✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kauyuka shida ke rayuwa da ruwan tafki daya a Gombe

Wasu al’ummar karkara da ke kauyuka shida daban-daban a yankin Karamar Hukumar Kwami a Jihar Gombe suna rayuwa da ruwan kwari guda daya a yankunansu,…

Wasu al’ummar karkara da ke kauyuka shida daban-daban a yankin Karamar Hukumar Kwami a Jihar Gombe suna rayuwa da ruwan kwari guda daya a yankunansu, saboda rashin ingantaccen ruwan sha da suke fama a kauyukan.

A Rahoton musamman da Aminiya ta yi, inda wakilinmu ya yi tattaki zuwa garin Roddo ya zanta da Jauro Bappah, Sarkin Roddo, don jin yadda al’ummar kauyuka shida suke rayuwa da wannan ruwa na kwari wanda idan damina ta wuce suke shiga matsanancin hali.

Jauro Bappah, ya ce tsakanin kauyukan nasu da garin Kwami inda nan ne helkwatar Karamar Hukumar Kwami bai wuce kilomita biyar ba, amma an bar su a baya babu ruwan sha mai tsafta.

Basaraken ya kara da cewa wannan kwari da suke diban ruwa a cikinsa ma albarkacin wani kamfanin aikin hanya ne suke ci da ya yi kwangilar hanyar Gombe zuwa Dukku lokacin mulkin farar hula na Alhaji Habu Hashindu a shekarar 1999 da suka tona shi saboda diban kasa, daga bisani sai ruwa ke taruwa cikinsa, amma kafin wannan daga wani kwari daban suke samun ruwan kai tsaye, idan ya gama wucewa shi kenan sun kwala.

Ya ce bayan garin nasa Rodda Bappah, akwai sauran garuruwan da suke amfani da wannan ruwan da suka hada da Roddo Sadu da Roddo Kangiwa da Roddo Jauro Jingi da Roddo Disa da Roddo Jauro Hamidu, wadanda dukan su suna karkashin Hakimin Kwamfulata ne anan Karamar Hukumar Kwami.

Ya kuma ce akwai wani lokaci da su shugabannin kauyukan su biyar suka tara mutane mota biyar suka kai kukansu wajen Hakiminsu kan matsalar ruwan sha, shi kuma ya tura su wajen Shugaban Karamar Hukumar Kwami, Alhaji Ya’u Hassan Marafa, suka koka masa halin da suke ciki, suka kuma nemi a taimaka a samar musu ko da rijiyoyin burtsatse, ya ce za a duba, amma har yanzu shiru.

A cewar Jauro Bappah, idan damina ta wuce, wannan ruwan yana karewa, sai sun tsallaka garin Jabla sannan su sami ruwan rijiya, wanda ita ma rijiyar ba ta isar su, domin an yi mata yawa a wani lokaci ma sai an kwana ana jiran ruwan ya taru kafin wasu su samu.

Da wakilinmu yake tambayarsa kan cewa ba ya ganin shan irin wannan ruwan zai iya haifar da cututtuka, sai ya ce su mutanen kauye da yake sun dade suna shan wannan ruwa, basa iya gane irin cutar da suke kamuwa da ita, sai dai idan mutum bai da lafiya ya yi ta jinya kawai har sauki ya samu ko kuma a mutu.

Sannan ya ce dan gudun shigar dabbobi wannan kwari, suna hada kudi duk wata daga jama’ar kauyukan suna biyan masu gadinsu mutum biyu Naira dubu goma goma.

Wasu samari da ‘yan mata da na zanta da su suna diban ruwa a wannan kwari, suma sun koka matuka bisa yadda suke shan wannan ruwa duk da cewa ba su da nisa da Kwami, suna cewa indai ba za a iya samar wa kauyukansu ruwan sha mai tsafta ba, to irin wannan lokaci na siyasa bai amfane su da komai ba, duk da cewa kuri’unsu na taka rawa wajen sosai kawo shugabanni bisa mulki.

Shi ma daya daga cikin masu gadin wajen da na zanta da shi, Malam Adamu Baka cewa ya yi aikinsa a wajen shi ne ya jira wannan ruwa dan kada dabbobi su shiga ciki su lalata shi, kasancewar shi ne kadai ruwan shan su da suke rayuwa.

Kazalika Aminiya ta shiga garin Jabla dan ganin rijiyar da ake komawa idan wannan na tafkin ya kare, inda Isma’il Jibrin wanda mahaifinsu ne ya tona wannan rijiyar kimanin shekaru 27 da suka gabata, ya ce rijiyar tana da gaba 12 ne amma yanzu haka duk da cewa lokacin damuna ake ciki ruwan babu.

Isma’il Jibrin, ya kuma ce suna rokon ‘yan siyasar yankin da gwamnati da su kawo musu dauki wajen daure rijiyar saboda suna fuskantar barazanar zaizayar kasa, sannan kuma kauyukan da suke zuwa diban ruwa a wannan rijiya suna da yawa, don haka suke son a taimaka musu a gyara musu ita, sannan kuma a tona musu rijiyar burtsaste.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin shugaban Karamar Hukumar Kwami, Alhji Ya’u Hassan Marafa da Dan Majalisar Jihar mai wakiltar Kwami ta Yamma Walid Muhammad da kuma Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gombe da Kwami da Funakaye, Honorabul Yaya Bauchi Tongo, amma har kawo lokacin hada wannan rahoto, hakan ya faskara.