✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Mai Siket ‘ya yi wa tsohuwa fyade’

Shekara guda ke nan al’ummar garin Kwanar Dangora da ke jihar Kano na zargin wani wanda ba a san ko wane ne ba da kutsawa…

Shekara guda ke nan al’ummar garin Kwanar Dangora da ke jihar Kano na zargin wani wanda ba a san ko wane ne ba da kutsawa cikin gidaje yana yi wa mata fyade.

Mai fyaden dai bai bar matan aure ba, balle ‘yan mata, haka nan bai bar kananan yara ba, balle tsofaffi.

Wannan lamari ya jefa tsoro a zukatan mutanen garin, saboda zaton cewa wanda ake zargin aljani ne.

“Kamar shekara guda [ke nan] mutanen gari [suka] farga da wannan mutum”, inji sakataren ‘yan sintiri na mazabar Yalwa Sani Sama’ila, wanda aka fi sani da Sani Jos.

Ya kara da cewa, “Yakan yi amfani da gwiwar hannunsa ya danne [wa mace] kirji; da ta yi yunkurin za ta yi ihu sai ya sa hannaunsa ya rike mata makogwaro.

“Tun tana mutsumutsu har sai ta galabaita, ta saduda, ta hakura, sannan ya samu wannan dama, ya [yi abin da zai yi] ya tafi.

“Saboda ba wanda ya taba ganin yanayin da yake, sai dai matan su ce wani mutum ne ya zo musu tsirara, suka sanya mishi suna ‘Mai Siket’ – duk ya tashi hankalin matan Kwanar Dangora”.

Sai dai kuma a makon jiya ‘yan sinitirin garin suka kama wani matashi tsirara haihuwar uwarsa, kuma suka yi amanna shi ne yake wa matan yankin fyade.

Yadda dubunsa ta cika

Dubun ‘Mai Siket’ ta cika ne lokacin da ya yi yunkurin shiga wani gida da tsakar dare bayan kafa ta dauke amma mai gidan ya gan shi ya kuma fafare shi.

Daga nan ‘yan sintirin suka yi masa kofar rago suka kama shi a tsirararsa suka daure shi a turke har gari ya waye jama’a suka taru.

Da yake amsa tambayoyinsu, ‘Mai Siket’ ya tabbatar wa ‘yan sintirin cewa shekararsa daya yana yi wa mata fyade a garin.

Ya yi fyade wa akalla mace 40 ciki har da tsohuwa mai shekaru 95 wadda kuma ya yi wa sata bayan fyaden.

Zuwa yanzu dai tsohuwar ce kawai ta amince cewa ya yi mata fyade; sauran matan 39 shi da kansa ya lissafa wa ‘yan sintiri gidajen da ya shiga ya kuma aikata aika-aikar.

Ya kuma shaida musu cewa ya zo garin ne domin kasuwanci da malanta daga garin Kankiya na jihar Katsina.

Barazana ga matan gari

Da yake karin haske a kan kamen, Sani Jos ya shaida wa Aminiya cewa ‘kwarton’ ya kan tube ne kafin ya tafi inda duk ya yi niyya.

“Ya kan tube ne tsirara, duk unguwar da ya tafi, sai ya tafi karshen gari ya nemi kango ya kwabe rigarsa da wandonsa da takalminsa ya boye, sannan ya shiga gari duk gidan da ya samu sai ya fada”, inji Sani Jos.

Sakataren ‘yan sintirin ya kuma ce sun kama ‘Mai Siket’ ne bayan da suka yi masa kofar-rago.

“Ranar Alhamis din nan da ta wuce, muna sintiri a gari sai muka ji an yi ihu ta wani bangare; sai muka kai dauki a guje —za mu kai kamar mu shida haka.

“Sai muka tarar da shi tsirara haihuwar uwarshi an biyo shi ya fito daga Gidan Kwano, sai muka rutsa shi – duk inda ya duba zai ga mutanenmu a wurin”, inji Sani Jos.

Ya kuma ce a wurin suka daure ‘Mai Siket’ har gari ya waye suka kai shi wajen sarkin garin, sannan suka mika shi ga ‘yan sanda.

‘Jama’a su kara sa ido’

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Mai Anguwar Rimi Alhaji Ahmadu Ya’u ya ce makwabciyarsa ce ‘yar shekara 95 din da katon ya yi wa fyade.

Mai garin ya yi godiya ga Allah bisa nasarar kama kwarton sannan ya bukaci jama’arsa da su ci gaba da sa ido don kawar da bata-gari a cikin al’ummar.

Zuwa yanzu ‘yan sintiri sun damka ‘Mai Siket’ a hannun Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, domin kammala bincike da gurfanarwa a gaban kotu.

Rundunar ‘Yan Sandan ta tabbatar cewa ‘yan sintirin sun mika mata matashin da aka kama a Kwanar Dangora kuma tana gudanar da bincike.