Yayin da wa’adin daina amfani da tsofaffin kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya saka ya kusa cika, kasuwar masu cuwa-cuwar sabbin takardun kudade na ci ba kama hannun yaro a Jihar Yobe.
Bayanai sun nuna a Damaturu, babban birnin Jihar, irin wadannan masu canjin kan canza kowace Naira 10,000 a kan dubu guda.
- Bacewar N100,000 ta sa dalibin jami’ar Akure ya rataye kansa
- Ba don mu karya mutane muka kirkiro canjin kudi ba – Buhari
A bayanan da Aminiya ta tattara a karshen mako, ta gano cewar, mutanen, wadanda akasarinsu matasa ne sukan tsaya a gefen banki dauke da sababbin kudaden da kuma na’urar cire kudade ta POS.
Sai dai duk da haka, mutane na tururuwa wajen su saboda yawan layin ciran kudi daga injunan banki na ATM yadda suke karbar katuna nasu, suna cire musu kudaden.
‘Kwana muke a ATM saboda mu same su’
Aminiya ta tambayi wani matashin da ke da sabbin kudaden kan yadda ya same su, inda ya ce kusan kwana suke yi a ATM don neman kudaden.
Ya ce a haka suka bi har suka tara wadannan kudaden.
Wani mutum da ya nemi a sakaya sunansa da yake kokarin shi ma a ba shi wadannan sabbin takardun kudaden, ya ce ya shafe sama da awa biyar kuma duk da haka akwai sama da mutum 30 a gabansa a layi.
Ya ce, “To ai ka ga idan ya ci gaba da zama a layi lamarin sai ya baci, tunda ko cefanen abincin rana ban yi ba.
“Don haka tilas ta sa zan karbi kudin tare da biyan wannan caji lura da cewar, hakan zai fi min sauki tun da mafi yawan ’yan kasuwa ba sa karbar tsoffin kudaden,” in ji mutumin.
Sai dai mutane da dama sun ce suna cike da shakku a kan hakikanin hanyoyin da wadannan matasa ke bi wajen samun kudaden, sannan suke tsayawa a bakin bankunan don yin hada-hada.
Wasu dai na zargin bankunan da hada baki da irin wadannan matasan wajen karkatar da irin wadannan kudaden, lamarin da ya sa har yanzu suke wahala a hannun jama’a.