Shekaru 29 da suka gabata, Auwalu Hussaini, mai shekara 44 a yanzu, ya tsinci kansa cikin yanayin rayuwa da ya tilasta masa zabar sana’a kan karatun boko.
Hussaini, wanda aka fi sani da suna ‘Manaja’ ya shiga sana’ar a matsayin dan-aike (masinja) amma da tafiya ta nutsa, saboda kwazon da Allah Ya ba shi, ya zama Mataimakin Manajan gidan burodin.
Daga nan, sunan “Manaja” ya yi ta bin sa har ya ginu ya kuma gina rassan gidan burodi 10 da ya dauki ma’aikata fiye da 1,000 da dubban mutane ke ci a karkashinsu.
Manaja ya ce, abun da ya fi burge shi shi ne yawan ma’aikatan da ya sama wa aiki da jama’ar da Allah Ya yi masa, wanda kusan bashi da na biyu a fadin masarautar Gumel.
– ‘Na ajiye karatun boko na rungumi sana’ar burodi’
Hussaini, wanda aka haifa a 1976, ya fara karatun boko, amma bai yi nisa ba ya jingine, saboda tunanin da ya ginu a kai na cewar neman ilimin burodi zai fi yi masa riba.
“A lokacin Shugaban Kasa Sani Abacha ne, al’amura suka cukume, sai na yi watsi da karatun boko na dawo gida.
“Bayan na dawo ne na fara aiki da gidan burodin Alhaji Nuhu Karami a nan Gumel domin samun abun da zan ci.
“Wani lokacin ba a biyan mu kudi sai dai idan mun gama aiki sai a ba mu konannen burodi mu ci”, inji Hussani.
Da tafiya ta yi tafiya, sai manajan gidan burodin ya lura da kwazon Hussaini, sai ya mayar da shi mataimakinsa.
Haka aka cigaba da tafiya har ya zama manaja bayan maigidansa ya yi murabus.
Hussaini ya ce, zaman sa Manaja ya ba shi damar sani da kwarewa a harkar tafiyar da gidan burodi. Sai dai kash! Ba shi da kudin da zai gina na shi gidan burodin.
Ya ce, bayan dan lokaci sai kawunsa, mai sana’ar gidan burodi, ya ba shi aiki, wanda a nan ne ya samu damar mallakar fili a bayan tashar mota taGumel.
Daga bisani ya gina nashi gidan burodin da ya sanya wa suna ‘Lautai Bakery’.
Manaja ya ce, a halin yanzu yana da gidajen burodi 10 a tsakanin garin Gumel da Dutse, baban birnin jihar Jigawa.
Takwas a Gumel sai biyu a Dutse kuma akalla mutane 100 na aiki a kowane gidan burodi.
“Abun da nake yi, idan muka koya wa mutum sana’ar, kuma muka gamsu da kwarewarsa sai mu bude masa gidan burodi da zai kula mana da shi.
“Hakan kuma yana ba mu damar daukar wasu matasan su yi aiki a karkashinsa. Ta haka muke kara fadada kasuwarmu mu kuma sama wa mutane ayyukan yi”, inji Manaja.
– Yawan mutanen da ke aiki karkashina na sani farin ciki
“Ba karamin abun farin ciki ne ba ya zamto mutane na ci a karkashinka, wannan yana matukar sa ni farin ciki a duk lokacin da na tuna”, inji Manaja a ce cikin fara’a.
Ya ce hakan ya sa ya yi farin jini da suna a duk inda ya sa kafa cikin Masarautar Gumel. “Ana girmama ni, kuma babu abinda ya ke bani annashuwa kamar hakan.
“Ina matukar jin dadin yadda mutane suke haba-haba da ni. Ban tsammanin akwai wanda ake yi wa irin karramawar da ake yi mini.
“Zai yi wahala ka shiga gida ba ka samu wani da muka ba aiki ba ko yana ci karkashin wanda muka ba aiki ba.
“Abun da ya fi faranta mini rai shi ne, yawan mutanen da na sama wa abun yi da abinci. Kuma a duk lokacin da raina ya baci, da na tuna da hakan sai bakin cikin ya wanye”, inji manaja.
Ya kuma ce wani lokaci mataimakinsa kan yi masa laifin da ya kamata ya kulle gidan biredin, amma da ya kalli mutanen da ke rayuwa karkashinsa sai ya kasa, “Sai na yi hakuri na ba abun da ya faru baya”.
— Yadda Manaja ya sauya rayuwar ma’aikatansa
Daya daga cikin manajojin gidan biredin Manaja da ke kula da gidajen burodi biyu ya ce a rana sukan murza burodi na buhun fulawa 65.
