Zubairu Yusha’au mai shekara 13 kuma da na biyu daga cikin ’ya’yan Malam Yusha’u da ke kauyen Lakkau a karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe an raba shi da kauyensu ne zuwa almajiranci a makarantar Malam Sirajo da ke Unguwar Kagarawal a garin Gombe shekara 3 da suka gabata shi da kanensa mai shekara 7 jim kadan da rasuwar mahaifiyarsu.
Ranar 3 ga Maris din nan, rana ce da Zubairu ba zai taba mancewa da ita a rayuwarsa ba, domin kamar kowace rana da yake fita zuwa barar abinci, a ranar ya shiga wani gida inda ya ga wata tsohuwar waya (kirar Techno) a yashe sai ya dauka bisa tsammanin marar amfani ce zai yi wasa da ita.
Bayan kwana uku da faruwar haka sai wata mata ta zo makarantar Malam Sirajo tana karar Zubairu da dauke mata wayarta lokacin da ya shiga gidan bara.
Zubairu yana jin haka nan take ya dauko wayar ya kawo ya ba da hakuri ya ce shi ya dauka ba mai amfani ba ce an yasar ne shi ya sa ya dauka don ya yi wasa da ita. Ashe wannan waya ce za ta zamo silar da zai rasa hannunwansa daga baya.
Da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe da ke Gombe, malamin almajirin Alaramma Malam Sirajo Mohammed, ya ce shi da kansa ya daure hannuwan almajirin da igiya a makarantar saboda ya ladabtar da shi bisa ga laifin zarginsa da satar waya, kuma bayan kamar awa daya sai aka yi masa sallama cewa Malam hannun yaron nan ya kumbura shi ne sai ya ce a kunce shi.
Ya ce kafin a kunce shi ya yi ta murza hannun yana kokarin ya kunce ya gudu shi ne hannun ya yi rauni sai suka kunce shi suka fara yi masa magani.
Malam Sirajo, wanda ya ce yana da almajirai 1,500 kuma shekararsa 50 inda ya shafe shekara 27 daga ciki yana karantar da almajirai bai taba samun wata matsala da kowane almajiri ba, sai a wannan karo.
Ya ce lokacin da abin ya faru sai ya sanar da mahaifin yaron Malam Yusha’u halin da ake ciki, ishi kuma ya ce ya yafe kuma ya dauki hakan a matsayin kaddara da za ta iya fadawa a kan kowa.
Malamin ya ce tunda aka kawo yaron wurinsa a matsayin almajiri bai taba zuwa ganin gida ba, sai dai mahaifinsa ne yake zuwa duba shi.
Malam Sirajo, ya bai wa malamai shawarar cewa duk horo ko hukuncin da mutum zai yi ya yi shi cikin tausayawa kuma duk abin da ya same ka, ka dauke shi a matsayin kaddara daga Allah ba wai ka ce wani ne ya dora maka ba.
Ya ce duk darajar mutum ba ta kai ta Annabawa ba, Annabi Yusuf (AS) jarrabawa ta same shi inda ya shekara tara a kurkuku don haka ya ce yana godiya ga Allah da Ya yi shi Musulmi kuma ya yarda da kaddara kuma yana kan hanya ta shiryar da al’umma.
Malam Sirajo, ya ce wannan hukunci da ya yi wa yaron bai yi daidai ba inda ya kara kira ga sauran Malaman Tsangaya cewa duk abin da ya faru da almajirai su rika yin hukunci da sauki kada su hau dokin zuciya.
Da yake zantawa da wakilinmu a gadonsa na asibiti, almajiri Zubairu, ya ce wata rana ce ya shiga gidan sai ya ga waya a kasa bai dauka mai kyau ba ce, sai ya dauka da niyyar ya yi wasa da ita.
Ya ce bayan kwana uku sai ya ji malaminsu yana magana da mai wayar cewa an sace mata waya a gidansu, “Shi ne da na ji sai na ruga a guje na dauko wayar na kawo mata, malamin namu bai ji dadin abin da na yi ba, sai ya ji haushi ya ce in nemo igiya in kawo, da na kawo shi ne sai ya daure min hannuwana duka biyu,” inji shi.
