Kwacen waya na kara zama barazana ga duk wani mazaunin Kano da ke rike wayar hannu.
Kofar Dan Agundi, Kofar Famfo, Tal’udu, Kaguba, Ibrahim Taiwo Road da sauran lunguna da sako na Kano sun zama wuraren da suka yi kaurin suna wajen kwacen waya ba dare ba rana.
- Budurwa ta rataye kanta a Kano
- Rikici: ’Yan sanda sun kashe matasa 2 a Kano
- Iyayen matasan da ‘yan sanda suka kashe a Kano na neman hakkin ‘ya’yansu
- Masu yi wa kasa hidima sun kamu da COVID-19 a Kano
Da misalin karfe 11 na dare, a kan titin Ibrahim Taiwo wanda yake daya daga cikin tituna masu yawan ababen hawa a cikin birnin Kano, Bello Sagir, mazaunin garin Kano kuma kwararren mai fassara, jim kadan da kammala waya sai ya hangi wani matashi ya sauka daga babur mai kafa uku.
Ba zato ba tsammani sai wani matashi ya fizge wayar da Bello ke kokarin sakawa a aljihu.
Sai dai Bello ba zai iya komai ba, ganin irin wukar da matashin ke rike da ita, wadda zai iya yi masa rauni idan ya yi wani yunkurin karbar wayar.
Shi ma Abdulmalik Shu’aib, irin haka ta faru da shi inda masu kwacen wayar suka yi awon gaba da wayarsa kirar Infinix X4 wadda kudinta ya kai N70,000.
“Ba mu wayarka ka tsira da lafiyarka”, cewar masu kwacen wayar.
Yanzu masu kwacen waya a Kano na cin karensu ba babbaka, kuma a wasu lokutan idan mutum ya yi musu gardama wajen kwatar wayarsa sukan caka masa wuka kai tsaye sannan su tafi da ita.
Mutane da yawa sun samu raunuka, wasu kuma sun rasa rayukansu baki daya sanadin kwacen waya.
Me ya sa kwacen waya ke karuwa?
Muktar Nura malami ne a Sashin Nazarin Tsaro a Makarantar Cigaban Ilimi ta Jami’ar Bayero da ke Kano, ya danganta yawaitar kwacen waya a garin da yawan talauci, shan kayan maye, rashin aikin yi, rashin cikakken ilimin addinin Musulunci, da sauransu.
“Talauci, rashin aiki, rashin ilimin addini da shaye-shaye na kadan daga cikin abubuwan da ke jefa su harkar kwacen wayar.
“Wannan ya faru ne saboda yadda a lokuta da dama masu aikata wannan laifi ba sa cikin hayyacinsu na hakika kuma suna son biyan bukatunsu”, inji Nura.
Ya kara da cewa idan aka lura za a ga cewa masu aikata irin wadannan laifuka ba wani cikakken ilimin addini ko tarbiyya gare su ba.
Kazalika, ya ce su wadanda ake wa kwacen wayar suna da nasu laifin: Sau da dama sukan fito da manyan wayoyi masu tsada suna burga da su yayin da suke kan hanya, wanda a cewarsa hakan na tunzura masu irin wancan hali aikata kwacen.
Ya kara da cewa wuraren da ake sayen ire-iren wayoyin da aka kwace ko sato yana taimaka wa masu aika laifin wajen sake yin laifuka cikin sauki, tun da sun san cewa da zarar suka kwaci waya akwai in da za a saya ba tare da bata lokaci ba.
Wane mataki mahukunta suka dauka?
Mataimakin kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Sule Balarabe, ya bayyana cewa sun kama sama damutum 60 da ake zargi da kwacen waya, wanda aka kama a wurare daban-daban a fadin jihar.
Sannan rundunar ‘yan sandan Kano ta shirya, taron wayar da kai ga masu sana’ar saye da sayar da wayoyi, domin dakile sayen wayoyin sata a jihar.
Da yake Magana dangane da irin gudunmawar da gwamnatin jihar ke bayarwa, wajen dakile yaduwar irin wadannan ayyuka na bata gari, kakakin gwamnan Kano Abba Anwar, ya ce gwamnatin tana ba wa jami’an tsaro dukkan gudunmawar da suke bukata wajen magance matsalar tsaro a jihar.
Ya ce gwamnatin ta dasa na’urorin CCTV a wurare daban-daban a fadin jihar domin ganin abubuwan da ke gudana.
“Irin wadannan laifuka sun zama ruwan dare a duniya baki daya, amma duk da haka gwamnatin Ganduje ta na iya bakin kokarinta wajen magance matsalar tsaro.
“An samar wa da daruruwan matasa ayyukan gwamnati, sannan gwamnati ta gina cibiyoyin koyar da sana’o’in dogaro da kai, wanda ake koyar da sana’o’i sama da 24,” inji shi.
Ya kara da cewa gwamnatin Ganduje tana ci gaba da kokari wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a fadin Kano.
Ina mafita?
Mukhtar Nura, ya ce dole gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da jama’ar gari su zauna domin nemo mafita, ta hanyar kirkiro hanyoyin da za su cire matasa daga cikin kangin talauci.
Ya ce dole ne a samar wa da matasa ayyukan yi, sannan a samar da sana’o’in dogara da kai tare da ba da tallafi ko jarin da za su kama sana’a.
“Dole ne iyaye, gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki su dauki bigiren magance matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa”, cewar Nura.
Kamar yadda ya bayyana, ya ce akwai bukatar yin nasiha, fadakarwa ga matasa, sannan kuma dole ne gwamnati ta yi doka ga masu sana’ar saye da sayar da wayoyin da ba sabbi ba.