✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mai juna biyu ta shirya garkuwa da kanta a Yobe

Ana dai zargin matar ne da hada baki da wasu matasa don shirya garkuwar.

A Jihar Yobe, dubun wata mata mai juna biyu da ake zargi da hada baki da wasu matasa guda biyu don shirya garkuwa da kanta, ta cika.

An dai ba da rahoton batan matar, mai suna Nafisa Saleh, ranar Juma’a, lokacin da take kan hanyarta ta zuwa awo a Asibitin Kwararru da ke Damaturu.

Jim kadan da faruwar hakan ne kuma matasan suka kira mijin nata don neman kudin fansarta.

Sai dai daga bisani binciken ’yan sanda ya gano da cewa matar ce ta hada baki da matasan domin su karbi kudi daga wurin mijinta da kuma ’yan uwanta kamar yadd Kakakin a ’yan sandan Jihar, ASP Dungus Abdulkarim  ya tabbatar a ranar Talata.

Ya ce da jin haka ba su yi wata-wata ba suka shiga farautar mutanen, har suka sami nasarar kama mutum biyun da ake zargi: Goni Modu da kuma Umar Mai Gudusu, dukkansu mazauna kauyen Dadinge da ke Karamar Hukumar Gujba a Jihar.

Kakakin ya ce tuni aka garzaya da Nafisa zuwa asibiti, bayan ta yi korafin rashin lafiya domin  duba ta.