✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda makaho ya nakalci Naira ‘Nakan iya tantance kudi da zarar na taba su’

Aminiya ta sami tattaunawa da wani makaho mai suna Munka’ilu Usman, mai kimanin shekaru 60, wanda ya nakalci Naira, kuma yake iya tantance ta da…

Munka’ilu Usman ke nan a yayin da yake kirga NairaAminiya ta sami tattaunawa da wani makaho mai suna Munka’ilu Usman, mai kimanin shekaru 60, wanda ya nakalci Naira, kuma yake iya tantance ta da zarar ya taba ta. Sannan yana iya kirga kudi komai yawansu tare da bambance su ba tare da wani bata lokaci ba:
Za mu so ka gabatar da kanka?
Ni dai sunana Munka’ilu Usman, an haife ni a kauyen Diginsa da ke Birniwa ta Jihar Jigawa kimanin shekaru 60 da suka wuce. Ban yi karatun boko ba, amma na taba karatun Alkur’ani. Na taba aure, amma mun rabu da matar. Ina da ’ya’ya uku yanzu. Na gamu da lalurar makanta tun ina dan kimanin shekaru biyu a duniya. An ce ciwon agana ne ya kama ni, sakamakon haka na makance.
Ya ake kake iya tantace kudi?
Wannan wata baiwa ce ta Ubangiji, domin ni ban taba ganin kudi a rayuwata ba. Na gaya maka tun ina dan yaye na gamu da lalurar makanta. Nakan iya tantance kudi tare da bambance su da zarar na taba su. Da na taba Naira biyar ko Naira goma ko Naira ashirin ko Naira hamsin ko Naira dari biyar ko Naira dubu zan gane. Ita Naira 20 ta fi Naira 50 santsi; haka Naira 10 ta fi Naira biyar santsi. Sannan akwai bambancin girma. Idan ka lura, za ka ga Naira 20 ta fi Naira 10 fadi kadan; sannan Naira 50 ta fi Naira 10 fadi sosai, amma kusan tsawonsu daya. Kuma idan ka lura, za ka ga Naira 100 ta fi Naira 50 da Naira biyar da Naira goma da Naira 20 fadi da tsawo. Sannan Naira 200 ta fi Naira 100 fadi kadan, kuma ta fi ta kauri. Naira 500 kuma ta fi su fadi da kauri kadan. Naira dubu kuwa ta fi su fadi da tsawo kadan, amma bambancinta da Naira 500 shi ne fadi da tsawo. Ni nake iya kirga kudina kuma har wasu makafin ma ni nake kirga musu kudi.
Kakan iya tantance takarda da takardar kudi?
Babu shakka. Da ka ba ni takarda da na taba ta na san ba takardar kudi ba ce. Bambanci shi ne mafi yawan kudinmu na yanzu leda ne saboda haka idan ka cukwikuye kudi, nan da nan zai tashi, amma ita takarda kana cukwikuye ta ba za ta tashi ba.  Ka ga kamar takardar jarida da ba kauri gare ta ba, kana cukwikuye ta shi ke nan ta tashi daga aiki.
Kakan iya tantance kudin karfe?
Su ma tun da can da ake amfani da su nakan iya tantance su da na taba su. Ka ga kamar kwabo, bambancinsa da sule shi ne girma. Kwabo ya fi sisi girma da fadi da kauri kuma ya fi sule fadi da kauri, amma sisi da sule sun fi kwabo santsi.
Kudin kasashen waje fa za ka iya tantance su?
Gaskiya ba zan iya tantance su ba domin ban san su ba, ban taba taba su ba, ban san yanayin su ba. Kudin Najeriya kawai na iya tantancewa saboda mu’amalar da nake yi da su yau da gobe. Amma su ma kudin kasashen wajen da zan rika taba su yau da gobe zan iya gane bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar fadi ko kauri ko santsi ko tsawo.
Me ye ya kawo ka Jihar Legas?
Na zo neman kudi ne domin na samu dan abin da zan rufa wa kaina asiri. Ni kaina dole ce ta sa na zo Legas domin ai Hausawa na cewa da arziki a garin wasu gara a garinku. Saboda haka ina fatan komawa gida duk lokacin da Allah Ya nufa.