Ga dukkan alamu za a iya alAkanta tafiyar-hawainiya da bunkasar tattalin arziki da walwala ke yi ga watsi da aka yi da bangaren noma a matsayin ginshikin ci gaba.
Daga cikin manyan abubuwan da ke yi wa batun cikas kamar yadda tawagar kwararru da Babbankin Najeriya ya kafa shekarun baya ya gano shi ne sanya isassun kudi a bangaren shi zai yi maganin matsalar. Dalili kuwa shi ne bankunan Najeriya suna dari-darin baiwa manoma bashi yayin da su kuma manoman ba su damu da karbar bashin ba ko da bankunan sun yi musu tayin ba su bashin saboda hadarin da ke tattare da harkokin noma a kasar.
Akwai dalilai na hakika da suka sa ya zama wajibi a mayar da hankali kan bangaren noma. Na farko, bangare ne da aka yi hasashen samun riba musamman ma idan aka tabbatar da dorewarsa wanda zai mayar da danyen amfani zuwa abin da za a rika ci a gida da kuma fitar da shi waje.
Na biyu, kodayake bangaren ya samar da ayyuka kimanin kashi 70 cikin dari ga yawan al’ummar kasar nan akwai wasu damarmakin da za a iya cin gajiyarsu wadanda za su samar da ayyukan yi a bangaren ta hanyar kwadaitar da mutane su koma noma.
Kwararru sun gano cewa ta hanyar komawa noma zai zama wata dama ga matasan da a da ba sa noma kwata-kwata su rika gyara kayan amfanin gona da kuma sayar da shi tare da yin wasu sana’o’i.
Masu bincike na Babban Bankin CBN sun bayar da shawarar cewa don a kara kwadaitar da bayar da bashi a bangaren noma akwai bukatar a fito da wani tsari wanda zai kare asarar bangaren don baiwa manoma da bankuna karfin gwiwar sanya jari a bangaren. Sun bayar da shawarar a kafa Hukumar Rage Asarar Bashin Noma wacce atakaice ake kira NIRSAL
Bankin CBN ne ya kafa Hukumar NIRSAL a cikin shekarar 2013 wacce take tsayawa bashin da za a baiwa manoma tare da basu dama su biya kudin a cikin lokaci.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da ta sanya a gaba na kai harkar noma karkara, Hukumar NIRSAL ta rika tabbatar da bayar da kudi ga dukkan wadanda ke taka rawa a harkar noma.
Hukumar NIRSAL tana rage yin asarar da hukumomin za su yi yayin da suke bayar da bashin noma ta hanyar karfafa bankuna da masu karbar bashin bin turbar da ta dace a harkar sanya kudi a bangaren noma.
Don cimma wannan buri, Manajan Daraktan Hukumar NIRSAL, Aliyu Abdulhameed kwannanna ya ce “Hukumar NIRSAL ta saukaka samar da bashin Naira biliyan 77 da digo hudu daga bankunan harkar noma da bayar da horo ga manoma dubu 700 a kan harkokin noma da ilimin tattala kudi sannan kuma da tabbatar da bayar da tallafi ga kananan manoma dubu 500.
“A matsayin Hukumar da ba bankin kasuwanci ba wacce aka dora mata alhakin kawar da asara a bangaren noma tare da tabbatar da kasuwancin noma, Hukumar NIRSAL tare da da ni mun mayar da hankali wajen bin ka’idojin da aka shimfida don cimma wannana manufa’’.
Hukumar NIRSAL tana magance matsalar karancin gudanar kudi a bangaren noma wadanda suka hada da karancin fahimtar bangaren da yawan asara da wahalar samun bashi da tsadar biyan bashin.
Ayyukan Hukumar ya wuce tsayawa manoma don samun bashi tare da gyara harkokin noma har tabbatar da bangaren bankuna ya baiwa bangaren bashi cikin aminci tare da karfafa bankuna su bayar da bashi ga manoma ta hanyar basu hasafi mai yawa da kuma kayan aiki.
Don cimma hakan, Hukumar NIRSAL ta tsara ginshikai biyar don kawar da asarar kudin da aka sanya a harkar noma mai dorewa da kafa turba mai karfin gaske da bunkasa bayar da bashi ta hanyar yin amfani da jarinta na Dalar Amurka miliyan 500.
Ginshikai biyar na Hukumar NIRSAL sun kunshi abubuwa kamar haka:
Dala miliyan 300 wacce aka ware don raba asara. Hukumar tallafawa manoma ta NIRSAL ta na amfani da wannan tsarin magance kirdadon bankuna kan yawan asara a bangaren ta hanyar raba asara ga bankunan bayar da lamuni.
