✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Madrid ta kusa shekara biyu tana jan zarenta

A wannan kakar, Real Madrid din ta lashe kofuna uku.

Kwanaki 50 da suka gabata sun kasance masu armashi wa kulob din Real Madrid, inda ta lashe dukkanin wasanni taran da ta buga a jere inda hakan ya ba ta damar fara kakar 2022/23 da kafar dama.

Kodayake za a iya cewa kulob din mai mazauni a babban birnin Sifaniya ya kasance cikin wannan ganiyar na kimanin kwanaki cur a jere zuwa yanzu.

Kafa wannan dambar da Madrid ta yi ya faro ne tun gargarar kakar wasannin 2020/21, ke nan za a iya cewa a daukacin shekarar 2021 da ya dangana da farkon kakar wasannin ta bana da a yau za a shiga wasannin mako na bakwai a Laligar Sifaniyar.

Tun daga watan Fabrairun 2021, Real Madrid ta buga wasanni 89 a dukkanin gasannin Turai da take bugawa, inda ta yi nasara a wasanni 63, ta yi kunnen doki 16 yayin da aka doke ta a wasanni 10.

Ke nan alkaluman nan na nuna cewa kungiyar ta Los Blancos da ke nufin farare a harshen Sifaniyanci, ta lashe kashi 71 na ilahirin wasanni n da ta buga a wannan tsakanin.

Idan aka maida hankali kan wasannin gasar Laliga kadai, a nan alkaluman nasarorin da ta yi sun cira zuwa kashi 73, inda ta ci wasanni 45, da buga canjaras 13 sannan aka doke ta sau hudu kacal cikin wasanni fiye da 62 da ta buga.

Idan aka yi gwari-gwari, Real Madrid ta samu maki 148 cikin maki 186 da ya kamata samu kwata, wanda yake daidai da kashi 80 cikin 100 na daukacin makin na wadannan wasannin.

Sannan a daya gefen, idan aka kwatanta da wasanni 62 da kulob din Barcelona da Atletico Madrid suka buga a wannan tsakanin a gasar ta Laliga, Real din ta yi gaban babbar abokiyar burminta daga yankin Catalonia da maki 20 yayin da ts ma kerewa babbar abiyar hamayyarta a birnin Madrid da maki 31 cur.

Ita Barcelona ta iya samun kashi 69 ne kacal na makin da ya kamata ta samu a wadannan wasannin da ta kara, inda ita kuwa Atletico ta Atletico ta tsira da kashi 62 na wannan makin.

Sai dai wani abin lura a nan shi ne shi ne mene ne dalilin da ake la’akari da wasannin da Real din buga tun daga Fabrairun 2021 kadai?

Eh, dalili shi ne wannan ne lokacin da ya zama Madrid din ta farfado daga kangin da ta tsinci kanta ciki lokacin da tsohon kocinta Zinedine Zidane ya kusan rasa aikinsa.

A Janairun 2021, an yi waje rod da Real Madrid daga gasar babban kofin Sifaniya Supercopa de Espana da kofin Copa del Rey sannan ta yi faduwar totuwa a gasar LaLiga lokacin da kulob din Lebante ta bi ta har gida ta yi mata dukan tsiya, lamarin da ya jefa Real din maki 10 a bayan Atletico Madrid.

Rashin nasara guda daya tilo a watanni hudun karshe na kakar 2020/21 Bayan da ta samu kanta cikin kakanikayi, Real Madrid din ta farfado daga bisani; inda watanni hudu na karshen kakar wasannin 2020/21 suka sanya ta zama tauraruwa.

Ta yi nasara kan kulob din Huesca a ranar 6 ga Fabrairun 2021, sannan ba a sake doke ta ba dukkanin wasannin LaLiga har sai a ranar 22 Mayun shekarar.

Lokacin ne kulob din ya samu nasara a wasanni 13 da canjaras biyar, wanda hakan ya ba ta damar hankoron lashe kofin gasar har zuwa ranar wasan karshe –lokacin da aka raba gardama.

Sannan ko gasar Zakarun Turai, Madrid din ta kai har matakin semifainal inda ta kafsa da Chelsea, wacce ita ce kadai ta doke Real din a wannan tsakanin.

Jimilla, Real ta yi nasara a wasanni 16 da canjaras bakwai yayin da aka doke ta sau daya kacal.

Wannan ya kasance sakamakon da Real ta samu a watanni hudun karshe na kakar 2020/21, wanda kyakkyawan sakamako ne ainun in ban da rashin cin kofi ko guda daya da ta yi a kakar.

Ba a taka mata birki a kakar da ta gabata Kulob din Real Madrid ta dora daga inda ta tsaya har zuwa kakar bara tare da kocinta Carlo Ancelotti.

Ta kasance kulob din da a Sifaniya ba ta tsara a gasar LaLigar kakar inda ta lashe kofin ana saura wasanni hudu gabanin kammala gasar a nasarorin wasanni 26 da kunnen doki takwas inda aka doke ta sau hudu kacal, tare da samun maki 86 (daidai da kashi 77) cikin maki 114 da ya kamata a samu a wasanni 38 na gasar, ana saura wasanni hudu a karkare gasar, Real din ta wanke allonta.

A wannan kakar, Real Madrid din ta lashe kofuna uku cikin hudun da ta shiga gasar lashe su inda ta kare kakar da cin wasanni 39, canjaras takwas yayin da aka doke ta wasanni tara cikin 56 da ta fafata.

Shiga kakar 2022/23 da kafar dama Ko a wannan kakar da muke ciki, kulob din ya ci gaba da jan zarensa yayin da yake taka wuta har kwano bisa yadda ya yi nasara a wasanni tara cur ba tare da barin maki ko guda ba.

Tuni Real Madrid ta lashe Babban Kofin Turai na UEFA Super Cup, sannan a halin yanzu it ace ke jan ragamar teburin gasar LaLiga har ma da teburin rukunin da take ciki a Gasar Zakarun Turai.

Bugu da kari, Madrid din ta yi nasara a wasan hamayya na birnin Madrid inda ta bi Atletico Madrid har gida ta doke ta a filin wasa na Cibitas Metropolitano.

Ko shakka babu, fara saka da zare mai kyau a kakar bana da Real Madrid din ta yi ya kara armashin ganiyar da take ciki na fiye da shekara daya da rabi.