✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mamayar Boko Haram ta tilasta wa dubban ’yan Geidam barin garinsu

Tsofaffi da kananan yara sama da 2,000 sun yi tafiya mai tsawon gaske domin tsira da rayuwarsu.

Har yanzu mayakan kungiyar Boko Haram na ci gaba da tafiyar da akalar garin Geidam na Jihar Yobe tun bayan mamayar da suka yi ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce lamarin ya tilasta wa dubban ’yan garin barin gidajensu tare da yin kaura zuwa garuruwan Yunusari da kuma Damaturu, babban birnin jihar domin neman mafaka.

Sama da mazauna garin 2,000 ne, ciki har da kananan yara da tsofaffi suka yi tattaki mai tsawon gaske domin tsira da rayuwarsu.

’Yan ta’addan, wadanda suka yi zaman dirshan a tsakiyar garin sun shafe sama da sa’a 48 suna ba-ta-kashi da sojoji.

Mazauna garin sun shaida wa wakilinmu cewa ’yan ta’addan na cika bakin cewa za su tashi sansanin sojojin garin.

Yadda wasu daga cikin mutanen garin ke yin kaura bayan harin na Boko Haram.

To sai dai rahotanni sun ce sojojin sun ja daga, ko da yake suna matukar taka-tsan-tsan wajen ganin cewa ba a kashe musu jami’ai ba.

Ko a ranar Asabar, sai da mutum 11 ’yan gida daya suka mutu a garin bayan wani bam da yake hakon ’yan ta’addan ya fada gidansu.

An dai yi jana’izarsu ranar Lahadi a Damaturu bayan mutanen gari da ke kokarin guduwa sun kai gawarwakinsu can.

Mayakan Boko Haram dai sun kutsa Geidam ne ta yankin Gabashin garin a ranar Juma’ar da ta gabata a cikin motoci kirar Hilux sama da 20 da kuma wasu motocin yaki.

Wakilinmu ya rawaito cewa bayan ruwan wutar da sojojin sama suka yi musu ta sama da kasa, ’yan ta’addan sun ja da baya, amma daga bisani suka sake dawowa suka ci gaba da ta’asa a garin.

Maharan sun kuma datse manyan hanyoyin sadarwar a garin mallakin kamfanonin MTN da Airtel, sannan suna ci gaba da fasa shaguna suna dibar kayan jama’a.