An kama wani direba mai suna Tigidam Bright bisa zargin sa da hadin baki wajen sace matar mai gidansa, Misis Gift Topba a birnin Fatakwal na jihar Ribas.
Jami’an Sashen Binciken Bayanan Sirri na Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa ne suka cafke shi tare da karin wasu mutum biyu da ake kyautata zaton masu garkuwa ne, Isaac Michael da Leera Barisua.
- Direba ya gano wanda ya yi garkuwa da shi a cikin fasinjojinsa
- An karrama direban Sardauna a bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa
Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga ne suka sace matar Mista Gani Topba, wanda sanannen mai fafutukar kare hakkin dan Adam ne a ranar 25 ga watan Agustan 2020 inda suka yi awon gaba da ita.
Daga bisani ne suka bukaci a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar ta, inda daga karshe aka amince aka ba su Naira dubu 500 kafin su sako ta.
Jami’an ‘yan sandan dake bin diddigin lamarin ne suka bibiyi masu garkuwar ta hanyar layukan wayar da suka yi amfani da su wajen cinikin kudin fansar wanda ya taimaka musu cafke su.
Da yake tattauna da ‘yan jarida, Tigidam ya musanta hada baki wajen sace matar, ko da yake ya amince an bashi Naira dubu 100 daga kudin fansar ta.
Ya ce ya shaida wa abokan nasa biyu, Isaac da Leera yadda tsohon mai gidan nasa ya kore shi ba bisa ka’ida ba inda su kuma suka yi alkawarin daukar masa fansa.
Tigidam ya ce, “Wani lokaci a watan Agustan 2020, na ziyarci abokai na a kauyen mu na Khana inda suka tambaye ni ko har yanzu ina aiki amma na ce musu a’a, mai gida na ya kore ni saboda zargi na a kan laifin da ban aikata ba.
“Daga nan sai suka kudiri aniyar daukar fansa a madadi na, amma ban san shirin sace matarsa suke yi ba.
“Na sami labarin garkuwa suka yi da ita, bayan sun sako ta kuma suka bani Naira dubu 100 a matsayin nawa kason,” inji shi.
Sai dai Tagidim ya ce ya karbi kudin ne saboda yana fargabar za su iya kashe shi idan ya ki ba su hadin kai.
Mai shekaru 34, Tagidim ya ce wani abokinsa mai suna Mark ne ya koya masa harkar ta garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, wanda shi kuma daga bisani ya hada shi da wasu karin mutum biyu inda suka tashi gungun mutum hudu.
Shi kuwa a nasa bangaren, Leera wanda Injiniyan Wutar Lantarki ne ya ce ya yanke shawarar tsunduma harkar garkuwa ne tun lokacin da ya rasa aikinsa a wani kamfanin mai a Fatakwal.