Tun bayan zuwan kafafen sada zumunta na intanet irin su Facebook da WhatsApp da Twitter da Instgram da sauaransu, mata da dama sun zama ’yar kasuwa ta hanyar amfani da kafafen wajen saye da sayarwa da kuma tallata hajoji iri-iri.
Aminiya ta fahimci cewa ana gudanar da irin wannan salon kasuwancin ne ta hanyar sanya hotunan hajoji a gurbin sanya hotunan mai shafin.
Idan wanda ke da sha’awa ya gani, zai yi magana da mai sayar da kayan. Ta haka za su yi tattauna har su kulla ciniki su kuma yi musayar kaya da kuma kudi.
Mai son sayen kayan zai aika da kudin ta asusun bankin mai sayarwa wadda ita kuma za ta aika da kayan da aka saya bayan kudin sun shiga asusunta.
- Farashin kayan abinci ya fadi a kasuwar Saminaka
- Kotu ta daure mata kan yin alfasha da jariri
- Karin farashi: APC ta roki ’yan Najeriya su kara hakuri
Yayin da manyan kamfanoni ke amfani da kamfanonin jigilar sako ga jama’a wajen isar da kayan da aka saya ta irin wannnan hanyar, kananan kamfanoni da daidaikun mutane kan yi amfani da motocin haya a tasoshi daban-daban wajen aikewa da sakonnin kayayyakin da aka saya ga abokan cinikinsu.
Aminiya ta kuma gano cewa ana gudanar da wannan kasuwanci ne ba tare da mai saye da mai sayarwa sun san juna ba ko suna zaune a gari guda da juna ba.
‘Masu bukata na rububi’
Khadija Kabir ita ce shugabar kamfanin KK Fashion, wanda ke samar da dogayen rigunan mata a Kano.
Ta shaida wa Aminiya cewa tana sayar da kusan dukkannin hajojinta a irin kafafen sada zumunta.
“A gaskiya kafafen sada zumunta na zamani sun taimaka min kwarai da gaske wajen bunkasa kasuwancina.
“Ina tallata kayana a kusan dukkanin kafafen sada zumuntar da ake amfani da su.
“Da zarar na dora hoton rigunan da na dinka, za ki ga mutane sun nuna suna so, kai wani lokacin ma sai na kara dinka wasu saboda yawan mutanen da ke bukata”.
‘Na fi samun ciniki ta shafukan zumunta’
Hajiya Hussaina Muhammad ’yar kasuwa ce mai sayar da mayafai a cikin gidanta.
Ta bayyana cewa ta karkatar da kasuwancinta ne ta hanyar shafukan zumunta.
“Zan iya gaya miki cewa ina sayar da mayafaina masu yawa ta wannan hanya fiye da wadanda nake sayarwa a gida.
“Ina da abokan ciniki a kusan dukkannin garuruwan da ke fadin kasar nan.
“Idan mutum ya nuna sha’awar sayen kayana to zan tura masa lambar asusuna na banki, idan ya turo min kudi ni kuma sai na tura masa kaya.
“Ina hada kai da wasu direbobi a tashar Unguwa Uku wajen aike wa abokan cinkina kayansu.
“Nakan hada musu kaya tare da lambar wayar wadanda za a kai wa sakon kayan.
“Sannan kuma zan karbi lambar wayar direban motar na aike wa abokan cinikina don su yi magana a tsakaninsu idan direban ya isa garin.
“Idan direban ya kai kayan sai shi wanda ya amshi kayan ya biya wasu ’yan kudade a matsayin ladan kai masa kayan”.
‘Ta fida dacewa da mata’
Wata ’yar kasuwa da ke sayar da layan kwalliya a kafar sadarwa ta zamani mai suna Humaira Adamu, ta ce kasuwancin da ake yi ta kafafen sadarwa na zamani abu ne da ya dace da mata, duba da cewa akasarin rayuwarsu ta cikin gida ce.
Mace tana zaune daga cikin dakinta za ta yi kasuwancinta ba tare da ta fita wajen gidanta ba inda kuma za ta yi hulda da mutanen da ma ba ta san su ba kai tsaye.
“A koyaushe za ki same ni da wayata a hannu ba wai ina hira ko kallon fim ba, illa harkar kasuwancina da nake yi.
“Da zarar na tashi daga barci na yi sallah to abu na gaba da zan yi shi ne na bude wayata don na ga ko mutane sun nemi na tura musu hajata.
“Idan sun yi sai na ba su amsa tare da tura musu inda suke.
“A gaskiya ina samun kudi sosai da wannan kasuwancin nawa”, inji ta.
Ga sauki, ga biyan bukata
Firdausi Malam na daga cikin masu sayen kayyayaki ta kafafen sada zumunta.
Ta shaida wa Aminiya cewa ta rungimi sayen kaya ta wannan hanya sosai da sosai.
“Ina sayen kayayyaki da yawa a kafafen sada zumunta na zamani daga abin ya hada da sutura da talkalma da kayan kicin da sauransu.
“Kin san kasancewar masu sayar da kayayyakin ta wannan hanya suna zaune a garuruwa daban-daban don haka za ki samu cewa kayayyaykin da ake tallatawa a kafafen sada zumunta wasu daga ciki mutum ba ya samun su a garin da yake.
“Wani abin kuma shi ne za ki iya sayen kayan da arha idan kika kwatanta da farashin da ake sayar da kayan a kasuwa; wannan ma idan mutum ya yi sa’a ya samu kayan a garinsu ke nan”, kamar yadda ta bayyana.
‘Ba na damuwa da kudin dako’
Da aka tambaye ta ko ta taba samun matsala sai ta bayyana cewa, “A’a, da zarar na biya kudina to ina samun kayana a wannan ranar sai dai idan mai sayar da kayan na zaune a garin da ke da nisa kamar Legas, to shi ne zan samu kayana washegari.
“Kamar yanzu da nake sayen leshi daga wata abokiyar kasuwancina a Legas, idan ta dora hotunan leshinta zan zaba na tura mata kudi ita kuma ta turo min da kayana.
“Kuma kayan sun fi arha daga wajenta a kan na je na saya a kasuwa.
“Shi ya sa ma ni ba na damuwa da kudin da nake biya idan aka kawo min kayan saboda kudin ba su da wani yawa”, inji Firdausi.
‘Kasuwa huta’
Wata mai sayen kaya ta kafafen sada zumunta na intanet Zainab Sani ta shaida wa Aminiya cewa ta gamsu da sayen kaya ta wanann hanya domin ya dauke mata shiga kasuwa koyaushe.
“Ni gaskiya ina jin dadin wannan harkar domin ni ina kallon abin a matsayain wata mafita gare ni domin ni ba na son shiga kasuwa sosai.
Shi ya sa nake sayen kayana ta intanet.
An samu akasi
“Matsalar kawai da na taba samu ita ce wani lokaci da na sayi wani kaya sai na iske cewa akwai bambanci a tsakanin abin da na gani da wanda aka turo min.
“Tun daga wannan lokaci sai ya zama cewa idan na ga kaya a hoto to nakan bukaci a turo min hotuna da yawa domin na tantance da abin da zan saya”, a cewar Zainab.