Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.
Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.
- An ƙaddamar da gidan rediyon EFCC mai yaƙi da labaran ƙarya
- Gwamnatin Kano za ta fara ɗaukar nauyin shirya fina-finan Kurame
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.
Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.
Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.