✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mata ke sayar da katinan zabensu a Kano

Binciken Aminiya ya gano yadda mata ke sayar da katin zabensu kan N1,000 a Kano

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano yadda mata a Jihar Kano ke sayar da katinan zabensu kan N1,000.

Wasu mata da muka tattauna da su sun bayyana mana dalilan da suka sanya suka zabi sayar da katin da suka sha wahalar bin layin yin rajista da karbowa.

“Idan ba mu sayar ba yaya kike so mu yi? Wadanda suke zancen hanyar kwatar ’yanci ne, ba sai muna da rai za mu kwaci ’yancin ba? Ina ma ’yancin yake?

“Ba zai yiwu ba mu da shi kuma ba mai ba mu, sannan a ce kar mu sayar da abin da muke da shi don ciyar da ’ya’yanmu.

A nata bangaren wata mata da maigidanta ya rasu ya bar ta da ’ya’ya uku, ta ce da fari ta ki sayarwa, amma daga baya da rashin kudi da yunwa suka yi yawa, suka sa ta sayar.

“Ni dai da daraja, wata matashiya ta zo har gida ta sayi nawa, N5,000 ta ba ni.

“Maganar saba wa doka kuma wadanda suka yi dokar sun yi wacce za ta dinga daukar nauyinmu ne?

“Ni dai ba zan kashe kaina da yara ba saboda katin zabe; Idan gwamnati na so mu daina sai ta samar mana hanyoyin ciyar da ’ya’yanmu,” in ji ta.

Rahotanni na nuna cewa, a duk kakar zabe, wasu ’yan siyasa na amfani da halin rashi da talakawa ke ciki, don sayen katinansu aikata magudin zabe.

Sayen katin zabe ‘taimakon’ ne —Matashiya

Wata matashiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce sana’arta ke nan a duk lokacin da zabe ya gabato, kuma tana samun kudi sosai da ita.

Ta ce, “Abin hawa hawa ake yi, akwai bangaren maza akwai na mata, amma kin san mata mu muka fi fita karbar katinan.

“Kowane dan siyasa da tsarin da yake bi wajen saya, amma mu ba mu da ikon ganin su kai-tsaye don mu kanmu ba mu san su wane ne ke aiko da kudin sayen ba. Yaransu ke neman mu su ba mu adadin da suke so da nawa za su ba mu.

“Daga nan mu kuma za mu shiga lunguna da sako da talakawa masu bukatar kudin suke mu saya mu ba su. Amma ban san me za su yi da shi ba.

“Ni a ganina ma taimakon wadanda muka saya a gurinsu muke yi saboda yawanci ba su da cin yau, ba su da na gobe, dan abin da ka ba su da shi za su ci abinci. Kin ga ai mun taimaka musu.”

Idan za a iya tunawa dai, a rahotannin Aminiya na baya, mun kawo muku yadda kotu ta tsare wasu mata da ake zargi da cinikin katinan zabe a unguwar Danbare da ke karamar hukumar Kumbotso.

Ko a watan da ya gabata, sai da kotun Majistare mai lamba 70 a Jihar Kano ta daure wani Shugaban Jam’iyya na garin Yautan Gabasawa a Karamar Hukumar Gabasawa bisa samun sa da laifin mallakar katunan zabe 367.

Cinikin kuria ba ya maganin talauci – Masani 

Farfesa Kamilu Sani Fagge na sashin nazarin kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero ta Kano, ya ce masu sayar da katinansu su kwana da sanin cewa, kudin da suke karba ba zai magance musu talauci ba, kuma shi ke sake jefa su a mawuyacin halin da suke ciki.

“Babbar matsalar sayar da katin zabe shi ne kawo gurbatattun shugabanni, domin wanda ya san ba shi da abinda zai yi wa mutane ne ke sayen kuri’arsu, kuma idan ya zuba kudi ya zama hannun jari a gurinsa, don haka idan ya hau karagar mulki , ko ya kama madafun iko, sai ya ga ya ci ribar kudin da ya kashe.

“Shi ya sa dimukuradiyyar ba ta biyan bukata a Najeriya. Kuma hakan dori ne kan zubar da mutuncin kasar a idon duniya, domin abu ne da ba a boye ake yinsa ba, a bude ne.Ana kallonmu har yanzu ba mu gane bambamcin hagunmu da damanmu ba, ba mu san inda ya ke mana ciwo ba”.

Mafita

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce dokar Najeriya ta riga ta samar da riga kafin matsalar da tuntuni ya kamata a ce an fara aiwatarwa.

“Da tuntuni ana ladaftar da wadanda ke yi, da mutane sun ji tsoro sun daina, amma saboda wadannan(gurbatattun) manyan, za ki ga an kama mutum da kuri’a, amma saboda da wani a bayansa da ya saka shi, sai a kyale shi.

Ga sauran al’umma kuma  amfitar ba ta wuce dagewa da wayar da kai ba, don a ranar zaben ma ana samun masu sayen kuri’a, wani loakcin da kudi wani lokacin da kayan abinci ko na sakawa.

“Jami’an tsaro kuma sai sun saka ido sosai a lamarin; Kuma nasarar hakan za ta samu ne idan sun kalli kansu a matsayin jami’an tsaro na alumma ba na shugaban kasa ko wani mai babbabn matsayi ba”, in ji shi.