“Bayan ya daure ni sai ya bar ni a rana a wannan lokacin ina ta kokarin kuncewa har hannun suka yi tsami na gaji sai aka kai ni asibiti ina bude idona a gadon asibiti sai na ga hannuwan duka a yanke,” inji Zubairu.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Mista Shina Tairu Olukolu, wanda ya gabatar da Malam Siajo ga manema labarai a ofishinsa ya ce suna ci gaba da bincike kan lamarin don gano gaskiyar batun.
Mista Shina Tairu Olukolu, ya ce suna ci gaba da binciken lamarin har zuwa lokacin da za a sallami yaron daga asibiti sannan a san matakin da za a dauka kafin a tura Malam Sirajo zuwa kotu.
Hukuncin da malamin ya yi wa almajirin bai dace ba – Alarammomi
Wani alaramma wanda ya ce yana da almajiran da suka kai 50, mai suna Alaramma Malam Musa da ke Bolari, Gombe ya bayyana hukuncin da malamin ya yi wa almajirinsa da cewa bai dace ba domin hukuncin ya yi tsanani lura da shekarun yaron.
Alaramma Malam Musa, ya ce a shekarun baya idan almajiri ya kangare ba irin hukuncin da ake yi masa ba ke nan, ana daure shi ne da mari (sarka) a kafa a hana shi yawo ana ba shi abinci zuwa wani lokaci.
Malamin ya ce duk da wannan malami ba ya yi da wata muguwar niyya ba ce amma ya kamata ya lura da karancin shekarun almajirin yayin yi masa hukunci.
Shi ma Malam Tasi’u wani malamin Tsangaya da yake da almajirai, cewa ya yi tsautsayi ne amma wadansu malaman suna yi wa almajirai horo ne daidai da yawan shekarunsu.
Malam Tasi’u, ya ce duk abin da aka ce tsautsayi ba yadda aka iya “Amma dai hukuncin ya yi tsanani, bai kamata malamai su rika hukunci cikin fushi ko bacin rai ba,” inji shi.
Sai ya bai wa malamai ’yan uwansa shawarar cewa su rika kiyayewa saboda abin da ya faru da wannan malami ya zama darasi gare su.
Za mu kwato wa almajirin hakkinsa – Gwamnati
Wani ayari na Gwamnatin Jihar Gombe a karkashin jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Alhaji Abdulhamid Ibrahim danmalikin Akko ya ziyarci almajirin a gadonsa na asibiti a Asibitin Koyarwa na Jihar, inda ya ce gwamnati ta dauki nauyin jinyar Zubairu Yusha’u kuma ta yi alkawarin bi masa hakkinsa.
Kwamishinan ya shaida wa mahaifin yaron cewa Gwamna ne ya turo su kuma ya ce gwamnati ba za ta yafe ba, duk abin da ya kamata a rayuwa za ta yi wa yaron don ganin ya tsaya da kafafunsa.
Kwamishinan ya ce Ma’aikatar Shari’a da ta Harkokin Mata suna bin diddigin lamarin don bi wa yaron hakkinsa idan suka gama tattara bayanai za su bar shari’a ta yi aikinta a kan malamin don ya zama darasi ga wadansu.
Ya ce Gwamnan ya damu da halin da Zubairu yake ciki shi ya sa cikin gaggawa ya ce shi da Kwamishinar Ma’aikatar Mata, Misis Rabi Daniel su wakilce shi su kuma ci gaba da bin sawun lamarin har zuwa karshe.
Ya kara da cewa duk wani abu da ya kamata gwamnati za ta yi masa idan likitoci suka duba shi suka ga ya kamata a yi masa hannun roba da zai taimake shi wajen gudanar da wasu ayyukansa, to gwamnati a shirye take ta yi masa.
Sai ya ja hankalin malaman Tsangaya cewa su lura da irin horon da suke yi wa almajiransu inda ya ce ko da ya tabbata wannan yaro satar wayar ya yi, hukuncin da aka yi masa ya yi tsanani ya wuce girman laifin da ya aikata.
Mahaifin almajirin Malam Yusha’u Abubakar, ya gode wa gwamnatin kan yadda ta shigo don taimaka musu inda ya ce ba su da karfin daukar nauyin jinyarsa.
Malam Yusha’u Abubakar, ya ce shi ya kawo yaron almajiranci saboda sun saba ana kawo masa yara yana karantarwa amma daga faruwar wannan lamari ya cire kanen Zubairu daga makarantar ya mayar da shi gida za su ci gaba da karantar da su a gida.