✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Mainin da Kiripto suka dauki hankalin matasa

Kada wannan harka ta bayyana haramun ce, amma ka ki bari don kwadayin duniya.

A yanzu babbar maganar da ta fi tashe a tsakanin matasa ita ce Mainin ko Kiripto.

Duk da cewa ba daya ba ne, amma suna da alaka da juna; inda Kiripto (Cryptocurrency) ke nufin asalin harkar, ita kuma Mainin (mining) ke nufin hako wasu sulalla (coins), wadanda idan aka kammala hakowa, za a iya amincewa da su, sai su zama cikin sulallan da ake hada-hada da su a Kasuwar Kiripto.

A farkon watan nan ne sulallan Notcoin suka fashe, inda matasa da dama suna samu dalolin Amurka, wanda hakan ya jawo hankalin matasan da ba sa yin harkar suka tsunduma.

Matasa da dama sun rika nuna shaidar kudin da suka samu daga Notcoin domin nuna wa wadanda suke musu dariya cewa wahalar banza suke yi.

Kuma kasancewar sun samu kudi sosai, sai wadanda suke shakkun lamarin, suka fara amincewa tare da shiga a dama da su.

Da yawansu sun yi mamakin cewa yaya za a yi mutum ya rika danna waya kawai, kuma ya samu kudi?

Idan aka kammala Mainin, ana tura wa mutum sulallansa cikin abin da ake kira edchanger, irin su Binance, wanda yanzu suka sa zare da Gwamnatin Tarayya da OKX da Bybit da sauransu.

Exchangers din (dillallai) kowane akwai farashin da yake ba sulallan. Misali a Notcoin, OKX ya fara da $0.0078.

A bayan ma Ice ya fashe, inda matasa suka samu kudade da dama.

Akwai abin da ake kira ‘holding’ wato ajiye kwandalar da mutum ya hako har zuwa lokacin da ake tunanin za ta kara tsada.

Sauran kwandalolin da suka fashe a baya

Bayan Notcoin da Ice da suka fashe, akwai kuma Remitano da Core da Smarrt Layer da Omega Network da Nyan da Pepe da sauransu da suka fashe a baya.

Sai kuma Pi da yawanci shi ne ya fi tashe a Arewa, amma har yanzu bai fashe ba, amma ana bumburutunsa a kan kusan Naira 500 duk guda daya.

Wadanda ake sa ran fashewarsu a gaba

Akwai kuma wasu da ake yi da ake sa ran za su fashe nan da lokaci kadan kamar su Tapswap, wanda shi ne matasa suka fi karba, da Over Wallat da Time Coin da WOW da OFC da Coin Sabi da Sidra da Yes coin da sauransu.

Ribar Mainin

Da yake bayani a kan ribar harkar, Sanusi Danjuma Ali ya rubuta cewa, “Ribar Mainin nakan waya yana rabuwa ne zuwa Crypto Projects, Miners, Investors (BCs) da kasuwannin Kiripto.

“Crypto projects suna samun tarin mutane da suke mainin dinsu (community) hakan kan jawo musu masu zuba jari da za su zuba manyan kudade a kan harkarsu.

“Sannan yawan community na sa kasuwannin crypto suna neman harkar su sa a kasuwarsu, sabanin a ce ba su da yawan mutane, inda za su sha wahala kafin su samu kasuwannin da za ta dora su.

“Haka zalika, yawan masu mainin yana sa kamfani ya samu karbuwa har hakan ya jawo hankalin masu hada-hada domin shiga kasuwa su saye shi.

“Masu mainin suna samun kudade na ladan aikin da suka yi. Aikin masu mainin ya kasu kashi biyu.

“Na farko shi ne mainin, na biyu shi ne su gayyato mutane,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Akwai Venture Capitalists (BCs) ko a ce masu zuba hannun jari a ayyukan da suke da masu mainin da yawa sukewato babbar community.

“BCs suna sayen kwandala tun kafin a fara amfani da ita. Sannan ribar exchanges shi ne na farko samun sabbin masu amfani da shi.

“Dole mutane su shiga kasuwar wato dillalai da za su tura kwadalolin. Sannan suna samun kaso idan an yi hada-hadar kwandalar.

