✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a Zamfara

Al'ummar sun ce rashin ruwan sama babbar matsala ce shi ya sa suka ga dacewar yin addu'a.

Al’ummar garin Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara, sun gudanar da sallar roƙon ruwa bayan da aka shafe kwanaki ba tare da an samu ruwan sama ba.

Mutane da dama sun fara nuna damuwa saboda har yanzu babu ruwa ba, duk da cewa an shiga lokacin damina tun da daɗewa.

Wasu manoma da ke jiran ruwa domin su yi shuka sun ce har zuwa ranar Laraba sun fito domin roƙon Allah Ya saukar da ruwa.

Babban limamin garin Kaura, Malam Badamasi, ne ya jagoranci sallar.

Ya ce sun ga dacewar yin wannan addu’a ne domin tun mako biyu da suka wuce ba su samu ruwa ba a garin.

Sheikh Malam Muhammad ya yi wa jama’a wa’azi mai ratsa zuciya, inda ya tunatar da su muhimmancin komawa ga Allah da yawaita ibada a irin wannan lokaci na fari da rashin ruwa.

Daga cikin waɗanda suka halarci sallar akwai Abdul Hadi Ibrahim Mai Yadi da Kasimu Namadi.

Sun ce sun zo domin neman gafara daga Allah da fatan zai saukar da ruwa.

Sun bayyana damuwarsu da cewa mako biyu kenan ba a yi ruwa a yankinsu ba, kuma ruwan da ya zo a baya bai wadatar wajen yin shuka ba, sai kuma ya ɗauke gaba ɗaya.

Sun ce fari na ruwa babbar matsala ce ga kowa, ba wai manoma kaɗai ba.

“Wannan musiba ce da ya kamata kowa ya tashi tsaye ya roƙi Allah Ya kawo sauƙi,” in ji su.