✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda lokacin daura aure ya koma na jana’izar amarya

Masu iya sun ce mutum yana nasa Allah Yana naSa. Wannan shi ne abin da ya faru da wasu iyalai a garin Bauchi, inda bayan…

Masu iya sun ce mutum yana nasa Allah Yana naSa. Wannan shi ne abin da ya faru da wasu iyalai a garin Bauchi, inda bayan sun kammala shirin aurar da ’yarsu a ranar Asabar da ta gabata, sai Allah Ya karbi rayuwarta cikin dare inda maimakon a daura mata aure da misalin karfe 11:00 na rana sai aka yi jana’izarta a daidai lokacin.

Wannan lamari ya girgiza al’ummar birni da na Jihar Bauchi  da ma dukan wanda ya samu wanna  labari.

A daidai lokacin da iyaye da abokai suka kammala komai don daura wa ’yarsu mai suna Fauziyya Abdulkadir Tataru aure da angonta Abduljalil Salisu Boyi kwanakin da Allah Ya nufa za ta rayu a duniya suka kare; inda aka yi jana’izarta a Masallacin Gwallaga da ke garin Bauchi, wurin da aka shirya za a daura aurenta da karfe 11 na safe.

‘Ta yi jinya bayan raba katin aure’ Iyayen ango da amarya, Injiniya Salisu Alhaji Boyi da Alhaji Abdulkadir Tataru, sun shirya auren ’ya’yansu ne a Masallacin Gwallaga ranar Asabar din da ta gabata da karfe 11:00 amma sai masu zuwa daurin aure suka zamo masu jana’izar amaryar a daidai karfe 11:00 din lamarin da ya jefa al’umma cikin dimuwa da jimami.

Aminiya ta bi diddigin wannan lamari, inda ta gana da iyaye da ’yan uwa da kuma angon da zai auri Fauziyya, Abduljalil inda suka fayyace yadda al’amura suka kasance ga marigayiyar.

Mahaifin amaryar Alhaji Abdulkadir Tataru ya ce marigayiya Fauziyya ta rasu ne bayan ta yi gajeruwar rashin lafiya. A cewarsa, “Tun bayan raba katin gayyatar daurin aurenta ta fara rashin lafiya, kuma ta dan samu sauki kafin ranar daurin auren nata. Sai dai daga Alhamis zuwa Juma’ar da suka gabata, sai ta dan daina cin abinci, wanda ya kai sai da aka sanya mata ruwa. Amma ranar Jumaa’a ma ta ce a cire mata ruwan da aka sanya mata. Aka cire; domin akwai yarta wacce take aikin asibiti. Ta ce mata in za a cire mata ruwan sai dai in za ta sha kunu da kanta, ta ce za ta sha. Aka cire mata ruwan ta karbi kunun ta sha.”

“Alhamdulillahi, ta dan fara magana da kowa kuma zuwa bayan magariba sai muka ji cewa Allah Ya karbi ranta. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un,” inji shi.

Alhaji Abdulkadir ya ce ta yi kyakykyawar rayuwa, tana zaman lafiya da kowa. Ita mahaddaciyar Alkur’ani ne, mai rikon addini kuma ta yi karatun boko, ta samu digiri a fannin Safiyo. Ta yi hidimar kasa a Maiduguri, Jihar Borno. Kafin rasuwarta, ta fara karatun digirinta na biyu a wannan fanni na Safiyo.

Rayuwata ta koma baya – Ango

Angon Fauziyya, Abduljalil ya ce sun hadu da ita ce tun tana karamar makarantar sakandare aji biyu. “Idan wanta ko wani ya yi mata wani abu sai in lallabe ta, ina share mata hawaye. Har zuwa lokacin tana cikin jami’a ma haka dai muka rayu. Abin kamar wasa, kamar gaske; muna wasa-wasa har batun aure  ya zama gaskiya. A takaice dai muna tare da ita tun shekarar 2008, wato kimanin shekara takwas ke nan zuwa yau in aka lissafa,” inji shi.

“Mun yi karatu da ita a wata makarantar sakandare, mai suna Ulul-Albab da ke Katsina, lokacin muna gaba da ita, muna ajin babbar sakandare tare da yayanta; ita kuma tana ajin karamar sakandare, daga baya sai aka dawo da ita sakandaren Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke nan Bauchi. Daga nan kuma sai ta shiga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa inda ta karanta fannin Safiyo,” inji shi.

Ya kara da cewa “Hakika rasuwar Fauziyya ba karamin rashi ba ne domin lokacin da abin ya faru ya gigiza ni kwarai, domin da aka gaya mini ba wai na ki yarda ba ne, sai da na je na ga gawarta kafin in yarda. Kuma mu Musulmi mun yi imani da kaddara mai kyau da mummuna. Komai kuma a kullum muna mai da shi zuwa ga Allah Ubangiji Mahalicinmu.  Don haka abin da ya faru da ita kaddara ne, sai dai kawai mu yi ta yi mata addu’ar neman dacewa kuma Allah Ya taikaita mata komai, tunda ciwo take yi Allah Ya dauki ranta. Kuma mu da muka ga yadda take cikn halin ciwon nan, ba dadi za mu ce mun ji ba, amma dai Allah Ya hutar da ita a rayuwa. Tunda ta rasu tana cikn jinya kuma zan ci gaba da yi mata addu’a a duniya, ina kuma fatan Allah Ya hada mu a Aljannar Firdausi da ita.”