“Misali, idan za mu sayar da kwandala da darajarta ta kai Dala 100, dillalai (exchangers) za su karbi Dala 1 ko 2 daga wajenmu.

“Yaya kuke gani idan kasuwa daya za ta samu idan miliyoyin masu mainin za su sayar da kwandalasru a kanta?

“Da aka yi Notcoin, mutane sama da miliyan 35 ne suka yi mainin na Notcoin, amma a karshe mutum miliyan 13 aka tura wa Notcoin dinsu.

“Wadannan mutane miliyan 13 an ba su damar su tura Notcoins dinsu zuwa Binance, OKX, Bybit da telegram wallet.

“Misali, a ce mutum miliyan 3 daga ciki sun tura OKX, kuma a ce kowane mutum ya samu Notcoin na Dala 100, yayin sayar da Notcoin dinsu, OKX zai samu akalla 1 daga kowannensu.

“Ke nan OKX ya samu Dala miliyan 3,” in ji shi.

Muhawara da sabani game da harkar

Harkar Kirifto da Mainin na ta samun karbuwa a tsakanin matasa, sai dai a gefe guda wasu na suka tare da caccakar lamarin.

Wasu na cewa cima-zaune ne suke yi, wasu kuma na cewa ba haka ba ne, wanda hakan kan sa idan ta fashe wasu suke nuna kudin da suka samu.

Fitaccen dan Kirifto a Arewa, da ke gaba-gaba a harkar, Sanusi Danjuma Ali ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Shawarata ga ’yan Kirifto da masu Mainin idan mun samu kudi, mu tabbata mun yi amfani da su wajen inganta sana’o’inmu na zahiri da muke yi.

“Mu kara zamanantar da kasuwancinmu na zahiri, mu kara jari, sannan mu fadada su ta hanyar bude rassa idan kudin za su isa mu yi hakan.

Misali, idan kai tela ne mai keken dinki daya a shagon gidanku da ke lungu, yi kokari ka kama shago a bakin hanya, ka karo kekunan dinki da na aiki (kamar Phoniex), ka zamantar da shagonka, sannan ka dauki yara kwararru da za su taya ka aiki.

“Ba lallai sai ka yi hakan lokaci guda ba, za ka iya farawa da kadan-kadan, ko da farawa da sayen kekunan dinkin ne kana ajiyewa.

“Mafiya yawanmu muna da sana’o’inmu na zahiri, amma ga wadanda ba su da su, su yi kokarin bude kasuwanci na zahiri.

“Mun sani Kirifto na da lokuta guda biyu, akwai bear season lokacin tafiyar hawainiya) da bull season (lokacin da harkokin ke kankama).

“Yin wasu sana’o’i za su taimaka maka lokacin bear season, kuma ko ba haka ba, akwai ganganci dogara da kasuwanci guda daya.

“Rarraba kafa na da matukar muhimmanci sosai a wannan rayuwa ta Nijeriya.”

Ba banza muke ci ba -Masu Mainin

Wani matashi mai suna Muhammad Ashir Muhammad ya ce ya samu alheri sosai a harkar, wanda a cewarsa ta taimaka masa.

“Maganar cewa cima-zaune ne, ba haka ba ne, ina da digiri, sannan inda da aiki. Kawai ina hadawa ne da wannan.

“A ICE na samu Dala 84 da yake asusu biyu nake yi, da wayata da wayar matata. Sannan a Notcoin na samu sama da Dala 100.

“Sannan na samu wasu coin din sama da biyar a baya. Aiki ne da yake bukatar lokaci da kwarewa.

“Musamman idan aka ce Air drop ne, wadanda su yawanci aiki suke sa mutum. Wannan na latsa wayar shi ne ake ganin kamar ya fi sauki, amma akwai masu wahala.

“Misali a ICE, ai har wata jarrabawa aka yi, wadanda suka fadi aka kona musu suka yi asarar kudin da ya kamata su samu.

“Sannan akwai over wallet da Marina protocol wadanda kullum sai ka amsa tambaya. Don haka akwai bukatar ilimi da kwarewa da lokaci.

“Don haka ban ga dalilin da za a cewa wai banza muke ci ba,” in ji shi.

Wani matashin mai suna Najib Salisu, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa “Kuna cewa mutane ana ba ku kudi ne a kyauta ba tare da wahala ba… motsi kadan ku sa hoton wasu daloli ko rasit na kudi.”

