A rana guda ’yan Yahoo 792 ’yan kasashn waje da ’yan Nijeriya suka shiga hannun hukuma kan laifin damfarar mutane ta intanet da sunan soyayya ko harkar Kirifto da sauransu a Jihar Legas.
Hukumar Yaki daMasuKarya Tattalin Arziki (EFCC) ta kama mutanen, wadand suka hada da ’yan kasashen waje 193 da kuma ’yan Nijeriya 599.
Wannan shi n kamen mutane mafi yawa da EFCC ta taba yi a tariri, bayan wani gagarumin samame da ta gudanar a Jihar Legas a ranar 10 ga watan nan na Disamba.
Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren ya ce ’yan kasashen wajen da aka kama ’yan kungiyar damfara ta intanet ne da kuma harkar damfarar Kirifto, da ke da maboya a wani gini mai hawa bakwai wanda ake kira Big Leaf Building a Legas.
Uwujaren ya shaida wa ’yan jarida a ranar Litinin cewa ’yan kasashen wajen da aka kama sun had da ’yan China 114 da ’yan kasar Filifins 40 da ’yan Kazakhstan biyu da dan Pakistan daya da kuma dan Indonesiya daya.
Ya ce suna amfani da ginin nasu a matsayin cibiyar horas da abokan cin mushensu ’yan Najeriya kan dabarun damfarar mutane ta hanyar soyayya ta intanet a kasasehn Amurka da ’yan kasashen Kanada da Meziko da sauransu.
Ta wanann hanya ce ’yan kasar wajen da aka kama suke tattarawa tare da amfani da abokan cin mushen nasu ’yan Nijeriya a matsayin yaransu, wajen damfarar wasu ta intanet.
Abubuwan da aka kwace a hannunsu sun hada da kwamfutoci na kan tebur da Laptop da wayoyi da layukan sadarwa da kuma motoci.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.