Ba shakka Ubangiji Ya albarkaci dan Adam sosai da samun intanet. Intanet ya kawo sauyi a duniya irin sauyin da ba a taba gani ba a shekarun baya.
Abubuwa sun saukaka: idan a shekara dari da suka wuce kafin ka iya isar da sako ga mutumin da ke nesa da kai zai dauke ka mako guda, to a yanzu cikin ikon Allah za ka iya isar da sakon nan a cikin wasu mintoci ko dakiku.
- Dalibi ya lakada wa malamar jami’a dukan kawo-wuka
- ’Yan sanda sun ceto dattijo mai shekara 80 da aka sace a Kano
Baiwar intanet ta kai matakin da a halin yanzu, wasu ma suna ganin saka kati a waya ka kira mutum ya zama tsohon “yayi.”
Abin da za ka yi shi ne ka yi amfani da datar wayarka don ka kira mutum ta WhatsApp ko Duo ko wata manhaja mai irin wannan sifa, ko kuma ka tura sako a rubuce ta hanyar kafofin sadarwa.
To ni wane abu ne ya fi jan hankalina game da al’amarin intanet a wannan zamanin?
A nan Arewacin Najeriya, muna fuskantar matsaloli iri-iri: rashin tsaro da rashin aikin yi da sauransu, wadanda suna daga cikin manyan-manyan dalilan da ke haddasa mana talauci.
Ga shi kuma wasu wurare a fadin duniya, intanet din nan an dauke ta a matsayin wata hanya ce ta neman kudi da kuma aikin yi.
Ma’ana, mutum zai iya amfani da intanet wajen neman na-kansa. Zai iya yana kwance a gida yana gudanar da ayyukan da zai sami kudi ba sai ya fita ya yi dako ko ya tafi ofis ba.
Tare da bayyanar annobar Coronavirus, al’amura da dama dangane da intanet sun fito fili ga jama’a.
A wasu kasashen ma, akwai ma’aikatun da ba sai ka je ofis ka yi aiki ba. Har a nan Najeriya, idon mutanenmu ya bude dangane da wannan.
Akwai aikace-aikace da mutum zai iya aiwatarwa ba tare da ya je ko kofar gidansa ba. Baya ga haka, ko taro za a yi a yanzu za a iya yin sa to Zoom ko Gmail saboda neman sauki.
Ba sai an kashe lokacin tafiya ba. Ba sai an kashe kudin mota ba. Ba sai an biya kudin otal ba. Ke nan muhimmancin yana da yawa sosai!
Ina na dosa?
Abin da nake son cewa shi ne, lokaci ya yi da mutanenmu za su rungumi harkar nan ta intanet hannu bibbiyu. Ko da aikin gwamnati kake yi, za ka iya yin wasu huldodin samun kudi ta hanyar kafar intanet.
Mutane da yawa suna yi. Alal misali, idan mutum yana da fasahar rubutu ko fassara ko hidimar sanar da shafin yanar gizo ko kuma idan mutum yana da fasahar sarrafa kwamfuta, zai iya samun damarmaki na samun kudi.
Babban abin da ke bukata shi ne a san ka. Da zarar an san ka kuma aka yaba da aikinka, to cikin ikon Allah za ka kai matakin da nemanka za a fara yi.
Wasu lokutan ma aiki sai ka zaba. Sai dai abin yana bukatar hakuri da kwarewa sosai, domin kwarewarka ita za ta ba ka lasisin yin irin wadannan ayyuka.
Bugu da kari, mutum zai iya amfani da dandalin bidiyon nan, wato YouTube, wajen neman kudi.
Idan kana da fasahar tsara kayatattun bidiyo, sannan ka cika wasu ka’idoji, to akwai abin da shi YouTube din yake kira da “monetisation”, wacce ita ce hanyar samun kudin ta hanyar mu’amala a dandalin.
A yanzu, mutum ko kaya yake sayarwa, zai iya amfani da kafofin sada zumunta wajen tallata hajarsa. Alal misali, akwai dumbin jama’a da ke amfani da WhatsApp ko Facebook ko Instagram ko kuma Twitter wajen tallata wa jama’a irin harkar da suke yi.
Kuma hakan tabbas yakan kawo kasuwa. Wani abu da zan ja hankali mai karatu kuma shi ne, da zarar ka tsinci kanka a kafofin sada zumunta na zamani, kar ka yi wasa wajen bayyana wa duniya irin fasahar da ka iya.
Saboda a haka ne wani zai gan ka ya san fasahar da kake da ita. A haka ne idan yana bukatar irin wannan fasahar, shi ke nan sai ka ga ya neme ka kun kulla harkalla ta arziki.
Saboda haka, shawara da nake bayarwa ga matasa ita ce, su daure sosai wajen saka kansu cikin hidimar intanet domin samun alfanu, tare da la’akari da cewa wadannan kadan kawai na kirgo.
Muhammad Sabi’u dan jarida ne kuma mai fassara, ya rubuto wannan muqala ce daga Bauchi. Za a iya samunsa ta tarho: 09078713542