Wata gobara ta hallaka wasu likitoci ma’aurata, Dokta Auta Gidado da matarsa, Dokta Amina Ahmad da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi a gidansu da ke Titin Legas a birnin Maduguri.
- Buhari ya nada sabbin ministoci
- Mayakan Boko Haram da ’yan bindiga 900 sun tsere a harin Gidan Yarin Kuje
Iyalan mamatan sun bayyana mana cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Sai dai suna zargin fetur ne ya haddasa ta, kuma daga yanayin raunukan, Dokta Auta ya kama da wuta yayin da yake kokarin ceto matarsa Dokta Amina, inda cikin gaggawa aka kai su sashin ba da agajin gaggawa na asibitin jami’ar.
Wata majiya ta bayyana cewa Dokta Auta ne ya fara rasuwa ranar Talata, kafin matar tasa, Dokta Amina ta bi bayansa ranar Laraba.
An kuma yi jana’izarsu an binne su, kamar yadda Musulinci ya tanada.
Da yake tabbatar mana da faruwar lamarin, Shugaban Kungiyar Kwararrun Likitoci Reshen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, Dokta Abdullahi Usman, ya ce yana cikin alhinin rashin wadannan jajirtattun likitocin, tare da sauran ma’aikatan Asibitin.
A karshe ya yi musu addu’ar Samun rahamar Ubangiji, da fatan mutuwar ta zama hutu gare su.