tankunan man fetur

Isa Ali wanda ake kira “Small,”  wanda saboda karamin jikinsa aka lakaba masa wannan suna lokacin da ya fara koyon aikin yin walda yana da…

Isa Ali wanda ake kira “Small,”  wanda saboda karamin jikinsa aka lakaba masa wannan suna lokacin da ya fara koyon aikin yin walda yana da shekara takwas da haihuwa. Amma yanzu yana da shekara 19 kuma yana kera gidajen man fetur na zamani da kuma motocin dakon mai da na daukar kaya da sauransu.
  Matashin dan kabilar Igom ne daga kauyen Dungu da ke garin Begi ta Jihar Nasarawa. Kwatsam sai mahaifinsa ya ce zai kai shi birni daga kauye domin ya koyi aikin walda don ya dogara da kansa nan gaba a rayuwa. Duk da shi bai san me ye walda ba, don yana zaune ne a kauye. Da aka isa birni sai aka kai Isa wurin Oga Jona wanda yake yin sana’ar walda. Ganin Isa bai kai yin aikin kirki ba, sai aka mayar da shi ‘dan-aike, har aka sa masa suna Small.
 A ranar da ya fara zuwa koyon aiki, sai bai yi tambayi abinda da ake yi ko ba a yi a gun walda. Isa ya kura wa wutar walda ido inda bayan ya koma gida sai ido ya dames shi ya yi ta kuka har ya ki zuwa aiki da safe wai ya yi tawaye domin idonsa ya yi jajawur kuma yana yi masa ciwo. “Ashe wannan na daya daga cikin horon masu aikin walda inda ranar farko ba’a cewa dan koyo ya rufe ido yayin da za a hada karfe da wutar walda,” kamar yadda ya bayyana. Mahaifin Isa mutum ne tsayayye don haka ya kama hannunsa ya mayar da shi wurin walda bayan ya ladabtar da shi.
Daga nan aka gaya wa Isa cewa ana rufe ido ne yayin da ake yi setin hada karfen da za a yi wa walda da wutan lantarki don maganin hasken wutan walda. Sai aka ba shi gilashin ido don rage karfin wutan waldan. Daga karshe dai tsoron bulalan mahaifinsa ya sa “Small” ya dage da koyon aikin.
Ya ce Oga Jona ya shahara ne kan waldan kofofi da tagogin gidaje. Bayan ya shekara daya da rabi sai aka mayar da shi Jihar Kano yana dan shekara tara da ’yan watanni.
A nan ma saboda karamin jikinsa sai sunan “Small” ya bi shi. Domin ya yi kankanta kwarai a inda ake kera manyan tankunan daukan man fetur da na daukan kaya sannan suna kera gidajen mai na zamani masu kan fanfuna da dama. A nan ya shekara tara yana koyon aiki har ya kware ya zama gani-na-gwanaye.
 Bugu da kari a yanzu Isa ya zama babba, domin cikin kwanaki uku zuwa hudu yana iya kera tankin da ake binnewa a gidan man  mai cin lita dubu 40 da biyar idan an samar masa da faifan karfe, da rodi da tsinken walda da wutar lantarki da kuma janereto.
 Isa wanda a yanzu yana gina gidan man fetur na zamani a kan hanyar zuwa filin jirgin sama da ke Abuja wanda zai ci tankunan karkashin kasa 16 mai daukar lita dubu 45 kowanne.  
 Har ila yau, ya ce yana da masu taya shi aiki kamar irinsu Abdullahim Ahmad, wanda shi ma walda ne daya shekara takwas ya na koyo, da Yusuf Yusuf wanda shekarunsa uku a cikin aikin. Sai kuma Yakubu Dabid wanda mai aikin gini ne wanda saboda rashin aikin ya fara koyon aiki.
 Wani hanzari ba gudu ba, yadda aka horas da Isa yayin da ya fara koyon aiki, shi ma ya koya ma Yakudu Dabid darasi inda ya ki gaya masa ya rufe idonsa yayin aikin walda sannan ya sa madubi inda ya yi kwanaki biyu ya na fama da ciwon ido sannan aka samar masa da madubi.
Shi dai Isa yanzu yana aiki ne a yadin Agibawa da ke Kano na Alhaji Dauda Agibawa da ke Kumbotso, kuma suna zuwa ko ina don yin aikin walda. A yanzu Isa ya kusa kammala gina gidan man fetur na zamani a Abuja, inda ya ke kammala hada rumfar gidan man kafin su koma Kano ko kuma su nufi wani garin don yin aiki.
Ya ce idan aka ba shi mako guda zai iya kera sabon tankan daukan man fetur, ko babban motan daukan kaya wato Tirela. Sai dai zai so ya samu masu kama masa kamar mutum uku wandansa suka iya walda.
 Har ila yau, ya kara da cewa suna kera Tirelan daukan kaya a kan Naira miliyan biyu da dubu 300. Sannan ta daukan mai wacce ta fi wuya a kan Naira miliyan biyu da rabi wanda zai iya daukan man fetur lita dubu 40 zuwa 50.
 Wannan matashi ya ce hadarin da ya taba samu guda daya inda karfe ya soke shi a gefen ido har ya yi watanni biyu bai yi aiki ba. A yanzu ya ce ba ya jin dadi idan ya wuni bai yi aiki ba. Domin ba rowan shi da Sati ko Lahadi. Ya ce ya horas da matasa kamar hudu wadanda su ma sun iya yin aikin da duk zai yi. Ya ce idan ya na kera mota da yi mata fenti, sai dai mai hada wayoyi ya yi aikinsa sannan don bai ba iya mota ba, wanda ya iya mota ya sa kan Tirela ya tuka a tafi.
Isa duk da a yanzu ya shahara amma idan ya je kauye yana mutumci da tsohon maigidansa Oga Jona wanda har yanzu yake yin waldan kofofi da tagogi.