“Na karu da dama a harkar gidan burodinsa, na auri mata biyu, na gina gidana, da motocin hawa guda biyu. Na je hajji, na kai iyayena, kuma in Allah Ya yarda zan kai yayata duk lokacin da aka bude tafiya Saudiyya. Saboda haka babu abun da zan yi sai godiya ga Allah da kuma ubangidana”.
Shi kuwa Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Danladi Ciyaman, cewa ya yi shekaru 16 ya kwashe yana aiki a karkashin Manaja.
“Alhamdulillah, a lokacin da na fara aiki a gidan burodin ba ni da komai, amma da wannan kasuwancin babu abun da ban mallaka ba. Na gina gida, na sayi mortar hawa, na kuma kula da iyalina”
Ya ce kuma Allah kadai zai iya biyan Manaja abun da ya yi masa sannan ya yi kira ga masu arziki da su yi koyi da ubangidansa ta hanyar gidana masana’antu da za su sama wa mutane ayyukan yi da rage munanan dabi’u a cikin al’umma.
Wasu mazauna garin Gumel sun ce Manaja mutum ne mai taimakon al’umma da ya fitar da mutane da dama daga kangin talauci.
— Manaja ya samar wa mutane ayyuka a wasu sana’oin
Ba a sayar da burodi ya tsaya ba, ya ci gaba da taba rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban.
Ya kuma ce saboda yanayin kasuwar da yake cikin ba zai iya fadin yawan dukiyarsa a kudi ko kaddara ba.
“A misali, watan da ya wuce na gina gidan biredi a Dutse. Na kashe fiye da miliyan 15 wajen gina shi. Don haka ba zan iya fadin adadin kudin da ke yawo cikin kasuwancin ba. Lokacin zakka kadai nake zaunawa na yi lissafin kudaden fitar.
Ya ce kuma ya shiga wadansu hakokin kasuwanci da suka hada da kamfanin ruwan leda (Lautai Table Water)
“Muna kuma da shagon sayar da fulawa da sauran kayayyaki da gidajen burodi ke saye a hannunmu”, ya nuna shagon inda akalla matasa hamsin suke saukar da buhunan fulawa.
“Muna kuma sayar da wake da ridi da dusa da siminti da sauran kayan amfanin gida a cikin Najeriya da jamhuriyar Nijar. Mukan kuma fitar da garin sabula da taliya zuwa Nijar, saboda ba ta da nisa daga Gumel “.
— Dalilin shiga wasu kasuwanci
Ya ce babban dalilin da ya sa shi shiga wasu kasuwanci shi ne fahimtar irin ribar da abokan huldarsu suke samu a cikin kasuwar.
“Idan muna zaune kasuwar da masu yin hulda, muna fahimtar yadda suke hada-hadar. Misali, ina da abokai a Maigatari, kullum muna tare kuma ina ganin yadda suke sayen kayan suna fita da su.
— Yawancin ma’aikatana masu digiri da NCE ne
Manaja ya ce yana biyan ma’aikatansa a kullum bayan an gama aiki ne, kuma da yawa daga cikinsu masu shaidar kammala Digiri da NCE ne, amma saboda kyawon albashin da yake biyan su ba sa karbar aikin gwamnati, sai dai aiki mai tsoka.
“Da yawa daga cikin wadannan matasan suna da aure. Wasu kuma ba su da aure amma ba su matsasa wa iyayensu da bani-bani ko kuma shiga wata mummunar dabi’a, mun dauke su aiki kuma suna jin dadin abun da muke biyan su”.
A matsayinsa na wanda ya samar wa matasa fiye da 1,000 ayyukan da ko wata karamar hukumar albarka, ya ce, “Ban taba neman taimako ko karbar taimako daga gwamnati ba”.
Sai dai kuma kamar yadda annobar COVID-19 ta shafi kowane kasuwanci, harkokin Manaja sun tabu, musamman harkarshi ta kai kaya jamhuriyar Nijar.
“Kafin bude garin da aka yi, muna kai akalla kwali 1,000 na taliya da buhu 500 na hatsi da sauransu zuwa Maigatari, mu biya haraji sannan mu ketara da kayan zuwa Nijar. Da aka kulle gari duk sai da harkokin mu suka tsaya cik”, inji shi.
Manaja, wanda ya haifi ‘ya’ya tara ya ba matasa shawarar “Kar don ka gama karatu ka rika zaman kashe wando kana jiran gwamnati ta ba ka aiki. Ko kuma Allah Ya kare, mutum ya jira mahaifansa su mutu ya gaji dukiyarsu.
“Ya kamata matasa su rika sama wa kansu abun yi, kuma kar a rika raina sana’a komai kankantarta”.