Angon ya ce “Kasancewar rashinta zai sa rayuwata za ta sauya bisa la’akari da cewa mun shirya yin rayuwa tare kuma Allah bai kaddara ba. A matsayinmu na Musulmi sai dai mu yi tawakkali, kasancewa komai na Allah ne. domin in ka lura da yadda rayuwa take tafiya, kowa da yadda Allah Ya rubuta masa rayuwarsa, kowa da yadda Allah Ya nufi rayuwarsa za ta kasance. Rasuwarta ta mai da rayuwata baya kuma hakan ya sa na samu gibi mai wuyar cikewa amma tunda Allah Ya bar ni ina numfashi, zan yi tawakkali in ci gaba da rayuwa bisa tafarkin da Allah Ubangiji Ya nufa; kamar yadda Ya rubuta mini.

“Zan yi kokarin karfafa tawakkalina da yardar Allah, da ikon Allah ba zan shiga damuwar cewa nan gaba ba zan yi aure ba. Kowane abu, ko shan wahala in Allah ya so kuma ina rokon dukan ’yan uwa da sauran al’ummar Musulmi su taya ni da addu’ar cin wannan jarrabawa daga Allah Ubangijinmu, don wannan aya ce ga dukan jama’a. Sai kowa ya dauki sako daga wannan abu da ya faru, domin gaskiya wannan abu ba karamin abu ba ne sai dai tawakkali.”

‘Yar uwa ce tagari’

Yayan Fauziyya, Abdulmalik, Abdulkadir Tataru wanda sanadinsa ne angon ya san amaryar tasa, ya ce shi Fasuziyya take bi kuma lokacin rayuwarta ta kasance ba ta da abokin fada.

“Tunda muka taso ban taba jin an ce ta yi fada da wani ba. Ba ta bata wa wani rai da nufi, ba dai za ka gan ta tana fushi ba, koyaushe tana cikin fara’a da mutane. Ko an bata mata rai za ta yi kokari ta danne, ta yi hakuri. Yarinya ce mai hakuri sosai, kuma wannan rashi nata a lokacin aurenta al’amari ne babba amma mun dauke shi kaddara daga Allah. Muna kuma rokon Allah Ya ba ta makoma mai kyau, Ya sa gidan Aljannah ne makomarta,” inji shi.

Abdulmalik ya ce su bakwai ne ’ya’yan mahaifansu kuma ita ce ta biyu bayansa sai kannenta maza uku da mata biyu, na karshe. Ya kuma bayyana cewa duk da cewa ango Abduljalil abokinsa ne, in ya ga wacce yake so a gidansu, su a shirye suke za su sake ba shi idan har Allah Ya nufa zai yi aure a gidansu to ba matsala suna rokon Allah Ya tabbatar da alheri

. “Don dukan komai nufi ne na Allah, don mu Abduljalil dan uwa ne a gare mu,” inji shi. Kanen Fauziyya, Sabi’u Abdulkadir Tataru, wanda shi ke bin ta ya ce “Abu ne da ya zo da ajali, wanda ba yadda muka iya, tunda kaddara ce da Allah Ya aiko mana kuma dole mu karbe ta a haka; don ba mu da zabi.”

Ya ce Fauziyya ta dan yi jinya na mako biyu kafin ranar da Allah Ya yi mata rasuwa. “Allah Ya ce duk tsanani yana tare da sauki, kafin rasuwarta ta samu sauki kwarai da gaske amma ba gaskiya ba ce da ake cewa ta je walimar aurenta. Ta dai samu sauki sosai amma ba ta samu saukin da za ta iya zuwa wajen walimar aurenta da aka shirya ba, domin lokacin da aka yi walimar ba ta kwanta ba amma tana fama da zazzabin amma da sauki,” inji shi.

Sabi’u ya ce an gama komai na shirye-shiryen aurenta a lokacin, sai kuma Allah Ya kaddara ana gobe auren za ta bar duniya, kuma ta bar duniyar. Ya bayyana marigayiya Fauziyya da wacce take hada kan mutanen gidansu.

Ya ce mace ce mai hakuri. “Na shaku da ita sosai saboda kusancinmu ya kasance duk lokacin da nake da matsala ta rayuwa, ita nake fara samu koyaushe kan matsalata, sannan ita ce jigon hadin kan gidanmu, kuma duk wani abu tsakanin mu kannenta da yayanta saboda nisan hankalinta, yawanci duk ita muke samu kuma takan ba mu shawara. Ita ce wadda duk abin da take da shi za ta iya dauka ta ba ka, ta hakura kuma mace ce mai addini. Komai za ta yi tana duba Allah cikin sha’aninta, sannan da karatun Alkur’ani take kwanciya kullum. Sannan ita take fahimtar da mu yadda rayuwa take. Hakika mun yi rashi. Allah Ya sa haka shi ya fi hutu a gare ta.”

Yanzu al’umma ko’ina labarin rasuwa mai ban mamaki ta Fauziyya ke yi, ana ta yada batun rasuwar a dandali da shafukan sada zumunta; yayin da jama’a ke jimami.