Wasu da ake zargin masu tara kudaden shiga ne sun yi sanadiyyar mutuwar wani direban babbar mota a Bridgehead, Onitsha, Jihar Anambra.
Shaidu sun ce masu karbar harajin sun bi matashin direban mai shekara 25 ne a guje, har motar ta kwace masa ya yi karo da wani shinge da aka yi na kankare.
- An ceto matar da ’yan uwanta suka kulle watanni 5 a daki
- An cafke mai wankin motar da ya tsere da motar kwastoma
- Gwamnati ta fara biyan ’yan ga-ruwa da direbobi tallafi
An garzaya da matashin a suma zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ya mutu, lamarin ya fusatsa wasu matasan yankin suka tare babbar hanyar suka yi ta kone-kone kafin daga baya a lallashe su.
Kakakin ’yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, John Abang, ya ba da umarnin gudanar da bincike a kai.
Mohammed ya ce: “Ranar Lahadi mun samu rahoton mummunan hatsarin mota a kan babbar hanyar Asaba-Onitsha wanda ya ritsa da babbar mota kirar Marsandi 911 mai lamba, ACA-178-XA, dauke da katakai ta wani mai suna Michael Okorie da ke Oduma a Karamar Hukumar Aninri ta Jihar Enugu.
“Hatsarin ya faru ne lokacin da motar ta kwace wa direban wanda ake zargin masu karbar haraji da ke aiki a Headbridge, Onitsha, sun biyo shi a guje ya daki shingen kankare a da Kasuwar Coca-Cola.
“Sakamakon haka ya sume kuma ’yan sintiri da ke sashin Okpoko suka garzaya da shi asibitin Toronto inda likita ya tabbatar da mutuwarsa”, inji shi.