Dubun wasu mutum uku da ake zargi da garkuwa da mutane a yankin Ossra-Irekpeni da ke kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja a Jihar Kogi ta cika, bayan da aka cafke su a maboyarsu.
Daya daga cikin mafarautan yankin, wanda su ne suka sami nasarar kama masu garkuwar, ya ce sai da aka samu musayar wuta tsakaninsu da masu garkuwar kafin su shiga hannu.
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake a Imo
- Sabuwar doka ta ba ’yan New Zealand damar sauya jinsinsu na haihuwa
Ya ce mafarautan, tare da hadin gwiwar Shugaban Karamar Hukumar Adavi ta Jihar Kogin, Samuel Omuya, su ne suka yi wa dajin kawanya da yammacin ranar Laraba, bayan samun wasu rahotannin sirri kan maboyar bata-garin.
A cewarsa, hakan ne ya sa ’yan bindigar suka bude musu, wuta, inda su kuma suka mayar da harbi.
“Nan take muka fara musayar wuta da su, har muka samu nasarar kama uku daga cikinsu,” inji shi.
Ya kuma ce wasu daga cikin masu garkuwar sun tsere da harbi a jikinsu, yayin da kuma aka damka wadanda aka kama din ga jami’an tsaro da ke Lokoja, babban birnin Jihar.
Shugaban Karamar Hukumar Adavi, ya tabbatar da akama mutanen, inda ya ce shi ne ya jagoranci aikin ka samamen.
Ya ce mutanen da aka kama din na cikin wadanda suka hana matafiya a kan hanyar Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja sakat.
Daga nan sai ya jinjina wa mafarautan kan kokarinsu wajen samun nasarar, tare da kiran sauran mazauna yankin da su ci gaba da lura da kuma kai wa jami’an tsaro muhimman bayanai.
Yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Ovye Aya, ya ci tura saboda bai daga kiran waya ba sannan bai amsa rubutaccen sakon da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.