Matasa sun yi wa wani jigo a jam’iyyar APC reshen Jihar Nasarawa tsirara bayan sun lakada mishi duka a bainar jama’a.
Matasan da ake kyauatata zaton magoya bayan jam’iyyar ne sun yi wa Abubakar Abu Giza dirar mikiya ne a lokacin babban gangamin yakin neman zabe da jam’iyyar ta shirya a jihar.
- Maroko da Portugal: Shin Afirka ta za kafa sabon tarihi a duniya?
- Qatar 2022: Argentina ta sha da kyar a hannun Netherlands
Shugaban Kwamitin Shawara na Jam’iyyu IPAC a Jihar Nasarawa, Cletus Ogah Doma, ya tabbatar da faruwar lamarin, bayan an yada bidiyon abin da ya faru da Giza a Lafia, hedikwatar jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan mummunan abin ya faru da Abubakar Giza ne a Fadar Sarkin Lafia a ranar Alhamis.
Mista Ogah Doma wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar ZP Reshen Jihar Nasarawa, ya ce babu dalilin yi wa dan siyasar tsirara a bainar jama’a, don haka ya kirayi masatan jihar da su nisanci dabanci.
Ya ce ya kamata a ce an wuce matakin irin wannan kidahumanci, sannan a matsayin matasa na kashin bayan kowace al’umma da hadin kanta, bai kamata ba su bari miyagun ’yan siyasa na amfani da su wajen aikata ba daidai ba.
Shugaban na IPAC, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da ma Jam’yyiar APC reshen jihar da su fito su yi Allah wadai da duk wani nau’i na dabanci da miyagun halayya da yunkurin kawo rabuwar kan al’umma.