Tsarin Inshora an ware masa Dala miliyan 30. Wannan tsari abin da yake son cimmawa shi ne ya fadada inshorar kayan amfanin noma don samun bashi daga tsarin da ake da shi a yanzu zuwa sabon tsari ga sabbin amfani kamar inshorar yanayi da annoba da inshorar cututtuka.
Tallafin kayan aiki wanda aka warewa Dala miliyan 60: Hukumar NIRSAL ta na amfani da wannan tsari don karfafa bankuna su bayar da bashi mai dorewa ga noma da kuma yadda manoman za su samu bashin tare da yin amfani da shi ta hanyar da ta dace tare da kara bunkasa yawan amfanin da suke nomawa masu inganci.
Tsarin tantance Bankuna wanda aka warewa Dala miliyan 10: Hukumar NIRSAL ta fito da wannan tsari don tantance bankuna ta hanyoyi biyu wato karfin bayar da bashin noma da amfaninsa ga rayuwar al’umma da kuma damar samun bashin ga jama’a.
Tsarin baiwa bankuna hasafi wanda aka warewa Dala miliyan 100. Wannan tsari ne wanda ke baiwa bankunan da suka yi nasara shiga tsari na hudu ta hanyar basu hasafi don karfafa matsayinsu na bayar da bashi ga harkar noma. Hakan zai iya kasancewa ta hanyar ba su tallafin kudi ko kuma kyautuka.
Aiwatar da ayyukan Hukumar NIRSAL da gaske zai kara kudin shiga ga kasa da bunkasa tattalin arzikinta da samun karin shigar kudin kasashen waje da kara karfafa matsayin Babban Bankin CBN na tattala darajar kudin kasar da rage tashin farashin kayayyaki da bunkasa kudin ajiyar kasshen waje tare da daidaita tsarin hada-hadar kudi.
Dadin-dadawa, aikin zai ’yanta bankuna daga bukata fiye da kima tare da yawan tallafi marar iyaka ga bangaren noma.
Hukumar NIRSAL za ta karfafa bangaren kudin Najeriya saboda samar da damarmarki ga bankuna su samu riba mai soka a basukan da suka bayar tare da tabbatar da ci gaban bunkasar samar da kudi ta hanyar karanta haifar da bashi da tsadar raba shi ga manoma.
Tsakanin 2012 da 2015 yayin da Hukumar NIRSAL ke aiki a matsayin ofishin da ke aiwatar da ayyuka tare da Sashen Bunkasa Kudi na Bankin CBN ta cimma nasarori kamar haka:
Samar da bashi na fiye da 454 ga harkokin noma wanda ya kai kimanin Naira biliyan 61 da digo 161 da biyan kudin ruwa na fiye da Naira miliyan 753 da digo 36 wadanda suka biya basukansu a lokaci.
Bayar da horo ga fiye da manoma dubu 112 a kasa baki daya a kan noman zamani da dabarunsa da tafiyar da kasuwancinsa.
Tun lokacin da Bankin CBN ya nada tawagar gudanarwar hukumar a watan Disemban shekarar 2015, Hukumar NIRSAL ta tallafa wajen sayo taraktocin noma dubu daya na biliyoyi don tallafawa kananan manoma da manya a kan farashi mai rahusa.
NIRSAL ta cimma hakan ne ta hanyar tsarin samar da taraktoci wanda bankunan ba za su yi asara ba sannan kuma zai janyo sha’awar kamfanonin samar da taraktocin.
Tsarin ya cimma nasara ba tare da samun wata matsala ba ta biyan kudi da karin bunkasar noman zamani.
Dukkan masu mu’amalar harkar noma wadanda suke da tsari za su iya mika takardun bukatar neman bashin Hukumar NIRSAL.
Wadanda suka hada da: Kananan manoma da masu samar da kayan noma da kungiyoyin manoma da manyan manoma da masu sarrafa amfanin gona da kamfanonin noma da masu samar da kayyakin aiki noma da dillalan kayan noma.
Yana da kyau a sani cewa Hukumar NIRSAL ba ta mu’amala da daidaikun manoma, NIRSAL na mu’amala da kananan kungiyoyin manoma.
Wadanda ke bukatar bashi za su iya nema ta hanyar aika takardun neman bashin Hukumar NIRSAL ta bankunan da suke amfani da su ko ta ofishin Hukumar NIRSAL.