Matashin ya ce lamarin ba haka yake ba, saboda sai bayan ya shiga ya gane cewa wadannan kamfanonin biyan mutane ladan wahalarsu suke yi ta hanyar ba su coins din da suka yi kokari suka gina masu ta hanyar mainin.

“Waɗannan mamallakan mainin (coins) ɗin ba kuɗi suke bayarwa ba, coin za su ba ka lada wahalar da ka musu ta gina musu jama’a (community) har coin ɗinsu ya samu shiga kasuwa,” in ji shi.

Ya kara da cewa “Idan suka ba ka coin ka sayar ko ka riƙe kayanka.”

Lamarin nan na Kirifto bai tsaya a kan musayar yawu a tsakanin matasa ba, har malamai suna tofa albarkacin bakinsu.

Da yake jawabi a kan harkar Dokat Aliyu Muhammad Sani Misau a wani rubutunsa a Facebook mai taken matsayin malamai a cikin harkar Kirifto, cewa ya yi, “Su malamai rahama ne ga mutane, kuma fitilu ne da haske a cikin al’umma.

“Saboda asali malamai magada Annabi (SAW) ne. Shi kuma rahama ne ga talikai, shiriya ne ga mutane.

“Don haka kada ka yi zaton don kana wata harka ta samun kudi, idan malamai suka hana ka, suka ce haramun ne, ka yi zaton hasada suke yi maka, a’a, alheri suke so maka.

“Don so suke yi ka tsayu a kan shari’ar Allah, don ka rabauta a duniya da Lahira, ka tsira daga fushin Allah da azabarSa.

“Ita shari’ar Allah dalilanta suna da yawa. Saboda ayoyi da hadisai suna nuni zuwa ga hukunci ta fuskoki masu yawa, ta nassin aya da Hadisi, ta zahiri, “umumi” da “khususi”, da makamantansu). Kuma dalilan ba su takaita a kan Alkur’ani da Hadisi ba, sun hada da Ijma’i da Kiyasi da maganar sahabi, da sauran hujjoji a shari’a, ciki har da manufofin shari’a da ka’idojinta.

“Daga cikin manyan manufofin shari’a akwai samar da gamammiyar maslahar a’lumma da kawar da barna.

“Da kare dukiya da kawar da barna a dukiyar al’umma don wanzuwar bunkasar tattalin arzikin al’umma da kawar da cutarwa ga bayi.

“Saboda haka shi mumini, duk lokacin da aka ce masa shari’a ta yi hukunci kaza, a kan aiki kaza… ko harka kaza… ko abu kaza… to zai mika wuya ne, saboda rayuwarsa gaba daya neman yardar Allah ce.

“Saboda haka abin da ya shafi harkar “digital currency” (Kirifto) gaba daya, harka ce wacce har zuwa yanzu akwai sabani mai girma a tsakanin malamai wajen halaccinta.

“Don haka ya kai dan uwa! Ka zama cikin shiri, duk lokacin da hukuncin wannan harka ta “Kirifto” da “Mainin” ya bayyana maka to ka ji tsoron Allah ka bi fatawar da ta fi karfin hujja, wacce ta fi dacewa da manufofin shari’a da ka’idojinta.

“Ya kai dan uwa! Kada wannan harka ta bayyana haramun ce, amma ka ki bari don kwadayin duniya. Ka sani lallai duniya jin dadi ne dan kadan, asalin rayuwa tana Lahira.

“In kuma ta bayyana halal ce, to sai ka ci gaba da abinka, cikin kwanciyar hankali. Abin nufi shi ne; mu ji tsoron Allah, mu nisanci son zuciya da munana zato ga malamai magada annabawa, masu yi mana fatawa a harkokin rayuwarmu, don ta dace da shari’ar Allah.”

Daga cikin malaman da suka kushe harkar akwai Sheikh Dokta Bn Uthman, wanda Aminiya ta ga wani bidiyonsa yana kushe lamarin, duk da ba ta gano yaushe ya yi bidiyon ba.

A bangaren wadanda suka ganin babu laifi kuma akwai Dokta Bashir Aliyu Umar da Farfesa Mansur Yelwa da wasunsu.