✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mace ta saci yara ta tafi da su Legas suna bara

A Ranar idin sallah ƙaramar da ta gabata ne al’ummar garin Ogere da ke  Jihar Ogun suka wayi gari cikin zullumi bayan da wata mata…

A Ranar idin sallah ƙaramar da ta gabata ne al’ummar garin Ogere da ke  Jihar Ogun suka wayi gari cikin zullumi bayan da wata mata ta yi nasarar sace wasu yara ƙanana ta yi gaba da su.
Mahaifiyar yaran da aka sace mai suna Hauwa Muhammad ta shaida wa Aminiya cewa, bayan sun dawo daga sallar idin ƙaramar sallar da ta gabata ne, dama sun yi da ƙaninta zai ka ’ya’yan nata gidan  kakanninsu da ke Alaba a Legas “ashe ya zo gidan ranar sallah sai aka fada masa mun tafi sallar idi, ko da na dawo na kira shi ta waya, sai ya ce min ai ya tafi har ya kai Oshodi, jin haka ne yaran suka fara kuka sai na kai su, sai na ce musu su bari gobe don a yanzu ba ni da kuɗin mota. Jin haka sai matar mai suna Asama’u, wacce a kafi sani da Maman biyu ta ce in bata su daman za ta je Legas unguwar Idiyarba bayan sun  kwana ɗaya, sai ta kai su wajen kakanninsu, a haka na ba ta su,” inji ta.
Na tambaye ta ko tana da wata alaƙa da Maman biyun sai ta ce babu wata alaƙa a tsakanin su, hasali ma mijinta ne ya shiga wani ibtila’i bayan da ya kaɗe wasu mutane kasancewarsa direban babbar mota hakan ne yasa aka ɗaure shi. To ita maman biyun ta je ne ta yi mata jaje ne , “bayan da ta zo ta yi min Allah ya kyauta, sai ta zauna a gidana tana yi min ‘yan aikace-aikace ina biyan ta, inda nakan ba ta Naira 400 ko 500 a kullum. Mun yi wata huɗu da ita muna haka, yawancin mutane in na tambaye su sai su ce sun santa tana da ɗan uwa a Shagamu. Bayan da ta tafi da yaran ne da na je gidan mu a Legas sai ban ga yaran ba, tun daga nan in mun kira wayarta ba a samunta, daga nan ne na koma gida ko ta dawo da su, a nan ɗin ma  ba mu gansu ba. Hankalinmu ya tashi muka bazama nema.
“Sai da muka yi mako biyu muna nema har da duk abin hannuna ya ƙare” inji ta.
Sarkin Hausawa Ogere Alhji Abdullahi Saminaka ya shaida wa Aminiya cewa, sai bayan da lamarin ya faru da kimanin mako biyu ne labarin ya riske shi na ɓatan yaran. Ya ce a lokacin ne mahaifiyar tasu ta sanar da shi.
“Nan fa na ce mata to kin ga wannan abu in mun sanar da hukumar ’yan sanda ke za su fara kamawa, don haka na tara malamai aka yi ta addu’a na kuma yi shelar cigiyar yaran,  tare da bayyana kamanin su, bayan kwana ɗaya da haka sai ga wata mata ta zo ta shaida mana cewa ta gansu  a can wani ƙauyen mata dake yankin Ikorodu a Legas, wata mata na  yin bara da su. Daga nan na tura ma’aikatana na ce su taho da yaran da matar da ta tafi da su.   Saboda surƙuƙin wajen sai bayan sallar isha’i suka dawo da su, inda na basu Naira dubu takwas na sufuri”  inji shi.
Ya ce ganin yadda mutanen garin suka hassala ne ya sanya a ka kai matar wani waje a ka ɓoye ta, don gudun ka da jama’a su farmata su hallaka ta, kafin daga bisani ya  miƙata ga dan uwanta da ke garin Shagamu, wanda ya shaida wa masarautar cewa  rabonsa da ganin matar ya wuce shekaru 10.  
“Don haka na miƙata garesu na umarcesu da su gyara zumuncin da ke tsakaninsu,” inji shi.
Malam Kabiru Gambo ne  ya jagoranci aikin gano yaran da matar ta sace ta tafi bara da su. Ya shaida wa Aminiya cewa da suka isa ƙauyen da matar ta ɓoye yaran su riske su cikin mummunan yanayi na ƙazanta sanye da yagaggun tufafi, domin sababbin kayan sallar da aka sanya musu sai matar ta bai wa wata mai sayar da abinci jingina, a haka take ba su abinci su ci, kayan sawarsu na hannunta. Nan take muka yi musu wanka muka biya kuɗin abincin da matar ta karɓar musu, muka karɓi suturunsu, muka sanya musu sannan muka tawo da su. Ba mu bari ma mahaifiyarsu ta gano irin halin da muka gansu a ciki ba,” in ji shi.
Yaran da aka sace ’yan ƙanana ne ƙwarai, waɗanda suka haɗar da Amina mai shekaru 6 da Ruƙayya ‘yar shekara 7. Amina ta shaida wa Aminiya cewa, matar na sanya su bara ne inda ta ce su rinka cewa Allazi wahidun, suna bin mutane, domin su ba su kuɗi. Ta ce da farko sun ƙi yin barar suka yi ta kuka, sai matar ta rufe su a ɗaki ta yi ta dukansu, ta haka ne suka saba suka rungumi yin barar.