’Yan bindiga sun kashe mutum 17 a kauyen Rimi da ke kusa da yankin da sabuwar Rijiyar Mai ta Kolmani da Shugaban Bauhari ya kaddamar take a Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.
Shugaban Kungiyar Matasan Najeriya (NYC) Reshen Alkaleri, Kwamared Bala Mohammed Duguri, ya shaida mana cewa mahara kusan 300 ne a kan babura suka kai harin suka hallaka mutum 14 a kauyen da ke cikin Gandun Dajin Yankari.
- Zan mayar da Najeriya tamkar Maroko a harkar kwallon kafa —Atiku
- Ku yi hattara da romon bakan Atiku —Tinubu ga ’yan Najeriya
Ya ce, “Da misalin karfe 3 ne, bayan Sallar Juma’a, suka zagaye kauyen Rimi, kusan su 300 a kan babura, nan take suka kashe mutum 14 suka kuma kona gidaje 70; Sun kone mota kirar Hilux da tarakta sannan sun yi awon gaba da dabobbi masu yawan gaske a yayin harin.
“Jiya (Asabar) mun raka Hakimin Duguri zuwa kauyen Rimi, inda muka jajanta musu, muka karbi ’yan gudun hijira daga kauyen, muka raba musu kayan tallafi,” a cewar Kwamred Bala.
Wani mazaunin kauyen Yashi, Babawo Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun yi wa mutane kawanya ne, suka bude musu wuta ne bayan idar da Sallar Juma’a
Babawo, ya ce sojojiin da aka ajiye a kauyen Duguri sun kai dauki Rimi, inda suka bi sahun maharan suka kashe da dama daga cikinsu a ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa dubban mutane sun fara hijira daga gidajensu bayan yawaitar munanan hare-haren ’yan bindiga a kauyukan karamar hukumar.
Wasu bayanai sun nun bayyana cewa yawaitar ayyukan hakar ma’adanai da kuma Gandun Dajin Yankari da ke yankin na daga abubuwan da maharan ke amfani da su wajen buya, tare da sace mutane domin karbar kudin fansa.
Sai dai Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, ta karyata kai harin tare da kashe mutane a Alkaleri.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya ce babu wani hari da akai yankin da aka gano danyen man fetur din.
“Rundunarmu ta lura da wani labari da aka wallafa a ranar 11 ga watan Disamba, 2022 cewar ’yan bindiga sun kashe mutum 10 a sabon wurin da aka gano man fetur. Wannan labari baki dayansa ba gaskiya ba ne,” a cewar Wakil.
’Yan bindiga sun kashe ’yan kasuwa 4 a Katsina
A wani harin kuwa, akalla ‘yan kasuwa hudu ne ‘yan bindiga suka hallaka har lahira a kauyen Zandam da ke Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina.
Shugaban Karamar Hukumar Jibiya, Bashir Sabiu Maitan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi.
Shugaban, ya ce maharan sun kashe ’yan kasuwar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwar mako-mako da ke ci ranar Lahadi a Jibiya.
Wata majiya a kauyen Zandam, da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa harin daukar fansa ne saboda, “Jiya (Asabar) wasu ’yan banga sun kashe wani Bafulatani, shi ne yau maharan suka kawo hari suka kashe mutum hudu a hanyar Kasuwar Jibiya.
“Mutum biyar suka harba, amma take hudu suka mutu, na biyar din, Malam Ibrahim Julius, yana asibiti yana jinya.”
Ko da aka tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wanda ya ji raunin yana kwance a Babban Asibitin Katsina.
Karamar Hukumar Jibiya na daga cikin yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar a baya-bayan nan ta bayar da umarnin rufe titin da ya tashi da Jibiya zuwa Zurmi a Jihar Zamfara.