Matafiya da dama sun makale a hanyoyin Bida zuwa Minna, da Bida zuwa Lambata da Bida zuwa Mokwa a Jihar Neja.
Hakan dai ya biyo bayan tare hanyoyin ne da direbobin manyan motoci suka yi suna zanga-zangar nuna takaicinsu da rashin kyawun hanya a yankin.
- Hotunan Bikin Nadin Sarkin Hausawan Badun
- Ciyo Wa Najeriya Bashi Zalunci Ne Da Bautar Da Na Baya —Sheikh Nuru Khalid
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, zuwa lokacin hada wannan labarin, an kwashe sa’o’I 24 babu abin hawan da ya shiga ko ya fita daga Bida saboda wannan mataki.
Bugu da kari, direbobin manyan motocin sun rufe gadar Gurara da nufin hana ababen hawa shiga ko fita daga babban birnin Jihar ta Neja, Minna.
‘Yara ba su je makaranta ba’
Matafiyan da abin ya shafa sun koka da yadda masu zanga-zangar suka yi wa gadar, wadda ta hade Lambata da Izom, kawanya.
Abubakar Musa, wani mazaunin Bida, ya shaida wa NAN ta waya cewa motocin haya da dama da suka fito daga Legas da wasu jihohi sun makale a garin.
A cewarsa, lamarin bai yi wa matafiya da mutanen gari dadi ba.
“Wannan mataki ya shafi harkokin kasuwanci, sannan yara da dama ba su samu damar zuwa makaranta ba.
“Wani abin dubawa kuma shi ne barazanar da ke tattare da kasancewar tankokin mai a wurin, musamman ganin wasu mutane suna shan sigari”, inji shi.
Babu mafita
Ya kara da cewa “DIrebobin sun ce wannan hanya tana da muhimmanci saboda ita ta hada kudanci da arewacin Najeriya, amma babu wata mabulla baya ga hanyar Bida zuwa Agaie zuwa Lambata wadda tuni ta lalace.
“Sun yi ikirarin cewa an yi kwanaki hanyar na wahalarwa matuka saboda ta kara lalacewa”.
Shi kuwa Alhaji Ahmad Ibrahim, wani matafiyi, cewa ya yi, “Na kwashe kusan sa’a 24 a Bida, a kan hanyata ta zuwa Minna daga Legas”.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Neja, Mista Monday Kuryas, ya ce jami’ansa za su tabbatar da doka da oda a yankin.
“Mun tura isassun jami’ai Lambata da Bida don su tabbatar da bin doka da oda”, inji shi.