✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Kwankwaso ya yi Babbar Sallah a Kano

Kwankwaso ya bayyana yadda magoya bayan ɗariƙar ke son zaman lafiya.

Dandazon magoya bayan ɗarikar Kwankwasiyya ne suka yi cikar ƙwari a gidan jagoran jami’yyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso domin taya shi murnar bikin sallah babba.

Bikin wanda aka fara da misalin ƙarfe 4 na yamma, ya haɗa da magoya bayan tafiyar a jihar da ma wasu daga jihohin Najeriya.

Da yake jawabi a yayin taron, Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Yusuf Kofarmata, ya ce bikin shi ne karo na shida da ake gudanarwa duk shekara.

Amma, ya ce cikar ƙwari da ‘yan Kwankwasiyyar suka yi a na bana shi ne mafi girma idan aka kwatanta da waɗanda aka gudanar a baya.

Ya ce, “Fitowar jama’a ba za ta rasa nasaba da son zuwa nishaɗi da suke son yi a lokacin bukukuwan sallah ba, amma abun takaici babu hawan sallah a bana.

Makaɗa da masu raye-raye da mawaƙa daga Kano ne, suka baje kolinsu a gidan jagoran Kwankwasiyya na ƙasa.

Shi ma da yake jawabi a wajen bikin, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce, “Bari na yi amfani da wannan dama domin tunatar da ku cewa ‘yan Kwankwasiyya a ko ina suke mutane ne masu zaman lafiya, muna ci gaba da zaman lafiya.

“A 2019 mun ci zaɓen gwamna a jihar nan amma maƙiyan Kano suka ci amanarmu ta hanyar amfani da INEC, ta hanyar kotu da sauransu kuma abin da ya faru yanzu ya zama tarihi.

“Haka kuma a wannan karon a 2023, mun ci zaɓe da gagarumin rinjaye amma maƙiya jihar nan sun yi ƙoƙari wajen ganin sun ƙwace mana, amma cikin ikon Allah Ya yi hukuncinsa gaskiya ta fito.

“Da alama maƙiya sun sake tasowa, abin da ke faruwa kan batun masarautu muna godiya ga duk masu goyon bayan gwamnati, ina mai farin cikin cewa ko a yau duk shugabannin ƙananan hukumomi 44 sun zo nan a yau. Na tambayi ko wani daga cikinsu ya bar tafiyar amma suka ce min a’a.

“Amma wasu sai ƙoƙari suke yi don ganin cewa mutane da yawa suna shiga wannan tafiya kuma ban yi mamaki ba domin talakan Kano ba ya son zalunci, shi ya sa muke a nan.”