Mata masu yi wa kasa hidima (NYSC) da aka tura Abuja sun koka kan tsananin tsadar haya.
Sun bayyana cewa tsananin tsadar kudin hayar ta sa ba sa iya biya, gas shi alawus din da gwamnati ke biyan su bai taka kara ya karya ba.
Wata ’yar NYSC mai suna Tina Joseph ta ce, “Bazan iya biyan kudin haya N500,000 ba, alhali alawus din da ake biya na N33,000 ne, kacal.”
Tina ta ciga da cewa, “Yawancin wuraren da (masu yi wa kasa hidima) suke yi wa aiki babu wurin kwanan, sai dai a ba ku dan kudin da ba zai ishe ku biyan kudin haya ba.”
Sakamakon hakan, yawancin mata ’yan NYSC a Abuja kan hada kudi ne da wasu matan su biya kudin hayar daki.
Amma sun bayyana cewa hakan kan jawo musu wasu wahalhalu a aikin nasu; Wani lokutan kuma, ejen din gidajen haya na amfani da damar domin cin zarafinsu. Wasunsu ke zama a gidajen danginsu ko abokan arziki na wucin gadi.
Sai dai kuma duk da haka, tsuguno bai kare ba, domin kuwa, wasu gidajen nesa suke da wurin aikin masu yi wa kasar hidima.
Dan alawus din da suke samu da bai taka kara ya karya ba, a kudin mota yake karewa — wani lokaci sai sun nemi ciko, ko su nemi abokan aikinsu masu abin hawa da za su rage musu hanya.
Amabel Keston ta ce, “Neman masauki ya matukar ban wuya, ga tsadar kudin haya, daki ciki daya da bandaki yana farawa daga N400,000 alhali alawus din da ake biya bai wuce 33,000 be, ta yaya mutum zai samu irin wannan kudin.
“Wurin zama a Abuja yana da tsada sosai. Na zo na sami karamin wuri a Biagi a kan N230,000, amma duk da haka akwai tsada sosai saboda zan yi ajiya alawus dina gaba daya don in sami damar biya. PPA dina na Dutse, kuma sai kashe kudin mota N600 zuwa N700 a kullum.”
Ita ma wata mai yi wa kasa hidima, Grace Omaye, ta ce, “Na wahala sosai wajen neman masauki, yawancin wuraren da gidaje ke da sauki suna fuskantar da matsalollin tsaro.
“Amma a karshe na sami daki ciki daya a Kubwa a kan N300,000, wurin da nake aiki kuma yana Wuse3.
“Zuwa wurin aiki yana da wuya sosai saboda kowace safiya dole in farka da wuri don gudun cunkoson ababen hawa.
“Ina kashe kusan N700 zuwa da dawowa a kullum. Gaskiya da wahala, amma dole ne in yi wa kasata hidima.”