Hukumar gudanarwar Asibitin Tarayya da ke Jihar Gombe (FTH) ta haramta wa ma’aikatanta yin ‘kirifto’ ko ‘mining’ a lokacin da suke bakin aiki.
Hukumar ta ce ta lura harkar ‘mining’ din tana dauke hankalin ma’aikata daga kula da marasa lafiya a lokutan da suke bakin aiki.
Wata sanarwa da ta da aike wa ma’aikatan asibitin ta ce suna da damar yin harkokinsu na yau da kullum a lokacin da ba su bakin aiki.
- Rundunar sojin Nijar ta tabbatar da mutuwar jami’anta 12 da ƴan ta’adda suka yi
- Jerin tallafin ambaliya da ya shiga hannun Gwamnatin Borno
Kamar yadda Adamu Usman Tela, Mataimakin Daraktan Gudanarwa na asibitin ya tabbatar wa Trust Radio, ya ce sun lura da hakan ne tun da wuri suka dauki matakin gaggawa kafin a kawo musu korafi.
“Mun dauki wannan mataki ne tun kafin a fara samun salwantar rayuwa, domin kula da lafiyar al’umma shi ne abu na farko”
Harkar ‘mining’ a ’yan tsakankanin nan dai ta zama ruwan dare tsakanin al’umma maza da mata, ciki har da ma’aikata masu daukar albashi.